Saudiyya na zawarcin Son, Chelsea ta tuntuɓi Maignan

Lokacin karatu: Minti 1

Ɗan wasan gaba a Tottenham, Son Heung-min mai shekara 32 ya kasance wanda ƙungiyoyin Saudiyya ke rubibi a yanzu. (Telegraph)

Mai buga gefe a Manchester United, Jadon Sancho na iya komawa Saudiyya sakamakon yadda ƙungiyoyi irinsu Al-Hilal da Al-Ittihad da Al-Nassr ke zawarcin matashin mai shekara 25 daga Ingila. (Mirror)

Ɗan wasan tsakiya a Real Sociedad, Martin Zubimendi mai shekara 26 na nuna rashin tabbas kan tafiyarsa Arsenal, inda ɗan wasan na Sifaniya ke duba zaɓin da yake da shi. (Radio Nacional de Espana, via Metro)

Mai buga gaba a Brentford da Kamaru, Bryan Mbeumo, ɗan shekara 25 na fatan samun albashin £250,000 a kowanne mako - ninki har sau biyar kan abin da ake ba shi yanzu - idan ya koma Manchester United. (Times - subscription required)

Inter Milan ta tuntubi kocin Como kan ko tsohon ɗan wasan tsakiya a Sifaniya, Cesc Fabregas zai maye gurbin mai horas da su Simone Inzaghi, da ya tafi. (Sky Sports Italia - in Italian)

Chelsea tayi tuntuba kan ɗan wasan Faransa mai shekara 29, Mike Maignan, wanda yake da sauran kwantiragin shekara guda a AC Milan. (Talksport)

Ɗaya daga cikin masu hannun jari a Crystal Palace, John Textor, wanda shi ke da ƙungiyar Faransa ta Lyon, na shirin sayar da kaso mai yawa na hannun jarinsa. (Mail)

Mai tsaron raga a Ingila, Aaron Ramsdale ya tattauna kan yiwuwar tafiya West Ham daga Southampton. (Talksport)

Ɗan wasan tsakiya a Croatia, Luka Modric mai shekara 39, ya amince ya koma AC Milan idan ya bar Real Madrid. (Gianluca di Marzio, via Football Italia)