Mai shigar da ƙara a Kotun Duniya ya nemi a kama Netanyahu da shugaban Hamas

...

Asalin hoton, Getty Images

Babban mai shigar da ƙara na Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (ICC) ya nemi kotun ta ba da umarnin kama Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da kuma jagoran Hamas a Gaza Yahya Sinwar saboda aikata laifukan yaƙi.

Karim Khan ya ce akwai hujjoji ƙarara da ke tabbatar da cewa ɓangarorin biyu sun aikata laifukan yaƙi da na lalata rayuwar ɗan'adam daga ranar 7 ga watan Oktoban 2023.

Kotun ta ICC da ke birnin Hague na bincikar ayyukan Isra'ila a yankunan Falasiɗnawa da ta mamaye tun daga shekara uku da suka wuce - da kuma ayyukan Hamas a baya-bayan nan.

Mista Netanyahu ya siffanta ba da umarnin kama shugabannin Isra'ila da ICC za ta yi a matsayin "abin takaici da zai jawo matsala a tsawon tarihi".

Ministan yaƙi na Isra'ila Benny Gantz - wanda riƙaƙƙen ɗan'adawar Netanyahu ne ya nuna adawa da matakin kotun ta ICC.

"Ba za a kwatanta shugabannin mulkin demokuraɗiyya ta ƙasar da ke fafutikar kare kanta daga ta'addanci - da shugabannin wata ƙungiya mai son ganin an zubar da jini ba, wannan rashin adalci ne babba," kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X.

A yanzu alƙalan kotun duniya ta ICC za su duba ko hujjojin da aka gabatar sun cancanci a kai ga bayar da izinin kama wani ba.

Za a iya ɗaukar tsawon makwanni ko ma wata kafin daga lokacin da kotun ta buƙaci a bayar da takardar kamen ko da kuma lokacin da alƙalan kotun za su zauna su yanke hukunci a kan hakan ba.

...

Asalin hoton, Reuters