Yadda azabtarwar ‘yan bindiga ta sa DPO ‘kashin jini’

Asalin hoton, NPA
Iyalan shugaban ofishin ‘yan sanda na karamar hukumar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna a Najeriya sun ce jami’in na cikin matsanancin hali a hannun masu garkuwa da shi duk da naira miliyan 7 ta kudin fansa da suka biya.
Wani ɗan uwan DPOn, CSP Sani Gyadi-Gyadi, ya shaida wa BBC cewa an bukaci su biya kuɗin fansa har Naira miliyan 250, wanda ya fi karfinsu don haka suka bayar da abin da ke hannusu amma jami’in bai kuɓuta ba.
Musa Muhammad Gyadi-Gyadi wanda ya kasance babban yaya ga DPOn ya ce a duk lokacin da suka yi waya da ‘yan bindigar suna jin yadda ake lakaɗa wa jami’in duka.
Kuma ya shaida musu cewa azabar da yake ciki ta kai ga yana kashin jini.
A watan Yunin da ya gabata ne ‘yan bindigar suka sace, CSP Sani Muhammad Gyadi-Gyadi wanda ɗan asalin jihar Kano ne, a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa kama aiki a karamar hukumar Birnin Gwari, daga Panbegua a karamar hukumar Kubau ta jihar Kaduna.
Makusantan nasa dai sun ce duk da irin sintirin da suke yi wa rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna don ganin an ceto ɗan uwan nasu, har yanzu babu wani kwakkwaran yunkuri daga gare su.
'Sau biyu muna bada kuɗin fansa'
Musa Gyadi-Gyadi ya ce sau biyu suna tura kudin fansa, inda da farko bayan bukatar kuɗin fansa na Naira miliyan 250, sai da aka rinƙa bin ‘yan uwa kafin a tara miliyan biyar da aka aike wa ‘yan bindigar.
Amma sai ‘yan bindigar suka shaida musu cewa kuɗin abinci ne miliyan biyar din, don haka suka bukaci su aika kuɗin kati miliyan ɗaya da kuma siya musu babur.
End of Wasu labaran masu alaƙa da za a iya karantawa
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ɗan uwan jami’in ya ce sai suka sake haɗa miliyan biyu suka bai wa wani ya kai kuɗin daji, sai dai wanda aka bai wa kuɗin ya kai wa ‘yan bindigar sun hada da shi sun riƙe a daji.
Ya ce “muna magana da ɗan uwana ta wayar ‘yan bindiga wanda ya shaida ma na cewa duk ruwan daminar bana a kansa yake karewa, sannan ba shi da lafiya ya kamu da larurar kashin jini.”
“Ya roƙi mu ceto rayuwarsa, ya ce an ɗaɗɗauresu da sarka, kawai roko yake a ceto su, saboda bayan kashin jinin da yake yi, ya kamu da ciwon kashi da na kafa.
“Matarsa ma ta shiga cikin damuwa, saboda tsananin yanayi da yake ciki.”
Dan uwan ya ce sun tuntubi hukumar ‘yan sanda babu adadi domin ganin an taimaka musu. Sai dai har yanzu babu labari.
BBC ta yi kokarin ji daga bakin hukumomin ‘yan sanda a jihar Kaduna ta bakin kakakinsu, Muhammad Jalige, wanda ya bukaci a ba shi lokaci, amma bai ce uffan ba kawo yanzu.
Wannan ba shi ne karo na farko da ake samun jami’an ‘yan sanda cikin wannan yanayi ba.
Satar mutane domin karbar kudin fansa ba wai sabon abu ba ne a Najeriya, kodayake mahukunta na cewa suna kokari don magance matsalar.
Sai dai har yanzu barazanar ba boyayya ba ce, tana ci gaba da wakana.











