Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kotu ta tura Doyin Okupe gidan yari kan badakalar naira miliyan 702
Wata Babbar Kotu a birnin tarayyar Najeriya Abuja ta yanke wa tsohon mataimaki na musamman ga tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, Doyin Okupr hukuncin ɗaurin shekara biyu a gidan yari.
A wata sanarwa da hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa ta’annati EFCC ta fitar ta ce Mai Shari’a Ijeoma Ojukwu ce ta yanke wa Mista Okupe hukuncin a ranar Litinin bayan samun sa da laifin badaƙalar naira miliyan 702.
Mista Okupe dai shi ne darakta na yaƙin neman zaɓen ɗan takarar shugaban Najeriya na jam’iyyar Labour, wato Peter Obi.
EFCC ce ta shigar da ƙarar wanda kotu ta ce hukumar ta yi nasara bayan gabatar da ƙwararan hujjoji da ke nuna cewa Mista Okupe ya karɓi kuɗaɗe lakadan na biyan wasu ayyuka a yayin da yake gudanar da aikinsa, kuma bai kai kudin asusun da ya kamata ba.
Tun a shekarar 2019 ne EFCC ta gurfanar da Mista Okupe a gaban kotu kan zargin almundahanar.
An zargi Okupe da karɓar kuɗaɗe daga ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara an sha’anin tsaro, waɗanda ya gaza yin bayani kansu.
An yanke masa hukuncin ɗaurin shekara biyun ne bayan kama shi da laifi 25 daga cikin tuhuma 59 da ake masa.
Tuhume-tuhumen dai sun ta’allaƙa ne a kan karɓar makuɗan kuɗaɗe kama daga naira miliyan 10, a wasu al’amura daban-daban daga shekarar 2012 zuwa 2015..
Hakan ya faru ne a lokacin da yake mataimaki na musamman kan sha’anin jama’a ga tsohon Shugaba Jonathan.
Sai dai kuma kotun ta bai wa Okupe zaɓin biyan tarar naira 500,000 kan kowace tuhuma da ake masa.
Wannan lamari dai ka iya kawo cikas ga yaƙin neman zaɓen Peter Obi.
Har zuwa wannan lokaci dai babu wanda ya ce komai kan batun daga lauyan Okupe har Peter Obi.