'Yadda matsin tattalin arziki ya sa na kamu da cutar damuwa'

.

Abdullahi Yahaya Yusuf, wani matashi a jihar Kano da ke arewacin ƙasar, na cikin mutanen da ke jin tasiri da raɗaɗin matsin tattalin arziƙi ta yadda hakan ya janyo ya shiga gararin rayuwa.

Abdullahi ya ce ya zamanto yana kallon rayuwar kamar ba ta da wani amfani a gare shi ta yadda a kowa ne lokaci yake cikin fargaba da ɓacin rai.

Abdullahi ya aiko da labarinsa ne ga BBC, bayan wallafa neman jin ra’ayin mutane a wani shirin tattara labarai na musamman gabanin zaɓukan 2023.

Matashin ya ƙara da cewa ya yi karatu zuwa matakin N.C.E., inda daga nan ya tsaya saboda tsadar rayuwa.

‘‘Na fita da sakamako mai kyau amma ya gaza amfanar da ni saboda gwamnati ba ta samar mani da aikin da karatun da na yi zai yi amfani ba,’’ in ji Abdullahi.

‘Ga shi ban yi faɗi tashi da yawa a rayuwa ba wanda zai ba ni damar gogayya a fannin kasuwanci ba, ga kuma tarin burika da kullum nake son cimmawa a rayuwata. '

'Ɗimuwa da na shiga bayan rasuwar mahaifina'

Matashin ya bayyana cewa ya sake shiga wani irin mawuyacin hali na rayuwa bayan saka dokar kulle da gwamnati ta yi lokacin annobar korona, inda a lokacin ne kuma ya rasa mahaifinsa wanda ya ce shi ke taimaka masa a fannin rayuwa.

Abdullahi ya ce hakan ya sanya komai ya dawo kan wuyansa, inda ya shiga tunani kan me zai yi domin tallafa wa rayuwarsa saboda bayan gama makaranta ya zamanto babu aikin yi balle sana’a ta hannu.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

‘‘Abubuwa sun taru sun dabaibaye ni na rasa yadda zan yi da rayuwata,’’ kamar yadda Abdullahi ya shaida min.

Bayan matsin rayuwa da matashin ya shiga, ya ce a halin yanzu dai al’amura sun fara daidaita saboda ya shiga harkar kasuwanci kuma yana samun ɗan abin dogaro da na kaiwa bakin salati.

'Kira na ga gwamnati da kuma matasa'

Abdullahi ya ce hakkin gwamnati ne na ganin ta samar da yanayi mai kyau ta yadda matasa za su gudanar da rayuwarsu ta hanya madaidaiciya ko da ba ta samar masu da aikin yi ba.

Ya kuma ce ya kamata al’umma ta tsaya tsayin-daka wajen ganin matasa sun dogara da kansu ta yadda ba sai sun jira gwamnati ta samar masu da abin yi ba.

''Domin haka ƙalubale ga kowanne uba da yan uwa kamar yadda aka ɗauki ilimantar da yaro dole to haka ma koya masa sana'a ya zama su ɗauke shi da wajibi domin gudanar da rayuwa,'' in ji Abdullahi.

Matashin ya kuma yi kira ga matasa da su tashi su nemi abin dogaro da kai, amma ya ce duk da son yin wani abu idan babu jari mutum ba zai iya yin komai ba.