Ba ma zawarcin Jonathan a takarar 2027 - PDP

Lokacin karatu: Minti 3

Babbar jam'iyyar hamayya a Najeriya, PDP, ta ce babu ƙanshin gaskiya a rahotannin da ake yaɗawa cewa ta nemi tsohon shugaban ƙasar, Dokta Goodluck Ebele Jonathan da ya tsaya mata takarar kujerar shugabancin ƙasar a shekara ta 2027.

Jam'iyyar ta ce tana ta ganin ana yada wannan batu, sai dai labarin babu gaskiya a ciki.

Mai magana da yawun jam'iyyar na kasa, Ibrahim Abdullahi, shi ne ya musanta wannan labari a tattaunawarsa da BBC.

Kakakin ya ce: ''To abin da ke gaskiya shi ne ba rahoton gaskiya ba ne na cewa jam'iyyar PDP ta mika tiket dinta na takarar shugaban kasa zuwa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ko tana kira da ya zo ya yi takarar a 2027 mai zuwa.

Abdullahi ya kara da cewa: ''Abin da ya faru ni ne din nan na yi hira da danjarida, hirar da muke a kan wasu maganganu daban, sai a cikin hirar ya ambato tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan cewa mene ne tunaninmu a kansa?

''Ana kira kwanan nan na ya zo ya yi takarar shugaban kasa. 'Yan Najeriya na kira. Shi ne na amsa masa da cewa babu shakka ya cancanci ya yi din tun da dan Najeriya ne kuma yana da damar ya yi haka a fuskar doka kuma yana da wa'adi daya na takarar shugaban kasa. So fitowarsa ya yi takara ba illa ba ne a zamanshi dan Najeriya kuma babu abin da ya hana shi yin haka a idon doka.'' In ji kakakin.

Ya kara da cewa ta yaya ma za a ce sun yi zawarcin mutumin da daman shi dan jam'iyya ne - wanda jam'iyyar ce ya ce ta yi wa Jonathan din riga ta yi mishi wando.

Alhaji Abdullahi ya ce, su ko magana da Jonathan din ba su yi ba a kan takara, kuma ba su karkata akalarsu cewa sai shi kadai zai iya yin takara a jam'iyyar ta PDP ba.

Ya ce suna da gwamnoni 12 a yanzu haka, sannan suna da wadanda za su iya yin takarar ta shugaban kasa da dama, wadanda kuma 'yansiyasa ne fitattu.

Sai dai gain yadda jam'iyyar take fama da rarrabuwar kai da matsaloli na cikin gida da kan bijiro a lokacin neman takara, wasu na ganin tsohon shugaban kasar ka iya zamar wa jam'iyyar dan takara na maslaha.

A kan haka, ya ce ba shakka tsohon shugaban kasar yana da ta shi fa'idar idan da zai yi.

To amma a cewarsa jam'iyya ba za ta zauna zaman jiran mutum daya ba, wanda kuma mutumin nan ya ce idan ba a manta ba shi ne wanda jam'iyyar APC ta rika zaraci da karkata akalarta wajen kokarin ta kira shi ya yi mata takara lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari ya kare wa'adinsa.

'' A gaskiyar magana inda zai yi takarar da kuma jam'iyyar za ta ba shi takarar lalle zai iya, to amma matsalar ba a ba mutum irin wannan matsayi a zaune za ka fito ne ka nuna ra'ayinka ka nuna kwadayinka a kanshi,'' in ji.

Mai magana da yawun jam'iyyar ta PDP ya ce, duk wadannan maganganu ma da ake yi shi kansa tsohon Jonathan din bai nuna sha'awarsa da takarar ba.

''Idan ma ba a manta ba, ba da dadewa ba, kwanan nan matarsa ta fito ta ce babu abin da zai sa shi ya dawo ya sake neman shugaban kasa, babu abin da ya manta a bila balle ma a yi tunanin ya dawo neman shugaban kasa.'' In ji shi.

Ya ce: ''To shikenan mu kuma jam'iyyar PDP don mun fi kowa maita sai mu ce sai shi.''

Kakakin ya yi tutiya da cewa, ita jam'iyyar PDP ko ka yarda a yi da kai ko ka yi tafiyarka za ka dawo ka ganta.

Ya ce, tun da aka kirkiro ta har yanzu ita kadai ce ba ta canza sheka, ba ta canza ka, ba ta canza yanayinta ko sunanta ko akidarta ba, a tsakanin jam'iyyun Najeriya.

Har ma ya kara da cewa ita ce jam'iyyar da ta fi kowace jam'iyya dadewa a tarihin Najeriya.