Amurka ta kama ɗan Libya da ake zargi da tarwatsa jirgi a Lockerbie

Asalin hoton, Getty Images
Hukumomin Scotland sun ce wani ɗan ƙasar Libya da ake zargi da hada bam din da ya lalata jirgin Pan Am mai lamba 103 a kan Lockerbie shekaru 34 da suka gabata, yana tsare a hannun Amurka.
Amurka ta sanar da tuhumar da take yi wa Abu Agila Masud shekaru biyu da suka gabata bisa zargin sa da hannu a harin bam a ranar 21 ga watan Disamban 1988.
Fashewar a cikin jirgin Boeing 747, ta yi sanadiyyar mutuwar mutum 270.
Wannan dai shi ne harin ta’addanci mafi muni da ya faru a ƙasar Birtaniya.
Dukkanin fasinjojin 259 da ma’aikatan jirgin da ke cikin jirgin, sun mutu ne kan hanyar zuwa birnin New York daga Landan, yayin da wasu mutane 11 kuma suka mutu a Lockerbie lokacin da tarkacen jirgin ya lalata gidajensu.
A watan da ya gabata, aka bayar da rahoton cewa wasu gungun ‘yan bindiga a Libya, sun yi garkuwa da Masud, lamarin da ya sa ake yayata batu cewa za a miƙa shi hannun hukumomin Amurka domin fuskantar shari’a.
A sehakara ta 2001, aka samu Abdelbaset al-Megrahi, da laifin tayar da bam a jirgin Pan AM 103, bayan gurfanar da shi a gaban wata kotu ta musamman a Scotland a Netherlands.
Shi kadai ne aka yanke wa hukunci kan kai harin.
An yanke wa Megrahi, hukuncin daurin rai-da-rai, sai dai, gwamnatin Scotland ta sake shi bisa dalilai na jin kai a shekarar 2009 bayan samun sa da cutar kansa.
Ya mutu a Libya a shekara ta 2012.
Megrahi, wanda a kodayaushe yake bayyana cewa ba ya da laifi, ya kalubalanci hukuncin daurin shekara 27 da aka yanke masa. Ya yi nasara a ɗaya, yayin da aka yi watsi da ɗayan kuma.
‘Mai magana da yawun ofishin mai bincike na Scotland, ya ce an fada wa iyalan wadanda aka kashe a harin Lockerbie cewa Abu Agila Mohammed Mas’ud Kheir Al-Marimi na tsare a hannun Amurka.
‘Masu gabatar da ƙara da ‘yan sanda na Scotland da ke aiki tare da gwamnatin Birtaniya da abokan aikin su ‘yan Amurka, za su ci gaba da gudanar da wannan bincike, da nufin gurfanar da wadanda suka yi aiki tare da Al-Megrahi a gaban kuliya.’’
Lokacin da aka tayar da bam din Lockerbie
Masu bincike na Amurka da Birtaniya, sun tuhumi Megrahi a shekara ta 1991 amma ba a miƙa shi ga Libya ba sai watan Afrilun 1999.
> Watan Mayun 2000 – An fara zaman jin ƙara ta musamman karkashin dokar Scotland a sansanin Zeist da ke Netherlands.
> 31 ga watan Janairu – An samu tsohon jami’in leƙen asiri na Libya, Megrahi da laifin kisan gilla tare da daure shi na tsawon rai da rai da mafi karancin shekaru 27.

Asalin hoton, Reuters
> Watan Maris din 2002 – Aka yi watsi da ƙarar da Megrahi ya shigar kan hukunci da aka yanke masa.
> 20 ga watan Agustan 2009 – Aka sake Megrahi daga gidan yari wanda ke fama da cutar kansa saboda dalilai na jin kai.
> Mayun 2012 – Megrahi ya rasu a gidansa da ke Tripoli, yana da shekara 60.











