Ƙungiyar ƴandaban da ke jefa fargaba a zukatan mutanen Kamaru

    • Marubuci, Armand Mouko Boudombo
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Journalist - BBC Afrique
    • Aiko rahoto daga, Dakar
  • Lokacin karatu: Minti 4

A makonnin baya-bayan nan, cibiyar tattalin arzikin Kamaru ta gamu da hare-hare daga wata ƙungiya da aka yi wa laƙbi da 'microbes' - wato ƙananan ƙwayoyin halitta. Gungun matasan, galibi suna riƙe da adduna da wuƙaƙe, suna yi wa mutane sata suna kuma far wa mutanen da suka ƙi ba su haɗin kai.

A ƙarshen makon da ya gabata, birnin des Palmiers, wata gunduma a Douala ya kasance tsit ba yadda aka saba gani ba. Da ƙarfe 7:00 na yamma ta yi sai a fara rufe shaguna sannan mutane sun kulle kansu cikin gidajensu.

A jajiberin ranar, wani gungu ya ƙaddamar da hari a wata unguwa, lamarin da ya jefa tsoro a zukatan mutane kamar sauran yankunan Douala, babban birnin Kamaru.

"Sun yi wa wani rukunin gidaje ƙawanya," in ji Awa (ba sunanta na asali ba) wadda ta ga yadda harin ya kasance kamar yadda ta shaida wa BBC, tana nufin ƙungiyar matasan ta microbes.

A cewarta, da suka isa ranar Asabar, sun kai hari wani babban wurin shan shayi na Malibu da wasu wurare a shagunan bakin hanya.

"A ƙarshe sun kai hari kan masallacin birnin des Palmiers", in ji matar wadda har yanzu ke cikin kaɗuwa.

Mutane da dama da samamen ya shafa sun tsinci kansu a asibitin Cite des Palmiers bayan raunin da suka ji, in ji wata majiya a garin.

Ƙorafe-ƙorafe game da ayyukan ƙungiyar ya zama na yau da kullum ga mazauna Douala, birni mafi girma na Kamaru.

Tashin hankalin ya janyo yi wa wasu ɗaukan doka a hannunsu. Kwana guda kafin hare-haren cite des palmiers, an kashe wasu mambobi biyu na da ake zargi ƴan ƙungiyar ne a Nkomondo da New-Bell, bayan da aka zarge su da yi wa wani mutum fashi.

A cewar wasu rahotanni da aka samu a baya daga hukumomin yankin, waɗannan hare-hare sun faru aƙalla sau ɗaya a kowane lardi na birnin.

Hotunan ta'annatinsu da kuma irin martanin da al'ummar garin ke mayarwa ya yi kama da yaƙin sari ka noƙe. Hotunn hare-haren, da akasari ke karaɗe shafukan sada zumunta, na nuna matasa riƙe da adduna suna rikici da wasu riƙe da shebur.

Su wane ne microbes?

A yanzu babu wanda ya san asalinsu.

Ga Stéphane Nké daga ofishin ƙaramar hukuma, inda ake yawan samun hare-hare, 'ƴanbindiga" ne kawai da ke aikata ta'annati bayan ta'amali da miyagun ƙwayoyi.

A cewarsa, waɗannan mutane ba su da wata manufa, "idan ba haka ba, ba za su riƙa kai wa mutane hari ba," in ji shi.

Majiyoyi sun ce mambobin gungun matasa ne ƴan shekara 20.

Mista Aboubacar, shugaban unguwar Makea, birni na biyu a ƙaramar hukumar, ya kasance cikin shirin kai samame na makonni. Ya ce ya fahimci cewa "matasa a buge da ke yawan kai wa wasu matasan hare-hare, bayan samun saɓani a wani wuri a birnin."

Ya kuma bayyana lamarin a matsayin tashin hankali inda mutane daga wasu unguwannin suke zuwa su aikata laifi a yankunan da ba a san su ba. Sai dai ya ce wannan ba faɗan daba bane.

Idrissou Sarki, wani shugaban matasa a New Bell, ya ce ƴanƙungiyar microbes ba su da wani asali. "Sun fito ne daga kowane yanki na birnin," in ji shi.

Yadda gungun ke ayyukansu

Idrissou, wanda ke taimakawa wajen kare yankinsa daga ayyukan ƴandaban, ya ce daga abin da ya lura, sun shiga yankinsu da yawansu. Ana iya samun matasa kamar 30 riƙe da adduna a lokaci ɗaya inda suke yi wa mutane barazana kamar suna da matsala da wannan mutumin. Idan suka lura cewa akwai jami'an tsaro ko mutum na ƙin ba su hadin kai, sai su fara far wa masu wucewa.

Awa, wadda ta ga harin ranar 6 ga watan Oktoba a Cite des Palmiers, ta tuna yadda suka rufe hanya suke kuma yi wa mutane fashi ta hanyar amfani da adduna kan waɗanda suka ƙi ba su hadin kai.

A cewar ta, an shafe kusan minti 30 suna far wa mutane sai dai ƴansanda sun isa wajen ne bayan da ƴan dabar suka yi nasarar ƙwace wa mutane da dama kuɗaɗensu da wayoyinsu.

Galibin mutane ba sa iya ƙwatar kansu saboda maharan na kai musu harin ba-zato, in ji ta.

Ƙungiyoyin sa-kai a unguwanni

A yanzu hare-haren sun ragu a Makea sakamakon ayyukan ƙungiyoyin ƴansintiri, in ji Stéphane Nké.

"Mun shirya kanmu a nan tare da matasa ƴan sa kai. Duk lokacin da muka gan su, muna ce masu su ci gaba da tafiya", in ji Mista Aboubakar, wani babban jami'i a garin.

"Idan ba mu tunkare su ba, za su ci gaba da zama barazana har ma su riƙa kai wa gidaje hare-hare", in ji shi.

Hukumomin garin sun snar cewa sun kama mutane da dama da suka bayyana a matsayin ƴanbindiga da ke da hannu a tashin hankalin.

A tsakiyar watan Satumba, gwamnan yankin Littoral, Samuel Dieudonne Ivaha Diboua, ya ce mambobin gungun sun ci gaba da gudanar da ayyukansu saboda suna samun mafaka a wajen ƴanuwansu da ke unguwannin.

Ya yi alƙawarin ƙaddamar da yaƙi kan ƙungiyar.

Sai dai hare-haren na ci gaba da faruwa a yankuna daban daban kuma a kullum, abin da kuma ke jefa mutane cikin ɗimuwa.

A cewar Awa, "idan har ba mu magance wannan ƙungiya ba, mutane za su ci gaba da zama cikin fargaba."