Yadda ƴan Afghanistan da ke zaune a Pakistan ke cikin fargabar tilasta musu komawa gida

Wata yarinya ƴar shekara goma ƴar Afghanistan.
Bayanan hoto, "Mahaifin Nabila ya taɓa shiga rundunar sojin Afghanistan kuma iyalinta na fargabar cewa za a mayar da su Afghanistan
    • Marubuci, Azadeh Moshiri and Usman Zahid
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Islamabad
  • Lokacin karatu: Minti 7

"Ina cikin tsoro," Nabila ta faɗa cikin kuka.

Rayuwar yarinyar ƴar shekarar goma ya takaita ne a gidansu mai ɗaki ɗaya da ke Islamabad da kuma hanyar da ke cike da datti a waje. Tun watan Disamba ba ta sake zuwa makaranta ba, lokacin da makarantar ta ɗauki matakin cewa ba za ta sake karɓar ƴan Afghanistan waɗanda ba su da shaidar haihuwa ta Pakistan ba.

Sai dai ko da ta samu damar zuwa, Nabila ta ce ba za ta iya ba.

"Wata rana ba ni da lafiya, sai na ji wani ɗan sanda ya zo neman yara ƴan Afghanistan," ta faɗa cikin kuka, yayin da ta faɗa mana cewa an mayar da ƴan uwan ƙawarta zuwa Afghanistan.

Nabila ba shi ne asalin sunanta ba - an sauya dukkan sunayen ƴan Afghanistan da muka faɗa a wannan labari domin kare su.

Babban birnin Pakistan da kuma birni mai makwaftaka da shi Rawalpindi, na fuskantar ƙaruwar ƴan Afghanistan waɗanda ake kamawa da tsarewa da kuma mayar da su gida, a cewar MDD.

Ta yi kiyasin cewa sama da rabin ƴan Afghanistan miliyan uku da ke zaune a ƙasar ba su da takardun zama.

Ƴan Afghanistan ɗin sun ce suna rayuwa cikin fargaba da kuma tsoron samamen ƴan sanda a kan gidajensu a kullu yaumin.

Wasu sun faɗa wa BBC cewa suna fargabar kada a kashe su idan suka koma gida. Waɗannan sun kunshi iyalai da ke zaune karkashin shirin gwamnatin Amurka, wanda shugaba Trump ya dakatar.

Pakistan na nuna ɓacin-rai yadda aikin kwashe mutanen ke tafiya, a cewar Philippa Candler, wakiliyar hukumar kula da ƴan gudun hijira ta MDD a Islamabad.

Hukumar kula da ƙaurar jama'a ta Majalisar Ɗinkin Duniya (IOM), ta ce an mayar da mutum 930 zuwa Afghanistan a farkon watan Fabrairu, abin da ya ninƙa alkaluman idan aka kwatanta da makonni biyu da suka wuce.

Aƙalla kashi 20 na waɗanda aka mayar gida daga Islamabad da kuma Rawalpindi, suna da takardun zama a wajen hukumar kula da ƴan gudun hijira ta MDD, abin da ke nufin an ɗauke su a matsayin mutane da ke buƙatar kariya ta ƙasa da ƙasa.

Azadeh Moshiri zaune a kasa.
Bayanan hoto, Hamed ta ce idan suka kira hukumar kula da ƴan gudun hijira ta MDD ba a ɗaukar waya.
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sai dai Pakistan ba ta cikin yarjejeniyar ƴan gudun hijira kuma ta sha nanata a baya cewa ba ta san da ƴan Afghanistan da ke zama a ƙasar ba a matsayin ƴan gudun hijira. Gwamnatin ƙasar ta ce tsare-tsarenta na aiki ne domin laluɓo ƴan ƙasashen waje da ke zama ba bisa ka'ida ba kuma wa'adin da aka ba su na ficewa na ƙaratowa.

Lokacin ya ƙaru amma yanzu an ayyana 31 ga watan Maris a matsayin ranar ficewa ga waɗanda ba su da biza, sannan 30 ga watan Yuni ga waɗanda ba su da takardu.

Ƴan Afghanistan da dama na cikin zullumi a daidai lokacin da ke cikin ruɗani. Sun ce samun biza na da wahala sosai. Iyayen Nabila sun yi imanin cewa suna da zaɓi ɗaya: shi ne su ɓoye. Mahaifinta Hamid ya taɓa shiga rundunar sojin Afghanistan, kafin Taliban ta karɓi iko a 2021. Ya fashe da kuka tare da bayyana yadda ba ya iya yin barci da daddare saboda halin da ake ciki.

"Na bautawa ƙasata amma yanzu ba ni da ƙima. Wannan aiki ya kasance abin takaici a wajena," in ji shi.

Ƴan uwansa ba su da biza, kuma ba sa cikin jerin waɗanda ke da izinin zama. Sun faɗa mana cewa ba a ɗauki kiran wayar da su ka yi wa hukumar kula da ƴan gudun hijira ta MDD ba.

BBC ta nemi ji daga wajen hukumar.

A baya gwamnatin Taliban ta faɗa wa BBC cewa dukkan ƴan Afghanistan su koma gida saboda "za su rayu cikin ƙasar ba tare da fargaba ba". Ta yi iƙirarin cewa waɗannan ƴan gudun hijira sun je ne don "neman kuɗi".

Sai dai wani rahoton MDD a 2023 ya nuna shakku kan tabbacin da gwamnatin Taliban ɗin ta yi. Ya gano cewa an kashe ɗaruruwan tsoffin jami'an gwamnati da kuma sojoji duk da amincewa da shirin yi musu afuwa.

Tabbacin da gwamnatin Taliban ta yi - bai yi wani tasiri kan mahaifan Nabila ba inda suka zaɓi guduwa idan suka ji cewa hukumomi suna kusa da su. Makwabta sun riƙa bai wa juna mafaka, yayin da dukansu suka yi ƙoƙarin kauce wa komawa Afghanistan.

MDD ta ce ƴan Afghanistan 1,245 ne aka kama tare da tsarewa a faɗin Pakistan a watan Janairu, sama da ninki biyu idan aka kwatanta da lokacin a bara.

Nabila ta ce bai kamata a tilastawa ƴan Afghanistan ficewa ba. "Kada ku kori ƴan Afghanistan da ke gidajensu - ba mu zo nan don zaɓin mu ba, tilasta mana aka yi."

Akwai alamun damuwa da kuma kaɗaici a gidansu. "Ina da kawa wadda ta zo nan sannan aka mayar da ita zuwa Afghanistan," a cewar Maryam mahaifiyar Nabila.

"Ta kasance kamar ƴar uwa, kuma mahaifiya. Ranar da aka raba mu ta kasance mai wuya."

Na tambayi Nabila abin da take son yi idan ta girma. "Mai tallan kayan ƙawa," in ji ta, tare da yi min wani irin kallo. Kowaye a cikin ɗakin ya koma yin murmushi.

Mahaifiyarta ta yi mata raɗa a kunne cewa akwai wasu abubuwa da yawa da za ta iya yi, zama injiniya ko kuma lauya. Burin Nabila na zama mai tallan kayan ƙawa shi ne abin da ba za ta taɓa cimma wa ba a karkashin gwamnatin Taliban.

Burin mahaifiyarta na ganin ta zama injiniya ko lauya ba zai taɓa cika ba- ganin irin tsauraran dokoki kan ilimin ƴaƴa mata da Taliban ta saka.

Sabon babi

Pakistan na da daɗaɗɗen tarihi na ɗaukar ƴan gudun hijira daga Afghanistan. Sai dai hare-haren kan iyaka sun ƙaru da kuma ƙara zaman tankiya tsakanin makwabtan biyu. Pakistan ta ɗora laifin hare-haren kan mayaƙa daga Afghanistan, abin da gwamnatin Taliban ta musanta.

Tun watan Satumban 2023, shekarar da Pakistan ta kaddamar da "shirin mayar da ƴan ƙasashen waje gida," mutum 836,238 ne suka koma Afghanistan zuwa yanzu.

A daidai wannan lokaci da ake shirin mayar da wasu, ana riƙe da wasu ƴan Afghanistan a sansanin Haji da ke Islamabad. Ahmad na cikin zango na karshe na shirin tsugunar da mutane na gwamnatin Amurka. Ya faɗa mana cewa lokacin da shugaba Trump ya dakatar da shirin don yin bincike, ya katse mata fatan da yake yi na karshe.

BBC ta ga wani abu da ya kasance takardarsa ta ɗaukar aiki daga wajen wata ƙungiyar yamma, mai suna Christian non-profit group a Afghanistan.

Ƴan Afghanistan sun yi zanga-zangar adawa da dakatar da shirin sake tsugunar da mutane na gwamnatin Amurka.
Bayanan hoto, Ƴan Afghanistan sun yi zanga-zangar adawa da dakatar da shirin sake tsugunar da mutane na gwamnatin Amurka

Makonni kalilan da suka wuce, lokacin da ya fita don yin sayayya, ya samu kiran waya. Ƴarsa ƴar shekara uku ce ta kira. "Ƴata ta kira, ka zo baba ƴan sanda sun zo, ƴan sanda sun zo kofan gidan mu," kamar yadda ya faɗa. Har yanzu matarsa na jiran buƙatar ƙara wa'adin biza da ta nema, kuma tana ta bai wa ƴan sanda hakuri.

Nan da nan Ahmad ya ruga zuwa gida. "Ba zan iya barinsu ba." Ya ce ya zauna cikin wata mota don jira yayin da ƴan sanda suka ci gaba da samamensu. Mata da kuma yaran makwabtansa sun ci gaba da tururuwar shiga cikin motar. Ahmad ya fara samun kiran waya daga mazajensu, inda suka roke shi ya kula da su. Sun samu tserewa zuwa cikin wasu itatuwa.

An tsare iyalansa na tsawon kwana uku a cikin "yanayi mara kyau", in ji Ahmad, wanda ya yi iƙirarin cewa an bai wa kowane iyali bargo ɗaya da guntun bireɗi ɗaya a kowace rana, an kuma kwashe wayoyinsu. Gwamnatin Pakistan ta ce ta tabbatar da cewa "babu wanda aka ciwa zarafi ko musgunawa yayin aikin mayar da su gida".

Mun yi yunkurin kai ziyara sansanin Haji domin tabbatar da abin da Ahmad ya fuskanta, sai dai hukumomi sun hana mu.

BBC ta nemi tattaunawa da gwamnatin Pakistan da kuma ƴan sanda ko samun sanarwa, sai dai babu ko guda ɗaya da ta samu.

Wannan matar ta yi iƙirarin cewa an tsare ƴar uwarta.
Bayanan hoto, Wannan matar ta yi iƙirarin cewa an tsare ƴar uwarta a sansanin Haji a Islamabad

Wasu iyalai sun zaɓi barin Islamabad da kuma Rawalpindi yayin da suke cikin fargabar tsarewa ko mayar da su gida. Saura kuma sun faɗa mana cewa ba za su iya yin haka ba.

Wata mata ta yi ikirarin cewa tana zangon karshe na shirin sake tsugunarwa na Amurka kuma ta yanke shawarar tafiya da ƴaƴanta mata biyu zuwa Attock, mai nisan kilomita 80 yamma da Islamadab. "Ko biredi ba na iya saya," in ji ta.

BBC ta ga wata takarda da ke tabbatar da cewa ta tattauna da hukumar IOM a farkon watan Janairu. Ta yi iƙirarin cewa ƴan uwanta na ci gaba da fuskantar samame a kullu yaumin.

Wani mai magana da yawun ofishin jakadancin Amurka a Islamabad ya ce suna "tattaunawar kut-da-kut" tare da gwamnatin Pakistan "kan makomar ƴan Afghanistan da ke karkashin shirin sake tsugunarwa na Amurka".

A wajen kofar shiga sansanin Haji, wata mata na jira. Ta faɗa mana cewa tana da biza amma na ƴar uwarta ya daina aiki. A yanzu ana riƙe da ƴar uwarta a sansanin Haji, haɗe da ƴaƴanta.

Jami'ai a can ba za su ba ri ta ziyarci iyalinta ba, kuma tana fargabar cewa za a mayar da su gida. Nan da nan ta fara kuka, "Idan ƙasata na zaune lafiya, me ya sa zan zo nan Pakistan? Kuma ko a nan ma ba mu zauna lafiya ba."

Ta nuna ƴarta wadda ke zaune cikin motarsu. Ta kasance mawakiya a Afghanistan, inda doka ta bayyana cewa ba za a bar mata su yi magana a wajen gidajensu ba, ballanta kuma waƙa. Na juya wajen ƴarta don tambayarta cewa ko har yanzu tana waƙa. Ta kalle ni. Ta ce "a'a."