Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda 'yan Najeriya suka kashe bilyoyin naira wajen neman ilimi a Turai cikin watanni uku
Yayin da dalibai musamman 'ya'yan masu karamin karfi a Najeriya ke ci gaba da zaman gida sakamakon yajin aikin malaman jami'a, wani bincike da babban bankin ƙasar ya gudanar, ya bayyana yadda a cikin watannin uku, 'yan kasar suka kashe fiye da dala miliyan 220 wajen neman ilimi a kasashen waje.
Binciken babban bankin ya gano cewa a tsakanin watan Disamba 2021 zuwa watan Fabrairun 2022 ne a kashe wadannan biliyoyin naira wurin fita waje karatu.
Sai dai hakan bai zo ma yan kasar da dama da mamaki ba, la'akari da yadda karatun jami'o'i a Najeriyar ke tafiyar hawainiya.
Daga bara zuwa bana daliban jami'o'i a Najeriya sun shafe kusan shekara daya suna zaman kashe wando a gida, a dalilin yajin aikin malaman jami'o'i.
A bana yara sun kasance a gida ne tun cikin watan Fabrairu, kuma yanzu haka Kungiyar ASUU ta tsawaita yajin aikin da tunanin karkato da hankalin gwamnati.
Kungiyar ASUU na ikirarin cewa gwamnati ta ki cika alkawuran da ta dauka a yarjejeniyar da suka kulla a baya, kuma akan haka suke ganin rufe makarantun ne kawai mafita gare su.
Fita kasashen waje karatu ga dalibai a Najeriya ba wani sabon abu bane, amma irin yadda aka fara kashe biliyoyi naira cikin dan karamin lokaci manuniya ce kan yadda dalibai da iyaye da ke da karfi ke yanke kauna da inganci da makomar ilimi a kasar.
Wani dalibi daga jihar Zamfara da ya je Ghana don neman ilimin ya fada wa BBC cewa shika-shikai daga cikin dalilan da suka sa ya bar Najeriya zuwa waje karatu akwai rashin kayan karatu na zamani, da kuma yajin aikin jami'o'i, wanda a cewarsa zai sa dalibi ya dauki lokaci mai tsawo kafin ya kammala digirinsa.
Sai dai kuma ba kowa ne ke da zarafin fitar ba, lura da yadda ake kashe makudan kudade, ga kuma faduwar darajar naira akan dalar Amurka da a mafi yawan lokuta da dalar ne ake biyan kudin makaranta.
'Ɗalibai na yanke kauna da Najeriya'
Dakta Aliyu Tilde shi ne kwamishinan ilimi a jihar Bauchi da ke Arewacin kasar, kuma a ganinsa abun kunya ne a ce gwamnatin Najeriya ta kasa warware wannan matsala ta yajin aikin malamai, wadda ita ke kara sa dalibai da iyayensu su yanke kauna daga karatu a Najeriya, su fara tunanin ketarawa kasashen waje neman ilimi.
''Wannan ina fadin abinda ke cikin zuciyar ko wane uba ne irina wanda ke da ya'ya a jami'o'in Najeriya.''
''Yanzu suna nan zaune a gida, toh idan ina da hali me ye zai hana in tura dana waje?'' In ji Dakta Tilde.
A na kukan targade kuma sai ga karaya, don kuwa bayan da malaman jami'o'in suka tsawaita yajin aikin da suka shafe tsawon lokaci suna yi da wata uku, suma takwarorinsu na fasaha da kimiyya wato 'Polytechnics' sun shiga yajin aikin na tsawon mako biyu, wani abu da ya kara dagula al'amura.
Sai dai akwai masu ganin cewa masu fada aji a kasar na ko oho ne da tafiyar hawainiyar karatun ya'yan talakawa ne saboda suna cikin masu kashe makudan kudade don kai ya'yansu kasashen waje neman ilimi.
Kuma idan har masu ruwa da tsakin suka zuba ido hankalin matasan ya tashi daga kan neman ilimi, za a shiga wani yanayi a Najeriyar da ba zai yi wa kowa dadi ba.