Falalar karanta Ƙur'ani a watan Ramadan

    • Marubuci, Ahmad Bawage
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Digital Journalist
    • Aiko rahoto daga, BBC Hausa, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 4

Watan Ramadana lokaci ne da al'ummar Musulmi ke dukufa da yin ibada domin samun rabauta daga Allah SWT.

Mutane suna kuma dagewa wajen aikata ayyukan alkhairi da zai ninka ladansu.

Harwayau, azumi na ɗaya daga cikin rukunai biyar na addinin Musulunci, kuma a watan ne aka saukar da Alƙur'ani Mai Girma.

Karatun Ƙur'ani na ɗaya daga cikin abubuwan da Musulmi ke dagewa da yi a lokacin azumi.

To shin ta yaya mutum zai iya kammala karatun Ƙur'ani cikin watan na azumi, kuma mene ne zai iya tauye ladan da mutum zai samu na karatun Ƙur'ani a cikin watan?

Mun tuntuɓi Malam Abubakar Abdullahi Goran Namaye, malami da ke zaune a birnin Kaduna, inda ya ce hanya mafi sauki da Musulmi zai bi wajen sauke Ƙur'ani a cikin watan azumi shi ne karanta izu biyu a kowace rana har tsawon kwanaki 30.

Malam Abubakar ya ce Musulmi zai kammala karatun Ƙur'ani ta wannan hanyar ba tare da ya matsa wa kansa ba.

"Amma ya tabbata a cikin Sunnah mutum ya sauke Ƙur'ani cikin kwanaki uku, kada ya gaza haka, a ce kowace rana mutum zai iya karanta izu 20," in ji Malamin.

Falalar karanta Alƙur’ani

Malam Abubakar Goran Namaye ya ce kowane lokaci idan mutum ya karanta Al-Ƙur'ani Mai Girma, a kowane harafi yana da lada goma.

"Manzon Allah SAW ya yi misali da cewa idan mutum ya karanta Alif-La-Min wanda ya kasance harufa guda uku, kowane harafi mutum yana da lada goma idan aka haɗa ya kama lada 30," in ji Malamin.

Ya ce falalar karanta Ƙur'ani Mai Girma yana da lada mara iyaka.

"Manzon Allah SAW ya faɗa cewa yayin da bawa ya kammala karatun Ƙur'ani mai girma, Mala'iku 60,000 ne ke taya shi da faɗin amin-amin ga duk addu'ar da zai yi," a cewar Malam Abubakar.

Ya ake son mutum ya kasance idan yana karatun?

Malamin addinin Musuluncin da ke jihar Kaduna ya ce yanayin da aka fi son mai karanta Ƙur'ani mai girma ya yi shi ne ya kasance yana da alwala kafin yin hakan.

Ya ce ana so kuma mai karanta Ƙur'ani ya fuskanci Alkibla a duk lokacin da yake karantun.

"Amma yanayin da aka fi son mutum ya karanta Ƙur'ani shi ne a cikin Sallah saboda shi ne mafi girman daraja," in ji Malamin addinin.

Ya ce idan hakan bai yiwu ba, ana son mutum ya samu dama na karanta Ƙur'ani yana zaune, yana kuma karantawa daki-daki kamar yadda ya tabbata na ka'idoji da kuma yanda shari'a ta tsara.

Kura-kurai da masu karanta Alƙur'ani ke yi

"Kuskure ne mutum ya zo yana haɗa baki ba tare da ya je gaban malami ya koya masa ba.

"Manzon Allah SAW ya ce fiyayyen cikinku shi ne wanda ya koyi Ƙur'ani sannan shi ma ya koyar da wani, in ka yi haka ka kasance mafi alkhairi daga cikin bayin Allah SWT," in ji Malam Abubakar.

Ya ce wajibi ne sai mutum ya je gaban Malaman addini ya koyi Ƙur'ani.

Malamin ya ce kuskuren da mutum zai yi shi ne ɗaukar Ƙur'ani haka kawai yana karantawa ba tare da ya je an gaban Malami masanin Ƙur'ani ya koya masa ba.

"Ina bai wa al'umma shawarar cewa mu yi iya ƙoƙarinmu wajen tsayawa kan iya abin da muka sani. Kada mutum ya ce dole sai ya je Bakara ko Al-Imrana ko Ma'ida ko Nisa'i. Ka dawo kasa ka fara Fatiha da Nasi da Falaki da kuma Suraul Ikhlas saboda wajibi ne ba a iya yin Sallah sai da Fatiha," in ji Malamin.

Ya ce da yawa daga cikin kura-kurai da mutane ke yi yanzu idan sun je koyon Al-Qur'ani shi ne za su ce sai daga Bakara za su fara maimakon farawa daga ƙasa su yi sama.

Har ila yau, Malamin ya ce kuskure ne mutum ya riƙa yin surutu lokacin da ake karanta Ƙur'ani saboda lokacin da ake karatun, rahamar Allah tana sauka, lada mara iyaka na sauka, nitsuwa na sauka, da kuma albarka.

Ya ce duk waɗannan ni'imomi da ke sauka ba za su yi tasiri kan duk wani bawa da yake surutu ba lokacin da ake karanta Ƙur'ani.

"Allah ya ce kuyi sauraro daga mai karanta Ƙur'ani sannan kuma kuyi shiru.

Malamin ya bayar da misalin cewa akwai kuskuren da direbobi ke yi na kunna AlƘur'ani cikin mota sannan mutane kuma suna ta yin surutu, ya ce wannan zunubi yake samu ba lada ba.

Wane abu ne zai sa mutum ya karanta Alƙur'ani bai samu lada ba?

Malam Abubakar Abdullahi Goran Namaye ya ce babban abin da zai sa mutum ya karanta Ƙur'ani sannan ya kasa samun lada shi ne ya yi ba don Allah ba.

Ya ce ko da a ce mutum yana karantawa yana samun kuskure hakan ba zai hana ya samu lada ba, inda ya ce mutum zai samu lada biyu.

Ya kuma ce abin da ke tauye ladan mai karatun Ƙur'ani shi ne karatu ba tare da ya je gaban Malami ya koya masa ba.

Har ila yau, Malamin addinin Musuluncin ya ce wani abu da zai sa mutum ya kasa samun lada idan ya karanta Ƙur'ani shi ne karatu a wajen da babu tsarki kamar shiga bayi.

"Wani abu kuma da zai sa a rasa samun lada shi ne mutum ya je cikin kasuwa ya buɗe murya ya yi ta karanta Ƙur'ani mai girma alhalin ana hayaniya, wannan zunubi mutum zai samu maimakon lada," in ji Malam Abubakar Goran Namaye.