Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mece ce makomar Atiku bayan gwamnonin PDP sun yi watsi da batun haɗaka?
- Marubuci, Muhammad Annur
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 5
Yayin da wasu 'yan hamayya a Najeriya ke ta yunkurin hadewa waje daya domin tunkarar zaben 2027 wajen ganin sun kawar da gwamnatin APC ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu, gwamnonin babbar jam'iyyar hamayya ta kasar, PDP ta ce ba za ta narke cikin wata jam'iyya ba domin cimma wannan muradi.
Gwamnonin na PDP sun bayyana hakan ne kuwa duk da cewa akwai wasu jiga-jigai nata da suka hada da tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar da ake ganin sa tare da wasu ƴan hamayya, waɗanda ake tunanin za su ƙulla haɗakar gabanin zaɓen na 2027.
Baya ga Atikun akwai kuma tsohon gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir Ahmad el-Rufai, wanda ya bar jam'iyya mai mulki ta APC a kwanan nan da nufin yakar jam'iyyar a babban zaben na gaba.
Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin na PDP, a hirarsa da BBC ya ce a matsayinsu na babbar jam'iyyar hamayya suna nan a yadda suke kuma za su ci gaba da zama a haka, amma ba za su tafi wata jam'iyyar ba.
''Mu dai a jam'iyyance ba inda za mu je, a matsayinmu na babban jam'iyya na adawa a shirye muke mu bude fuka-fukanmu kowane mutum ko jam'iyya karama ko babba ta zo ta hada kai da mu saboda mu ba 'yan Najeriya dama idan aka zo zabe na 2027.
''Amma ba za mu bar jam'iyyarmu inda muke da gwamnoni 12 da sanatoci da kuma 'yan majalisar jiha da kansiloli da ciyamomi, mu je mu shiga wata jam'iyya wadda ko kansila ba ta da shi ba,'' in ji Gwamnan na Bauchi.
Kasancewar Atiku Abubakar, dantakarar jam'iyyar ta PDP a zaben shugaban kasar da ya gabata a 2025, inda ya zo na biyu a zaben bayan Tinubu na APC, ana kallon shi a matsayin na gaba-gaba wajen wannan hadaka, inda ake ganin matsayin na gwamnonin PDP tamkar kin amincewa da muradin na Atiku ne, shugaban kungiyar gwamnonin na PDP ya ce, su ma sun ji labari a kan batun.
''Ka san kowa yana da ra'ayinsa, mun ji labari yana wannan guje-gujen na komawa wani jam'iyya kuma bai taba tambayar mu ba kuma bai tuntubi jam'iyya ba kuma mun san yana da 'yancinsa yana da kima da zai yi abin da ya ga dama, amma mu ba inda za mu je muna inda muke tare da jam'iyya kuma muna masa fatan alheri,'' in ji Gwamnan.
Shugaban kungiyar gwamnonin na PDP ya kara da cewa babu wani laifi da jam'iyyar ta PDP ta yi musu da zai sa su fita daga cikinta su tafi wata jam'iyya, idan akwai wasu matsaloli kanana da suke da su za su tattauna ne a tsakaninsu domin su magance su, amma ba wai su gudu su je wata jam'iyya ba – ''gudu mu tafi mu bar jam'iyyarmu bai ma taso ba''.
Mece ce makomar Atiku?
Bisa ga dukkan alamu wannan wani sabon babi ne zai bude a tsakanin tsohon mataimakin shugaban Najeriyar kuma dantakarar shugaban kasar na jam'iyyar PDP a zaben da ya gabata na 2025.
A tattaunawarsa da BBC masanin kimiyyar siyasa daga Jami'ar Bayero da ke Kano, Farfesa Kamilu Sani Fagge, ya ce abu ne mawuyaci Atikun ya cimma burinsa na zama shugaban kasa muddin bai samu hadin kai daga jam'iyyarsa ta PDP da ma wasu 'yan hamayya ba - wato dai a samu babbar hadaka a tsakanin PDP da sauran manyan 'yanhamayya.
''Bisa ga dukkan alamu Atiku bai shawarci masu ruwa da tsaki a jam'iyyar ba - ya yi gaban kansa ne ya shiga neman wannan hadaka da wasu,'' in ji Fagge.
Ya kara da cewa, ''muddin idan ba zama suka yi ba suka tattauna a takaninsu, suka warware wannan sabani da bambanci ba zai yi wuya gwamnonin su zo su bi shi, hakan kuwa zai sa a rabu baram-baram.''
Farfesa Kamilu ya ce PDP tana ganin ita babbar jam'iyya ce da ba sai ta yi alaka da wata karamar jam'iyya ba sai dai su kananan jam'iyyu su je su yi hadaka da ita.
Me zai kasance idan aka tafi a ware?
Farfesa Kamilu Sani Fagge na ganin cewa idan har aka tafi a haka ba tare da an samu jituwa ba tsakanin gwamnonin ko kuma PDP din da Atiku Abubakar, sai dai a karshe ya tafi wata jam'iyyar kamar yadda ya taba yi a baya.
''Ai ya taba tafiya ya bar PDP kuma lokacin da za yi APC ma yana daga cikin wadanda suka tafi daga PDP suka shiga can zai iya yin haka ma a yanzu, saboda ya sha fita daga PDP ya je ya dawo,'' in ji malamin jami'ar Bayero.
Farfesan ya ce, ''Idan ya ga da burinsa ba zai cika ba a can PDP zai iya tafiya amma zai yi wuya hakarsa ta cimma ruwa, kamar yadda Buhari a baya ya sha tsayawa takara amma bai ci ba sai da ya yi hadaka da sauran 'yansiyasa da sauran bangarorin kasar.''
''To shi ma Atiku in har yana da wannan buri in ba haka ya yi ba da wuya ya cimma nasara, dalili kuwa shi ne idan aka duba dokokin zabenmu mutum ba wai kawai ya ci kuri'u mafiya rinjaye ba ne, a'a sai ya samo kashi daya bisa hudu na akalla jihohi 24, don haka in ba hadewa ya yi ba don ya yi karfi a wani bangare zai y wuya ya kai ga cin zabe.
'Matsalarmu ƙalilan ce'
Kungiyar gwamnonin na PDP ta nanata matsayarta cewa su a shirye suke su karbi kowa a yi tafiya tare a jam'iyyar domin cimma manufa.
Sanata Bala, ya ce,'' da yake um muka fi kowa yada da kuma 'yanjam'iyya a shirye muke mu karbik owa ko kuma kungiya da za ta shige mu don a samu maslaha amma ba daidai ba ne mu mu tashi mu bar jam'iyyarmu babu wani dalili da za mu bari.''
Ya kara da cewa, ''kuma ko me mutum yake nema shugaban kasa ko gwamna, ya neme shi a PDP saboda PDP tana da tarihi tana da mutane kuma ma yawancin masu batancinta su suka amfane ta.
Dangane da matsalolin da ake gani ita kanta jam'iyyar ta PDP tana fama da su, Sanata Muhammad ya ce, nan da watan Agusta za su yi babban taro inda za su zabi sababbin shugabanni, su yi sabon zubi.
''Tamu matsalar ma ta fi kowanne kankanta a cikin jam'iyyu na hamayya, muna tabbatar wa da mutane jam'iyyarmu tana nan lafiya za mu shawo kan 'yan matsalolin da ke damun mu, amma ba za mu je mu shiga wata jam'iyya wadda ko kansila ba ta da shi ba,'' in ji shi.