Jihohin da damuna za ta faɗi da wuri da waɗanda za ta sauka a makare a Najeriya

Lokacin karatu: Minti 2

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya, Nimet ta fitar da cikakken bayani dangane da yadda damunar bana za ta kasance da ya haɗa da lokacin saukar ruwa da dakatarwarsa.

Wannan na ƙunshe ne a wani daftari da ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya fitar dangane da hasashen abin da zai faru a damunar ta bana.

Bayanin ya ƙunshi jihohin da damunar za ta faɗi da wuri da waɗanda za a samu jinkiri da jihohin da damunar za ta ƙarƙare da wuri da kuma waɗanda za ta daɗe.

Sai dai daftarin ya nuna cewa wasu jihohin ka iya tsintar kansu a azuzuwa da dama kasancewar wasu sassan jiha ka iya fuskantar ɗaya daga cikin abubuwan da hukumar ta lissafa.

Jihohin da za a samu jinkirin damuna

Hukumar ta yi hasashen samun jinkirin saukar damuna a wasu jihohin arewaci da na tsakiyar ƙasar kamar haka:

  • Plateau
  • Kaduna
  • Niger
  • Benue
  • Nasarawa
  • Taraba
  • Adamawa
  • Kwara

A bisa al'ada damina na kankama a mafi yawan arewacin Najeriya ne daga watan Afrilu ko Mayu inda takan ƙare a ƙarshen Satumba zuwa cikin Oktoba.

Sannan yawancin manoma a yankin kan yi shuka ne a cikin watan Mayu zuwa Yuli, kasancewar abubuwan da aka fi nomawa - kamar masara da gyaɗa da waken soya - na buƙatar ruwa ne na kimanin tsawon wata huɗu kafin lokacin girbi.

Abubakar Isiyaku, wani malamin gona jihar Kaduna ya ce babban abin fargaba shi ne idan aka samu ƙamfar ruwa a tsakiyar damina.

"Babbar matsalar ita ce a samu mako ɗaya zuwa kwana goma ba a samu ruwan sama ba a cikin watan Mayu ko Yuli, wannan yana yin matuƙar illa ga shuka."

Jihohin da damuna za ta faɗi da wuri

Hasashen hukumar ya nuna cewa damunar bana za ta faɗi da wuri a wasu jihohin kudancin Najeriya kamar haka:

  • Delta
  • Bayelsa
  • Rivers
  • Anambra
  • Oyo
  • Ogun
  • Osun
  • Ondo
  • Lagos
  • Edo
  • Enugu
  • Imo
  • Ebonyi

Jihohin da ruwan sama zai tsaya da wuri

Dangane kuma da tsayawar ruwan sama da wuri, hukumar ta yi hasashen faruwar hakan a wasu jihohin ƙasar da suka haɗa da arewaci da kudancin Najeriyar:

  • Zamfara
  • Katsina
  • Kano
  • Kaduna
  • Jigawa
  • Plateau
  • Bauchi
  • Borno
  • Yobe
  • Adamawa
  • Taraba
  • Niger
  • Kwara
  • Kogi
  • FCT
  • Ekiti
  • Ondo

Jihohin da damuna za ta daɗe

Hukumar ta Nimet ta yi hasashen cewa za a samu ɗan jinkirin ƙarƙarewar damunar bana a wasu jihohi da sassan wasu jihohin ƙasar kamar haka:

  • Kaduna
  • Nasarawa
  • Benue
  • Lagos
  • Kwara
  • Taraba
  • Oyo
  • Ogun
  • Cross River
  • Delta
  • Akwa Ibom
  • Ebonyi
  • Anambra
  • Enugu

Shawarar masana

Umar Sale Anka da ke ƙungiyar da ke rajin kare muhalli a Najeriya ya ce waɗannan bayanan da hukumar ta Nimet ta fitar tamkar matashiya ce ga gwamnatoci.

"Waɗannan matsaloli da aka faɗa ba dabo ba ne ilimi ne. Idan ba a ɗauki mataki ba to lallai za a samu matsaloli idan har aka ɗauki damuna yadda aka saba. Kenan za a iya samun fari sakamakon rashin isasshen ruwan na sama a wuraren da zai ɗauke da wuri."

"Dole sai an samu irin shuka ɗan wuri ga wuraren da za a samu jinkirin damuna. Wuraren da ke noman rani su mayar da hankali ga noman ranin," in ji Umar Saleh.