Manchester United na tattaunawa da Crystal Palace kan Jack Butland

Butland ya buga wasa 87 a gasar Premier a kungiyoyi uku da ya yi wasa.

Asalin hoton, BBC Sport

Bayanan hoto, Butland ya buga wasa 87 a gasar Premier a kungiyoyi uku da ya yi wasa.

Manchester United ta fara tattaunawa da mai tsaron ragar Crystal Palace, Jack Butland domin komawa Old Trafford da taka leda.

Kocin Manchester United Erik ten Hag na neman samawa golan kungiyar David de Gea mataimaki, bayan ta mayar da golan Newcastle United, Martin Dubravka a watan Janairun 2023.

Tun shekrar 2020 Butland yake Crytal Palace, kuma wasanni 10 kacal ya buga wa kungiyar a Premier, kuma bai buga mata ko daya ba a wannan shekarar.

Kwantaragin dan wasan mai shekara 29 za ta kare a Selhurst Park a wannan kakar.

Butland ya buga wa Ingila wasa tara a kuma yana cikin tawagar d Gareth Southgate ya tafi da ita gasar kofin duniya na 2018.

Kuma tun bayan fadawar Stoke City Championship a 2018, lamura suka tabarbarewa mai tsaron ragar.