Isra'ila ta fusata kan yadda manyan kawayenta suka juya mata baya kan Gaza

Asalin hoton, Reuters
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya zargi takwaransa na Birtaniya Sir Keir Starmer da na Kanada, Mark Carney da kuma shugaban Faransa Eammanuel Macron, da goyon bayan wadanda ya kira masu aikata fyade da kisan jarirai, bayan sun soki yadda yake gudanar da yakin Gaza.
Netanayhau ya sanya wani hoton bidiyo a shafinsa na X, bayan da wani danbindiga ya harbe wasu ma'aikatan ofishin jakadancin Isra'ila biyu a Washington a ranar Alhamis.
Wannan kakkausar suka ce ta gani ta fada daga Firaministan Isra'ilar da ya y iwa wasu daga cikin manyan kawaye ko shakikan kasarsa.
Dukkanin kasashen uku da ya yi wa wannan wankin babban bargo, sun fito fili sun yi Alla-wadarai da kisan da aka yi wa ma'aikatan ofishin jakadancin Isra'ilan biyu – namiji da mace wadanda ke shirin aure a tsakaninsu.
Shugabannin kasashen uku sun ma nuna goyon bayansu ga Isra'ila, bayan mummunan hari na ba-zata da Hamas ta kai wa Isra'ilar wata 19 baya.
To amma a farkon watan nan, manyan kawayen na Isra'ila – Birtaniya da Faransa da kuma Kanada, sun waiwayo kan ita ma Isra'ilar inda suka soke ta kan fadada yakin da take yi a Gaza.
Sun ce matakin ya wuce gona da iri – suka kuma bayyana halin da al'ummar Zirin na Gaza suka shiga sakamakon matakin da Isra'ila daa datse hanyar shigar da kayan agaji da cewa abu ne da ba za a lamunta ba.
Firaminista Netanyahu ya zargi takwaransa na Birtaniya Sir Keir da na Kanada da kuma shugaban Faransa, da nuna son ganin Hamas ta ci gaba da kasancewa a kan mulki.
Ya ce : ''Lokacin da masu kisan kiyashi, masu fyade, masu kashe jarirai da satar mutane, mun gode muku, kun mara baya ga rashin adalci. Kun mara baya ga rashin tausayi da imani, sannnan kuma kun saba wa tarihi.''
Jagoran na Isra'ila ya yi wadannan kalamai ne yayin da yake ci gaba da shan matsin lamba daga cikin gida da kuma waje kan fadada yakin na Gaza da jefa al'ummar ta Gaza cikin mawuyacin hali na rashin kayan agaji.
Gwamnatin Birtaniya ba ta mayar da martani ba kai tsaye, kan kalaman na Netanyahu, illa dai ta kara jaddada sanarwar da ta fitar a baya kalaman da ta fitar a baya na kiran dakatar da bude wuta a Gaza, da sakin ragowar Yahudawan da Hamas ke rike da su.
Sannan kuma Birtaniyar a wannan sanarwa ta nuna goyon bayan kirkirar kasar Falasdinawa, da za ta wanzu kafada da kafada da Isra'ila.











