Wace ƙungiya ce za ta lashe gasar Zakarun Turai a bana?

Asalin hoton, Getty Images
Ƙugiyoyin Arsenal da Inter Milan da Barcelona da kuma Paris St-Germain sun samu gurbi a wasan kusa da na ƙarshe a Gasar Zakarun Turai.
Yanzu kuma tunani ya fara komawa kan ƙungiyar da za ta kafa tarihin lashe gasar, wadda ake sauya wa fasali.
A ranar 24 ga watan Mayu ne za a buga wasan ƙarshe a birnin Munich na ƙasar Jamus.
Tuni dai masana harkokin wasanni suka fara tsokaci kan ƙungiyar da suke ganin za ta iya lashe gasar ta bana.
Ga bayanai game da ƙungiyoyin huɗu da kuma hasashen masana wasanni kan lashe gasar.
Paris St-Germain

Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar - wadda tuni ta lashe gasar League 1 ta Faransa - na ɗaya daga cikin ƙungiyoyin da ake ganin za su lashe gasar.
Fitaccen masanin wasanni nan ɗan ƙasar Sifaniya, Guillem Balague na ganin PSG ce za ta lashe gasar.
''Suna da duk wani abu da ake buƙata don lashe kofin, sun iya riƙe ƙwallo, a yanzu ƙungiyar na da ƙarfi, tana da masu kai hari, da na tsakiya haka ma masu tsaron baya'', a cewarsa.
Ya ƙara da cewa hanya guda da za a iya doke ƙungiyar ita ce idan ƴan wasanta suka tare a baya domin tsare gida.
''In dai suka tsananta tsare gida to sai an cinye su, amma idan za su fito, to komai zai iya faruwa'', a cewarsa.
Shi ma Phil McNulty, babban marubucin wasanni na BBC na ganin PSG ce za ta yi nasara a gasar.
''Suna da zaratan ƴan wasa masu kai hari, misali Ousmane Dembele da Khvicha Kvaratskhelia da a yanzu ke kan ganiyarsu, ga kuma Desire Doue da Bradley Barcola waɗanda matasan ƴanƙwallo ne masu hazaƙa '', in ji shi.
Ƙungiyar za ta kara da Arsenal a wasan na kusa da ƙarshe.
Inter Milan

Asalin hoton, Getty Images
Babban wakilin sashen wasanni na BBC, Ian Dennis ya ce Zakarun na Italiya na da ƙwarin gwiwar lashe gasar, saboda yadda ƙungiyar ke da ƙarfi musammna masu tsaron bayanta.
''Sun fi kowace ƙungiya da ta rage a gasar ƙarfin tsaron baya, kawo yanzu babu golan da ya kai Yann Sommer, hana ƙwallo shiga raga a wasannin gasar ta bana'', in ji shi.
Ya kuma ce ta ɓangaren masu kai hari ma, ƙungiyar na da maciya ƙwallo, musamman Lautaro Martinez da a yanzu ke kan ganiyar zura ƙwallaye.
Wannan ne karo na biyu a kaka uku da ƙungiyar ke kai matakin wasan kusa da na ƙarshe.
Ƙungiyar - da ke jan ragamar teburin Gasar Serie A - za ta kara ne da Barcelona a wasan na kusa da ƙarshe.
Arsenal

Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar Arsenal ce ta fitar da Real Madrid daga gasar a matakin kwata fayinal bayan doketa 5-1 gida da waje.
Wakilin sashen wasanni na BBC, Alex Howell na ganin ƙungiyar ce za ta lashe gasar.
''Duk da matsalolin da ƙungiyar ta fuskanta a bana, amma ta iya kai wa wannan mataki a gasar, ai kasan sun shirya wa gasar'', in ji shi.
Ƙungiyar ta Mikel Arteta - wadda ke matsayi na biyu a teburin Gasar Premier - ba ta taɓa lashe gasar ba a tarihi.
''Ta fannin tsaron gida, ƙungiyar na da ƙarfi sosai, haka idan ka duba ƴan wasan gabanta - haɗakar Saka da Martinelli da Odegaard - za su iya doke duk wata ƙungiya da suka ci karo da ita,'' in ji shi.
Barcelona

Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona ce ta fitar da Borussia Dortmund daga gasar.
Babban wakilin sashen wasanni na BBC, Simon Stone ya ce yana ganin ƙungiyar ta Sifaniya ce za ta lashe gasar, saboda yadda take ƙara farfaɗowa a baya-bayan nan.
''A yanzu ƙungiyar ta ƙara ƙarfi musamman bayanta da tsakiya da masu kai hari'', in ji Simon Stone.
Ƙungiyar - wadda ke matsayi na ɗaya a gasar La Liga - na da zaratan matasan ƴanwasa da ke haskakawa a fagen ƙwallon ƙafa.
Rabon da ƙungiyar ta lashe gasar tun 2015 lokacin da take da zaratar ƴanwasa irin su Lionel Messi.










