Al-Hilal da Barcelona na son Salah, Man United na zawarcin Jarrad

Salah

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

Kulub din Al-Hilal na Saudiyya na son dauko dan wasan gaba na Masar mai taka leda a Liverpool, Mohamed Salah, 32, kafin gasar cin kofin duniya ta kungiyoyi a badi.(Mirror)

Ita ma Barcelona na son daukar Salah idan kwantiraginsa da Liverpool ya kare a karshen kakar wasa. (Sport - in Spanish)

Liverpool na shirin fara tattaunawa kan sabon kwantiragin dan wasan Scotland Andy Robertson, mai shekara 30, a lokacin bazara. (Football Insider)

Kulub-kulub din Premier League na da hakkin biyansu diyya kan rashin kudaden shiga, idan aka samu Manchester City da laifin take dokokin kashe kudi na League. (Times - subscription required)

Manchester United na shirin dauko dan wasan tsakiya na Ingila mai taka leda a Everton a Jarrad Branthwaite, mai shekara 22. (Talksport)

Sabon shugaban kulub Manchester United, Ruben Amorim na son dauko 'yan wasa uku da ke taka leda a Sporting, wato dan wasan tsakiya na Portugal Goncalo Inacio, 23, da mai tsaron gida na Ivory Coast Ousmane Diomande, 20, da dan wasan gaba na Sweden Viktor Gyokeres - domin komawa taka leda Old Trafford. (Sacha Tavolieri, via Teamtalk)

Dan wasan tsakiya na Ingila Harry Maguire, 31, ba zai bar Manchester United a watan Junairu ba, ya kuma yi amanna zai samu sabon kwantiragi a kulub din. (TBR Football)

Paris St-Germain na zawarcin dauko dan wasan gaban Colombia da ke taka leda a Aston Villa Jhon Duran, mai shekara 20. (Fichajes - in Spanish)