Ƴan Afirka da ake ganin za su haska a Gasar Premier ta bana

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Ian Williams
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport Africa
- Lokacin karatu: Minti 6
Yaya za ta kaya da Salah bana a Liverpool?
Mohamed Salah zai iya bugan ƙirjinsa ya ce shi ne kan gaba cikin ƴan ƙwallon Afirka da suka taɓa taka leda a Gasar Firimiyar Ingila.
Amma yadda kyaftin ɗin na tawagar Masar ke murza leda, za a iya cewa kakar bara ba ta yi masa kyau ba, inda ita kanta ƙungiyar Liverpool ta gaza wajen yin kataɓus.
Ƙwallo 18 da ya zura ne a kakar bara, biyar a bugun fanareti- shi ne adadi mafi ƙanƙanta da ya zura tun zuwansa ƙungiyar a shekarar 2017, duk da cewa ya taimaka an zura ƙwallo sau 10.
Rauni ya hana ɗan wasan mai shekara 32 buga Gasar Kofin Afirka ta 2023, da kuma wasu wasanni, sannan abubuwa sun ƙara caɓewa a lokacin da aka hango shi yana musayar yawo da kocinsa na wancan lokacin, Jurgen Klopp.
Amma bayan Klopp ya bar ƙungiyar, da kuma kasancewar saura masa shekara 1 a kwantiraginsa, sai aka fara hasashen cewa ɗan wasan zai bar Liverpool, har aka fara cewa zai koma Saudiyya da tamaula.
Ana cikin wannan ne Salah ya sanar da cewa zai cigaba da zama a Liverpool, inda ya ce zai fafata domin gyara abubuwan da suka faru da ƙungiyar a kakar bara, inda ta ƙare ba tare da lashe wani kofi ba.
Yanzu tambayar da ake yi, ita ce yaya Salah zai kasance a ƙarƙashin sabon koci Arne Slot?
Yiwuwar sauya salon wasan ƙungiyar, daga yawan kai hare-hare, zuwa tsarin da ake kira da na 'Dutch' na (rarraba ƙwalo daga gida zuwa tsakiya, sannan a jefa wa ɗan wasan gaba) wataƙila zai iya yi masa daɗi kasancewar shekarunsa sun fara ja.
To sai dai akwai masu ganin cewa tsarin zai iya kawo cikas ga Salah, wanda ya fi son ƙwallon zurawa da gudu.
Liverpool ba ta ɗauko wani sabon ɗan ƙwallo ba, wanda hakan ya sa ake tunanin har yanzu shi ne zai ja ragamar ƙungiyar a kakar bana.
Amma abin jira a gani shi ne yadd za ta kaya da ɗan wasan a kakar bana, da kuma ganin ko ƙungiyar za ta sabunta kwantiraginsa a ƙarshen kakar.
Shin Minteh ya cancanci fan miliya 30?

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ɗaya daga cikin cinikin 'yan ƙwallo da aka yi a kakar bana shi ne na ɗan wasan ƙwallon Gambiya, Yankuba Minteh, wanda a kakar bara ya taka leda a ƙungiyar Feyenoord a ƙarƙarshin koci Slot.
Ɗan wasan mai shekara 20 ya koma Newcastle ne daga ƙungiyar Odense ta Denmark a Yunin bara a kan kuɗi kusan fan miliyan biyar, amma ƙungiyar ta tura shi aro domin ya ƙara gogewa.
Bayan ya zura ƙwallo 10 a wasa 27 a gasar Netherland, sai Everton da Lyon da Borussia Dortmund suka fara zawarcin ɗan wasan, amma Brighton ce ta samu nasarar ɗauko shi a kan £30m.
"Na yi farin cikin tura shi aro da aka yi a ƙungiyar Feyenoord," in ji Tom Saintfiet, wanda shi ne kocin da ya fara ba Minteh damar buga wa ƙasarsa ƙwallo a lokacin yana ɗan shekara 18 a tattaunawarsa da BBC.
"Wannan kakar ce mafi muhimmanci a gare shi idan sun ba shi goyon baya tare da ba shi dama. Ina da tabbacin idan kakar ta yi nisa, zai nuna bajintarsa sosai."
Cewa zai nuna bajinta, kamar yadda Saintfiet ya bayyana ya yi daidai, kasancewar Minteh matashin ɗan wasa ne mai gudu, da iya zara da iya zura ƙwallaye.
Lallai magoya bayan Ƙungiyar Brighton za su yi fatan ganin ya fara da taka leda da ƙafar dama.
Wane amfanin Partey zai yi a Arsenal?
Lokacin da Arsenal ta kashe £ 45m ($57.8m) a kan Thomas Partey a Oktoban 2020, an sa rai sosai cewa zai ƙara wa tsakiyar ƙungiyar ƙarfi.
Amma duk da buga wasa 95 a Gasar Premier a kaka huɗu da ya yi, har yanzu ɗan wasan na Ghana bai nuna bajintar da aka yi zato ba, saboda yawan jin rauni.
"Ba na tsammanin Partey yana cikin zaratan 'yan wasan da ake dogaro da su na gaba-gaba yanzu a ƙungiyar," inji James Cook na the Same Old Arsenal podcast a tattaunawarsa da BBC Sport Africa.
"Yanzu ba shi da karsashi sosai kamar yadda yake a baya. Dole akwai damuwa."
Amma mene ne ra'ayin koci Mikel Arteta a game da shi?
A kakar bara, Arteta ya fara wasa biyar na ƙarshen kakar da Partey, inda Arsenal ta lashe dukkan wasannin.
"Ina yi tunanin Arteta ya yi haka ne domin ya ƙara wa tsakiyar ƙungiyar ƙarfi," in ji Cook, wanda ya yi amannar cewa ƙungiyar na buƙatar ƙarin ɗan wasan tsakiya.
"Ba zai yiwu ka dogaro da Partey ba, wanda zai yi wahalar gaske ya kasance cikin lafiya har ƙarshen kaka."
A yanzu da ya rage saura masa shekara ɗaya a kwantiraginsa, idan har zai iya taimakon Arsenal ta lashe Gasar Firimiyar Ingila a karon farko bayan shekara 21, hakan zai iya zama masa ban-kwana mai kyau.
Ko tauraron Sarr zai haska a bana?
Tun kakar bara da sabon kocin Tottenham Postecoglou ya fara aiki ne aka fara ganin alamar zai yi amfani da ɗan wasan na tsakiyar Senegal.
Duk da raunin da ya samu a tsakiyar kaka a lokacin da ake hutun Afcon, ɗan wasan mai shekara 21 ya buga wasa 27 a Premier a kakar 2023-24.
Don haka, shin ɗan wasa Sarr, wanda ake kallo a matsayin ɗaya daga cikin zaratan 'yan wasan wannan zamanin a ƙasarsa, zai iya ƙara wa Spurs ɗin wani takaɓuc?
"Lokacin da ya koma Tottenham, wasu da dama sun nuna fargabar ba zai iya gasar ba saboda yanayin jikinsa da kuma wahalar gasar ta Firimiyar Ingila," in ji Babacar Ndaiye Faye said.
"Amma a kakar ta farko a ƙarkashin kulawar Postecoglou, sai ya ba mutane mamaki. Sai dai akwai buƙatar ya ƙara gogewa wajen tafiya da ƙwallo gaba, musamman wajen ƙoƙarin neman zura ƙwallo.
"Idan Sarr ya ƙara gogewa, Spurs za ta ga wani nagartaccen ɗan wasa."
Ɗan wasan na Senegal, a kakar bana dai za a zura ido a gani irin rawar da zai taka ne a ƙungiyar ta Tottenham.
Wa zai taimaki sababbin 'yan ƙwallon da suka je Ingila?

Asalin hoton, Getty Images
Kakar bara ce kaka ta biyu a tarihin Premier da ƙungiyoyin uku da suka shigo gasar suka yi ƙarfon kifi, inda dukansu suka koma a Gasar Championship a shekarar.
Yanzu Ipswich Town da Leicester City da Southampton za su dage wajen ganin sun kauce wa irin abin da ya faru da ƙungiyoyin Burnley, Luton da Sheffield United.
Ƙungiyar Leicester za ta dogara ne da 'yan wasan Afirka da ke ƙungiyar, sannan sun yi farin cikin sabunta kwantiragin da fitaccen ɗan wasan tsakiyar Najeriya Wilfred Ndidi ya yi.
Ɗan wasan Zambia Patson Daka da ɗan wasan gaban Ghana Abdul Fatawu ne suka jagoranci gaban ƙungiyar a kakar bara, inda su ukun suka zura ƙwallo 12 a Gasar Championship.
Ƙungiyar Ipswich ta dawo Premier bayan shekara 22, inda yanzu kyaftin ɗinta shi ne Sam Morsy ɗan ƙasar Masar, sannan akwai Axel Tuanzebe ɗan ƙasar DR Congo a cikin 'yan wasanta.
Haka ita ma Southampton tana da zaratan 'yan wasan Afirka, inda ake sa ran ɗan Najeriya Joe Aribo zai nuna bajinta a ƙungiyar sosai a bana.
Kwanan nan ne kocin Southampton, Russell Martin ya bayyana ɗan wasan gaban Najeriya wanda ya yi kakar bara a Ƙungiyar Trabzonspor a matsayin aro, a matsayin na daban bayan wasannin atisaye da suka buga.
Amma har yanzu ɗan wasan Ghana Kamaldeen Sulemana bai gama warware ba daga raunin wata 18 da ya yi, inda yanzu haka aka tabbatar ba zai buga wasansu na farko na sabuwar kakar ba.











