WhatsApp ya dawo aiki bayan tsayawar wani lokaci a fadin duniya

Manhajar Whatsapp ta dawo aiki a Birtaniya da Najeriya da sauran sassan duniya, yana da ya tsaya na ɗan wani lokaci.

Kamfanin Meta mamallakin manhajar ya ce an warware matsalar amma bai fadi dalilin da ya jawo ta ba tun farko.

Tun da farko a ranar Talata da safe masu amfani da manhajar sun ce sun fara ganin matsalar ce tun kafin ƙarfe 8 na safe agogon GMT.

Fiye da mutum 12,000 ne suka wallafa ƙorafi kan hakan cikin ƙasa da awa ɗaya, a cewar sashen fitar da bayanai na manhajar.

Mutane da dama sun yi ƙorafi a shafukan sada zumunta cewar ba za su iya aika saƙonni ba.

A Najeriya ma mutane da dama ne Whatsapp dinsu ya daina aiki, inda har wasu suka dinga kashe wayoyi suna kunnawa da zaton matsalar daga wayoyinsu ne.

Akwai mutum biliyan biyu da ke amfani da manhajar WhatsApp a faɗin duniya.

Kuma manhajar na ɗaya daga cikin waɗanda aka fi amfani da su a Birtaniya da ƙasashe irin Najeriya.

Mutane da dama da suka yi so aika saƙwannin a ranar talata da safe sun kasa. kuma ba sa ganin sabbin saƙwanni.

A lokacin da matsalar ta faru, mai magana da yawun kamfanin meta ya ce "Muna sane cewa a yanzu mutane da dama ba sa iya aika saƙwanni amma muna ƙoƙrinmu don dawo da aikin Whatsapp nan ba daɗewa ba."

“Lamarin ya jawo tsaiko a abubuwa da yawa. Manhajar, wacce ke da tsarin sirrinta bayanai na saƙwannin mutane, ta yaɗu kamar wutar daji a tsakanin mutane a zamantakewa ta kowace fanni.

Tsayawar manhajar ya shafi ƙasashe da dama har da Australia da Ukraine.