Rahoto na musamman ya wanke Donald Trump tare da sukar FBI

Asalin hoton, Getty Images
Wani rahoto da aka dade ana jiran fitowarsa ya yi kakkausar suka kan yadda hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka, FBI, ta gudanar da bincike kan zargin alakar Rasha da yakin neman zaben shugaban kasa na Donald Trump na 2016.
Rahoton wanda lauya mai bincike na musamman John Durham ya jagoranta ya ce binciken hukumar (Federal Bureau of Investigation) bai samu kwakkwaran nazari yadda ya kamata ba.
Lauyan ya zartar da cewa hukumar binciken laifukan ba ta samu cikakkiyar shedar mu'amulla tsakanin kwamitin yakin neman zaben Trump da Rasha ba kafin ta kaddamar da binciken ba.
Mista Durham ya ce akwai tarin kura-kurai ko kauce wa hanya da hukumar ta FBI ta yi tare da Ma’aikatar Shari’a ta Amurka, wadanda suka kai ga yin wannan bincike da ya ce an dogara ga bayanan sirri wadanda ba a tsaya an gudanar da kwakkwaran nazari a kai ba tun da farko.
Sai dai kuma wannan rahoto da lauyan na musamman ya fito da shi ya ci karo da na wanda aka yi a baya a kan aikin na hukumar ta FBI, wanda Babban Mai Bincike na Ma’aikatar Shari’a ta Amurka ya gudanar, wanda ya zartar da cewa babu wata sheda ta nuna bambancin siyasa da aka yi.
To amma inda rahotannin biyu suka zo daya shi ne cewa FBI ta yi kura-kurai a lokacin binciken da ta yi kan zargin alakar yakin neman zaben na Donald Trump da Rasha.
Sai dai a martaninta hukumar ta FBI ta ce ta yi duk abin da ya dace a batutuwan da wannan rahoto ta ambato.
Duk da cewa wannan sabon rahoto na Mista Durham zai dadada wa Mista Trump to amma bai ko kusan tabbatar da abin da shi Trump din ya taba kira da ‘’babban laifin karni’’ ba, abin da yake dangantawa da kutungwila da bi-ta-da-kullin siyasa da ya ce ana yi masa ba.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Mista Trump da magoya bayansa, sun yi amanna cewa rahoton na Durham zai bankado cikakken bayani na makarkashiyar da suke gani hukuma ta gwamnati ta yi domin shafa kashin kaji da bata sunan yakin neman zabensa.
Maimakon haka sai wannan rahoto ya zayyana abubuwan da ya bayyana a matsayin kura-kurai da son zuciya ko nuna bambanci da FBI ta yi.
A takaice dai binciken na Mista Durham ya kai ga tuhumar mutum biyu da aikata mugun laifi, wadanda kuma dukkaninsu an sallame su zuwa wannan lokaci.
Sai kuma lauyan hukumar ta FBI da ya amsa laifin daburta bayanan da ke kunshe a wata wasika ta intanet.
Ko ba komai dai ana ganin wannan rahoto zai samar da wata kariya ga Donald Trump a lokacin fafutukarsa ta neman tsaya wa jam’iyyarsa ta Republican takara a zaben shekara mai zuwa.
Kamar da kasa tuni ma har ya yi magana a kan rahoton wanda a iya cewa ya wanke shi sumul ko ba sabulu inda aka ruwaito shi yana cewa, rahoton ya nuna an yi wa al’ummar Amurka zamba.











