Wane ne zai maye gurbin Masari a Katsina?

A ranar 18 ga watan Maris ne za a gudanar da zaɓen gwamna a fadin Najeriya.

Katsina na daga cikin jihohin da ake ganin fafatawar za ta yi zafi.

Jihar Katsina ce mahaifar Shugaban Najeriya mai ci, Muhammadu Buhari, kuma ta ja hankalin al'umma a zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar, inda jam'iyyar PDP mai hamayya ta lashe zaɓen.

Ana sa ran fafatawa kan kujerar gwamnan jihar za ta fi zafi ne tsakanin jam'iyyun APC mai mulki, da PDP mai hamayya, sai kuma jam'iyyar NNPP.

Dikko Umar Radda - APC

Dikko Umar Radda, shi ne dan takarar jami'yyar APC mai jan ragamar mulki a jihar.

An haife shi ne a ranar 10 ga watan satumba, 1970 a karamar hukumar Charanchi.

Dan siyasa ne, kuma ya taba zama Shugaban karamar hukumar Charanchi.

Bayan Gwamna Aminu Bello Masari ya yi nasara a zaben shekara ta 2015, ya naɗa shi a matsayin Shugaban ma'aikata na gidan gwamnati.

Mukami na karshe da ya rike shi ne shugaban Hukumar kula da ƙanana da matsakaitan masana'antu ta Najeriya (SMEDAN).

Daga nan ya shiga takarar kujerar gwamnan jihar ta Katsina.

Garba Yakubu Lado - PDP

PDP ce babbar jam'iyyar adawa a jihar Katsina wadda ke fafutukar kwace mulki daga hannun jam'iyyar APC.

Sanata Garba Yakubu Lado shi ne dan takarar Gwamna na jam'iyyar ta PDP a zaben 18 ga watan Maris na 2023.

An haifi Yakubu Lado ne a shekara ta 1961 a wani kauye da ake kira Ɗanmarke cikin Karamar Hukumar Kankara.

Ya taba zama Shugaban Majalisar Ƙaramar Hukumar Kankara, daga shekara ta 1999 zuwa shekara ta 2002.

Bayan nan kuma ya zama ɗan Majalisar Wakilai tsakanin 2003 zuwa 2007.

An zabe shi a matsayin sanata mai wakiltar Kudancin Katsina a shekarar 2007 karkashin Jam’iyyar PDP.

Lokacin da yake sanata, Yakubu Lado ya tsaya takarar kujerar gwamna a shekara ta 2007 a jihar ta Katsina a karkashin sabuwar jam'iyyar CPC ta Shugaba Muhammadu Buhari a wancan lokaci.

Yakubu Lado ya sha kaye a hannun gwamna Ibrahim Shehu Shema na jam'iyyar PDP.

Daga bisani, bayan ya sauya sheka zuwa PDP, Sanata Yakubu Lado ya sake tsayawa takara a shekara ta 2019 tare da gwamna mai ci Aminu Bello Masari na APC inda ya sake shan kaye.

A wannan zaben na 2023 kuma, jam'iyyar PDP ta tsayar da shi a matsayin dan takararta.

Injiniya Nura Khalil - NNPP

Sabuwar jam'iyyar ta NNPP, ta zabi Injiniya Nura Khalil a matsayin dan takararta na kujerar Gwamna a zaben na 2023.

An haifi Nura Khalil ne a kauyen Rimi a jihar Katsina a shekara ta 1962 amma asalin sa dan Kauyen Kan-dawa ne cikin Karamar Hukumar Bakori.

Ya yi aiki ne akasari a ɓangaren da ba na gwamnati ba.

Sai dai ya yi aiki a asusun tara raran man fetur (PTF) a karkashin Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a zamanin mulkin Marigayi Janar Sani Abacha.

Ya fara siyasa ne a jam'iyyar ANPP a shekara ta 2002. An tsayar da shi takarar Gwamna a shekara ta 2003, amma bai yi nasara ba.

A shekara ta 2007, ya sake yunkurin tsayawa takarar Gwamna, saidai bai samu nasara ba.

Ya sake neman tsayawa takarar Gwamna a shekara ta 2011 a karkashin Sabuwar jam'iyyar CPC.

A halin yanzu, jam'iyyar NNPP ta tsayar da shi a matsayin Dan takarar ta na Gwamna a wannan zaben na 2023.

Sauran 'yan takara

Baya ga waɗannan ƴan takara uku, sauran da za su fafata a zaɓen na ranar Asabar sun haɗa da:

  • Bara'u Muhammad Tanimu na jam'iyyar A
  • Dankani Garba Sani na jam'iyyar AA
  • Aminu Ibrahim Trader na jam'iyyar ADC
  • Ahmed Murtala na jam'iyyar ADP
  • Kado Kabir na jam'iyyar BP
  • Abu Musawa Ibrahim na jam'iyyar LP
  • Abudllahi Ishaka na jam'iyyar NRM
  • Jafaaru Jino Ibrahim na jam'iyyar PRP
  • Zakari Ibrahim Babangida na SDP
  • Tukur Aude Ingawa Ibrahim na ZLP