Abin da ya sa hare-haren ‘yan bindiga ke ci gaba da laƙume rayuka a Najeriya

Hare-haren yan bindiga

Asalin hoton, AFP

Wani rahoto da aka fitar kan matsalar tsaro a Najeriya na cewa a cikin watan Agustan da ya gabata an samu karuwar mutanen da ake kashewa a hare-haren ‘yan bindiga a ƙasar.

Rahoton ya ce karuwar na zuwa ne duk da matakan da hukumomin tsaro ke ɗauka da kuma nasarar da sojoji ke samu a ayyukansu a wasu sassan ƙasar.

Sai dai rahoton na kamfanin Beacon Consulting ya ce an samu raguwa a yawan sace-sacen mutane, da garkuwa da su domin neman kuɗin fansa.

Rahoton ya ce wannan na da alaƙa da far wa dazuka da kakabe kasurguman ‘yan fashin daji da jami’an tsaro ke yi.

Me rahoton ya kunsa?

Shugaban kamfanin Beacon Consulting da ya fitar da wannan rahoton, Dakta Kabiru Adamu, ya shaida wa BBC cewa bayanan da suka tattara a watan Agusta sun nuna an samu karuwar mace-mace a Najeriya da kashi 49 cikin 100 idan aka kwatanta da watan Yuli.

Ya ce a watan Yuli mutane 576 ne matsalolin tsaro ya yi ajalinsu, sai dai a watan Agusta adadin ya kai 859.

Sannan satar mutane domin neman kuɗin fansa ta ragu da kashi 28 cikin 100, a cewar rahotonsa.

Ya shaida cewa a watan Yuli an yi garkuwa da mutane 525, a Agusta kuma 380.

Wannan kuma na zuwa ne yayin da jami’an tsaro ke kara azama da zafafa ayyuka a jihohin da dama na Najeriya, wanda ke nuna cewa tsare-tsaren da suka gabatar a birnin Tarayya, Abuja da sauran jihohi 36 na tasiri.

Sannan akwai kasurguman ‘yan fashin daji da aka hallaka, wanda hakan ya taimaka wajen takaita satar mutane.

Me ya sa kashe-kashe ke karuwa?

Mazauna kauyuka da ke

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, 'Yan bindiga da aka tarwatsa a dazzuka na komawa kauyuka domin addabar al'umma

Dakta Kabiru Adamu, ya ce har yanzu akwai matsala a kauyuka, saboda barazanar tsaro na karuwa daga ‘yan fashin dajin da aka tarwatsa a dazuka.

Ya ce suna komawa ne yankunan kauyuka suna addabar mutane.

"Galibinsu – ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda- an tarwatsu su don haka sai suka koma rayuwa a ƙauyuka suna addabar mutane da karuwar hare-hare."

Ya bayar da misali da yankuna arewa maso gabas da ya ce ‘yan bindiga na zirga-zirga ba tare da wani tsari na kai-tsaye da ke bai wa kauyuka kariya ba.

Waɗannan su ke taka rawa wajen karuwar mace-mace a sanadin tsaro da ake samu daga kauyuka.

Mece ce mafita?

Dakta Kabiru, ya ce akwai bukatar bijiro da tsarin shiga kauyukan Arewa maso yamma da tsakiyar Najeriya da su Neja.

Ya ce jami’ai na taka rawar gani da ake ganin tasirinsu, sai dai akwai bukatar bijiro da tsarin hadin-kai tsakanin gwamnatocin jihohi da na tarayya, kan taswirar da za ta haɗa kan ɓangarorin tsaro a ƙasar.

Ya ce wannan za ta bude hanyar shawo kan matsalar da kuma shigar da nasu tsarin samar da mafita da kare kauyuka.

Sannan akwai barazanar satar mai da dole mahukunta su tashi tsaye su shawo kanta.

Saboda magance wannan fanin zai kara kudaden shiga da gwamnati ke samu, hakan kuma zai inganta ko samar da karin kudaden kashewa a fanin tsaro.