Halin da malaman jami'o'in Najeriya suka shiga saboda rashin albashi

Jama'a da dama na mamaki kan yadda malaman jami'o'in Najeriya ke rayuwa a ƙasar ganin cewa sun shafe kusan wata biyar ba tare da gwamnatin ƙasar ta biya su albashi ba.

Wasu malaman dai sun shaida wa BBC cewa sun soma fita hayacinsu saboda rashin kuɗi, inda har wasunsu sun soma sayar da kayayyakin gidajensu.

Sai dai wasu malaman sun ce da dama daga cikinsu ba su dogara da koyarwa ba kuma lamarin da sauki.

Har yanzu dai an kasa cimma matsaya tsakanin malaman jami'o'in Najeriya da kuma gwamnatin kasar, lamarin da ya sa ɗaliban jami'o'in ƙasar ke ci gaba da zama a gida.

Tun a ranar Litinin 14 ga watan Fabrairu ne kungiyar malaman jami'o'i ta Najeriya, ASUU, ta tsunduma yajin aikin gargadi ga gwamanatin Najeriya na tsawon wata guda sai dai daga baya ƙungiyar ta mayar da yajin aikin na Illa Masha Allahu.

'Mun shiga wani hali'

A tattaunawar da BBC ta yi da wasu daga cikin malaman jami'o'in Najeriya, wasu daga cikinsu sun bayyana cewa suna cikin matsala sosai sakamakon 'baƙin talaucin' da suka shiga.

Wasu kuma sun bayyana cewa lamarin da sauƙi ba kamar yadda ake ruruta shi ba.

Malam Aminu Makama, wanda malami ne a Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi, ya shaida wa BBC cewa suna cikin wani hali.

Ya bayyana cewa sakamakon wannan yajin aikin, da dama sun fara sana'o'in da bai kamata a ce malamai suna yin irin su ba.

"Na san malamin da yake aikin feshi a gonakin mutane kuma babban malami ne wanda yake da digirin-digirgir" in ji Malam Aminu.

"Akwai waɗanda wallahi manyan malamai ne amma sun soma sayar da kayayyakin gidansu, kamar irin su talabijin da injin wanki da abubuwan yau da kullum saboda su tafiyar da gidansu.

"Akwai malaman da 'ya'yansu da yawa ba sa zuwa makaranta saboda ba su samu damar da za su biya kudin makaranta ba, kuma makarantun ba za su saurara musu ba."

'Muna noma kuma muna bincike'

Sai dai a cewar Malam Kabiru Danladi Lawanti wanda malami ne a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria, ya bayyana cewa ba wannan ne karo na farko da gwamnatin Najeriya ke riƙe musu albashi ba.

Sai dai ya ce bambancin baya da yanzu shi ne a halin yanzu kayayyaki a kasuwa farashinsu ya yi tashin gwauron zabi.

"Akwai abubuwa da yawa da malaman jami'a ke yi su rayu idan ana yajin aiki, shi yasa Allah ya ba mu ilimi, babu yadda za a yi Allah ya ba ka ilimi sannan kuma ya hana ka yadda za ka yi," in ji Malam Kabiru.

"Yawancinmu manoma ne gaskiya, yawancinmu kuma masu bincike ne, akwai ayyuka da suke zuwa, har ita gwamnatin da take fada da mu, tana ba mu ayyuka da za mu yi kuma mu samu abin da za mu rufa wa kanmu asiri."

Sai dai duk da cewa gwamnati ta rike albashin malamai, amma kungiyar ASUU na iya bakin kokarinta wurin tallafa wa malaman jami'o'i, kamar yadda Malam Kabiru Danladi ya bayyana.

Sai dai Malam Aminu Makama na Jami'ar Bauchi ya ce duk yawancin tallafin da ake bayarwa yana zuwa ne a matsayin bashi.

'Za a ji jiki idan aka ci gaba da yajin aiki'

Ita ma Bilkisu Sani Yero wadda malama ce a Jami'ar Jihar Kaduna, ta shaida wa BBC cewa kamar yadda ASUU ke taimakon wasu malamai, haka a jami'arsu ta Kaduna su ma suna da wata 'yar karamar kungiya wadda tana tallafa wa malamai.

Ta bayyana cewa dama ba dabara ba ce mutum ya zauna ya ce ya dogara da albashi kawai.

"Ko babu yajin aiki wani lokaci mutum zai iya samun wata matsala ko daga banki ko wurin biyan albashi ya maƙale ya dauki wata da watanni, dole a ce mutum yana da wata hanya da ke kawo masa kudin shiga," in ji Malama Bilkisu.

Sai dai ta ce idan aka ci gaba da wannan yajin aikin na tsawon lokaci, lamarin ba zai zo da sauki ba kuma jama'a da dama za su ji jiki.