Gwamnatin jihohi na gaggawar zaɓen ƙananan hukumomi a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
A Najeriya, akalla jihohi goma sha uku sun sa ranar gudanar da zaben kananan hukumomi, bayan da a ranar Alhamis kotun kolin kasar ta yanke hukunci, wanda ya haramta mika kason kudi daga gwamnatin tarayya ga kananan hukumomin da ba a yi zaben shugabanninsu ba.
Ana ganin hukuncin kotun ne ya sa jihohin fara shirye-shiryen gudanar da zaben, har wasu ma sun sa ranakun da za su gudanar da wannan zabe.
Bisa ga dukkan alamu, hukuncin da kotun kolin Najeriya ta yanke, wanda ya ba kananan hukumomi 'yancin cin gashin kansu, yanzu haka ya zaburar da zaben shugabannin kananan hukumomi a jihohi fiye da goma, irin su Bauci da Binuwai da Kaduna da Kebbi da Katsina da Kogi da Jigawa da dai sauransu.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kaduna ta fitar da jadawalin zaben, wanda ya nuna cewa a ranar 19 ga watan Oktoba mai zuwa za a gudanar da zaben shugabannin kananan hukumomi a jihar.
Ita ma hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kebbi ta shirya gudanar da zaben kananan hukumomin a karshen watan Agusta.
Honarabul Aliyu Mohammed Mera shugaban hukumar ya ce sun kira dukkan masu ruwa da tsaki da sauran jam'iyyu sun zauna da su kafin su fitar da ranar da za a yi zaɓen, 31 ga watan Agusta.
Ya ce, "dukkan shirye-shiryen da ake cewa ma'aikatar zaɓe ta yi mun riga da munyi, mun tanadi kayan aikin zaɓen, kuma bakin gwargwado mun wayar da kan al'umma kan zaɓen, mun nemi taimakon jami'an staro domin ganin zaɓen ya tabbata."
Shugaban ya ce tun kafin hukuncin kotun suka sanya wannan rana ta zaɓen, "Mun saba zaɓe, kuma da wuya kaga wata jiha wata jam'iyya ta ci zaɓen ƙananan hukumomi wadda ba ta gwamanti ba, amman a jihar Kebbi ba haka ba ne saboda mun yi zaɓen kansiloli da yawa da ba ƴan jam'iyar gwamnati ba sun ci zaɓen kuma an tabbatar masu kujerunsu."
"Wanda duk ya ci za mu ba shi haƙƙinsa kamar yadda muka saba," in ji Aliyu Mera.
Ana ganin zaben kananan hukumomin da ke tafe a jihohi tamkar wani zakaran gwajin dafi ne na gina harsashin tabbatar da 'yancin cin gashin kai a matakin kananan hukumomin Najeriya.










