'Wulaƙancin da likita ya yi min kan ciwona ya sa ban yi karatu ba a rayuwata'

Asalin hoton, Getty Images
Wannan labari yana cikin jerin labaran da BBC Hausa za ta gabatar bayan neman jin ra'ayoyin ƴan Najeriya a manyan fannonin da suka fi shafi 'yan kasar.
Wannan shiri ne na musamman da BBC ta tsara dangane shirin manyan zaɓukan da ƙasar za ta gudanar daga watan Fabrairun 2023.
Fannonin da za a yi duba a kai din su ne na tsaro da ilimi da tattalin arziki da lafiya da kuma cin hanci.
Daruruwan mutane ne suka aiko da labaransu, kuma za mu dinga wallafa 25, ɗaya a kowace rana daga 10 ga Oktoban 2022.
Daga cikin matsalolin da 'yan Najeriya ke fuskanta a ɓangaren lafiya akwai ƙarancin likitoci da ƙarancin kayan aiki da kuma yin kuskure wajen gano ainahin cutar da ke damun marasa lafiya.
A wannan karon, wani bawan Allah da ya nemi a ɓoye sunansa ya faɗa wa BBC Hausa cewa wulaƙancin da wani ƙwararren likita ya yi masa kan kan wani kumburi da ya fito masa a fuska, shi ne sanadiyyar hana shi karatu a rayuwarsa.
'Dalilin da ya sa ban yi karatu ba ke nan a rayuwata'
Mun bai wa mutumin, wanda mazaunin birnin Kano ne, suna Damina.
Damina ya samu kan sa cikin halin tashin hankali da tsangwama tun yana ɗan shekara huɗu zuwa biyar bayan wani malaminsu a makarantar allo ya mare shi.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Daga nan ne wani kumburi ya fito masa a wuya kuma ya yi ta girma, har ta kai ga ya daina zuwa makaranta.
"Har sai da na daina zuwa makaranta saboda ana tsangwama ta ana ce min mai ƙululu, ana yi min dariya," a cewar mutumin mai shekara 41 a yanzu. "Na shiga cikin ƙunci da damuwa a lokacin nan. Na daina fita daga gida."
An yi ta bai wa Damina maganin gargajiya sannan mutane da yawa suka dinga cewa ciwon hangun ne ke damun sa, kafin daga baya ya je asibiti.
"Daga baya na je asibiti, inda wani babban likita a Kano ya faɗa min cewa ruwa ne a fuskata amma za a yi min aiki."
Mutanen gari da wasu daga cikin ma'aikatan lafiya suka dinga cewa kansa (cutar daji) ce ke damun Damina suna ba shi shawarar cewa "idan aka yi maka aiki fuskarka za ta taɓe, gara a ci gaba da na gargajiya". Hakan ya jefa shi cikin firgici.
Sai dai kuma ran wannan ƙwararren likita ya ɓaci matuƙa sakamakon wata tambaya da Damina ya yi masa kuma ita ce dalilin da ya sa ba a yi masa aikin ba a Najeriya.
"Saboda mutane sun tsorata ni, sai na tambayi ƙwararren likitan cewa: 'Shin idan aka yi min aikin ba zai shafi fuskata ba?' Daga nan kawai sai ransa ya ɓaci ya dinga yi min faɗa, ya ce na fita daga ofis ɗinsa kuma ya fasa yin min aikin."
"Cikin ikon Allah bayan na yi arziki daga baya, sai na kai kaina Saudiyya, inda likita ya ce wata jijiya ce ta yawu wadda ya kamata ta shiga bakina amma sai take shiga kumatuna kuma take jawo kumburin.
"Wannan shi ne dalilin tsayawar karatuna."
Damina ya ce bayan ya daina zuwa makaranta sakamakon tsangwama sai ya koma kasuwa.
"Kuma Allah ya taimaka min na samu nasibi, har na sayi mota kuma na kai mahaifiyata asibiti a Indiya."
Yanzu haka Damina mai shekara 41 ɗan kasuwa ne kuma ya ce ya haƙura da karatun boko.
'Karɓar kuɗaɗe a hannun marasa lafiya da aka ƙirƙiro'
Shi kuma Usman Muazu Funtuwa mai shekara 41 ya tsinci kan sa cikin zullumi ne da fargaba bayan ƙirƙiro biyan kuɗi da aka yi a asibitin da yake zuwa a Jihar Kaduna.
Malam Usman ya gamu da lalurar kurumta a shekarar 2006 sakamakon zazzaɓin maleriya da ya yi fama da shi.
Ya shafe kusan shekara 10 yana zuwa ganin likita a Asibitin Koyarwa na Jami'ar Ahmadu Bello inda yake samun kulawa kyauta. Sai dai lamarin ya sauya a baya-bayan nan.
"A yadda nasan asitin ba a ba da ko kwabo wajen ganin likita, sai kuɗin fayil kawai da ake biya da ba su wuce N200 ba," a cewar Usman.
A cewar mutumin, da ya koma kan wata larura sai ga al'amura sun sauya.
"A wurin tarɓar marasa lafiya, sai an biya kuɗin fayil kuma na ƙaramin katin zuwa ganin likita kan N400. Sannan idan katin ya cika sai mutum ya sayi wani.
"Haka kuma za a biya N500 duk lokacin ganin likita, idan likitoci biyu mutum zai gani sai ya biya N1,000 a buɗe fayil, kuma idan an je wurin ganin likita sai an sake biyan N1,000.
"Hatta takardar neman taimako da ake bai wa marasa lafiya su kai wani wuri (to whome it may concern), sai mutum ya biiya N1,000 ko N2,000, wadda a baya na san kyauta ce ba a biya."
Usman ya ce baya ga dogon layin da ake bi wajen biyan kuɗi, "sai kuma mutum ya sake hawa wani layin na ganin likita.











