Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ko firaiministan Indiya zai canza hali bayan rasa rinjaye a zaɓe?
- Marubuci, Soutik Biswas
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, India correspondent
Gwamnatin haɗaka ba sabon abu ba ne ga ƙasar Indiya.
Tana daga cikin ƙasashen duniya da aka samu gwamnatin haɗaka wadda ta kunshi jam’iyyu masu yawa, wadda ta kunshi jam’iyyu shida zuwa 12.
A tsakanin shekarun 1989 da 2004, babu wata jam’iyya da ta samu rinjayen da ake nema a manyan zaɓuka shida da aka gudanar a kasar ta Indiya.
Wasu daga cikin gwamnatocin hadaka da aka kafa sun zo da ƙalubale: a tsakanin 1989 zuwa 1999 an yi irin waɗannan gwamnatocin ƙawance sau takwas, kuma da dama daga cikin su sun rushe ba tare da daɗewa ba.
Sai dai wasu daga cikin muhimman sauye-sauye da bunƙasa na tattalin arziƙi da ƙasar ta samu sun samu ne a ƙarƙashin gwamnatocin haɗaka, wasu ma a ƙarƙashin jagorancin jam’iyyar Congress ko kuma BJP.
A karon farko daga shekarar 2014, Indiya za ta samu gwamnatin haɗin gwiwa kasancewar babu wata jam’iyya da ta samu rinjaye kai-tsaye.
Narendra Modi wanda a yanzu ya sha rantsuwar kama aiki a matsayin firaministan ƙasar karo na uku, jam’iyyarsa ta rasa rinjaye sanadiyyar ƙarin ƙarfi na jam’iyyun hamayya, inda yanzu zai dogara ga jam’iyyu biyu da ke cikin ƙawancen National Democratic Alliance (NDA) domin samun rinjaye a majalisa.
To amma ko Modi wanda ya mulki jihar Gujurat ƙarƙashin jam’iyyarsa wadda ta yi rinjaye kuma a matsayin firmanista kuma ya mamaye harkar siyasa a Indiya tsawon shekara 10 zai iya jimirin yin gwamnatin haɗaka?
Ko zai iya ajiye tsarinsa na yin bake-bake a kan mulki da ɗagawa saboda tarin magoya baya, tare da zama mai sauƙin kai ta yadda tafiya za ta yi daɗi tsakaninsa da jam'iyyun ƙawance?
Da dama na ganin cewa abin zai yi wahala ga Modi ya tafiyar da gwamnatin haɗaka a ƙare lafiya.
Jam’iyyu biyu da Modi ya fi dogara da su jam’iyyu ne na yankuna, wato Janata Dal (United) da jam’iyyar Telugu Desam Party (TDP).
Su biyun na da kujeru 28. Kowannen su na ƙarƙashin jagorancin gogaggun ƴan siyasa - Nitish Kumar da N Chandrababu Naidu – waɗanda dukkaninsu suka taɓa zama a ƙarƙashin ƙawancen da jam’iyyar BJP ta jagoranta, sai dai daga baya sun fice daga ƙawancen saboda saɓanin ra’ayi, musamman da firaiminista Modi.
A shekarar 2019, lokacin da yake jagorancin jihar Andhra Pradesh, Mista Naidu ya kira Modi da “ɗan ta’adda”.
Gwamnatocin haɗaka kan rushe musamman idan ɗaya ko biyu daga cikin jam’iyya uku da suka yi haɗakar suka yanke shawarar ficewa.
Mutane da yawa na ganin cewa samar da gwamnatin haɗaka ƙarƙashin Modi zai ƙara inganta mulkin dimokuradiyyar ƙasar. Suna ganin cewa haka zai rage kaka-gidan da Firaiministan ya yi, da ƙara samar da hanyoyin taka wa mahukunta burki da ƙara wa ƴan adawa da dimokuraɗiyya ƙarfi, haka nan zai ƙara wa ɓangaren shari’a da ƴan jarida ƴanci.
Atal Behari Vajpayee, ɗaya daga cikin ginshiƙan jam’iyyar BJP ya taɓa samar da gwamnatin haɗaka mai inganci a tsakanin shekarun 1998 zuwa 2004.
Shugaban ya sayar da kadarorin gwamnati, ya janyo masu zuba jari zuwa ƙasar, ya gina manyan tituna, ya sauƙaƙe harkar zuba jari tare da haɓɓaka fasahar sadarwar zamani.
Ya kawo ƙarshen shekarun da aka kwashe ana gwada ƙwanji ta hanyar gwajin makaman nukiliya, ya sassauta zaman tankiya da ake yi tsakanin Indiya da Pakistan tare da inganta alaƙar da ke tsakanin Indiya da Amurka.
Amma duk hakan sun faru ne saboda sauƙin kan Mista Vajpayee.
Sai dai gwamnatin haɗaka ta Modi ta sha bamban sosai da waɗanda suka gabace ta.
Duk da cewa ta samu ƙasa da kujerun majalisa 272 da ake buƙata domin samun rinjaye a majalisa, BJP na da kujeru 240, saboda haka har yanzu tana da ƙarfi sosai idan aka yi haɗaka.
Haka nan a baya gwamnatocin da jam’iyyu marasa rinjaye suka kafa sun samu nasara duk da cewa ba su da yawan kujerun da suka kai na BJP yanzu.
Jam’iyyar Congress ta taɓa yin haka da kujeru 232 a 1991 da kuma kujeru 145 a 2004 sai kuma a 2009 da kujeru 206.
Bugu da ƙari Modi na jagorantar jam’iyyar BJP ce wadda ke da ƙarfi fiye da na shekarun baya.
A baya BJP ta ta danne manyan ƙudurorinta da sukan janyo rarrabuwar kawuna, domin ta ɗauki wasu manufofi na jam’iyyun haɗaka.
Tuni jam’iyyar ta samu nasarar aiwatar da manyan ƙudurorinta – kamar ƙwace ƴancin yankin Kashmir da gina wurin bauta na Ram temple – a ƙarƙashin jagorancin Modi.
Shin, ko yanzu jam’iyyun da zai yi ƙawance da su za su buƙace shi ya jingine manufofinsa masu haifar da rarrabuwar kawuna? Musamman kalaman ƙin jinin Musulmai waɗanda yake furtawa gaba-gaɗi lokacin yaƙin neman zaɓe.
Duk wani haɗaka mai inganci na faruwa ne idan aka tafi da ra’ayin kowane ɓangare kuma aka yi aiki tare.
Babbar tambayar a yanzu ita ce waɗanne abubuwa ne jam’iyyun haɗakan za su samu fahimta a kansu tare da jam’iyyar BJP domin samar da haɗaka mai inganci?
Jam’iyyar Modi na ƙoƙarin ganin an aiwatar da tsarin yin zaɓen jihohi da na tarayya a a lokaci ɗaya, lamarin da ke cike da ruɗani, tsarin da ƙasar ta yi watsi da shi a shekarar 1967.
Haka nan jam’iyyarsa ta yi alƙawarin tabbatar da dokar bai-ɗaya ta rayuwar ƴan ƙasa. Wadda doka ce da wajibi ne kowa ya yi biyayya gare ta ba tare da la’akari da bambancin addini ko jinsi ba.
A baya mabiya addinin Musulunci da Hindu duk sun nuna adawa da ita.
Sai kuma batun sake jan iyakar ƙarfin majalisar dokoki, wanda shi ma ke cike da sarƙaƙiya, wanda aka tsara zai faru bayan shekarar 2026.
Jihohin ƙasar na yankin kudanci waɗanda suka fi arziƙi kuma ba su da yawan al’umma na zargin cewa Modi zai faɗaɗa majalisar, ta yadda jihohin tsakiyar ƙasa masu talauci da yawan al’umma kuma masu yawan mabiya Hindu, waɗanda kuma su ne ke goyon bayan jam’iyyar BJP - za su fi samun tagomashi.
Ga mutum wanda ya ya saba da yin abin da ya ga dama, sassauta ra’yoyinsa na siyasa domin daɗaɗa wa abokan haɗaka zai zama abu mai matuƙar wahala ga Modi.
To amma gogaggun ƴan siyasa da suka gabata sun san yadda suke sauya aƙida a lokacin da ya dace.
Shin Modi zai sauya tsarinsa, ko Modi zai sauya zuwa mutum mai karɓar shawara kuma mai la’akari da ra’yoyin wasu baya ga nashi?