Lauyoyin Eto'o sun ce ba su san da batun gurfanar da shi a kotu ba

Lauyoyin, Samuel Eto'o sun musanta cewar an sanar da shugaban hukumar kwallon kafar Kamaru (Fecafoot) matakan shari'a a kansa.

A wani jawabi daga kamfanin lauyoyin Faransa, Vey & Associes ya yi watsi da zargin da aka yi wa fitaccen tsohon ɗan ƙwallon mai shekara 42 da cewar ''Batun zai shafi bata suna''.

Ya kara da cewar ba a sanar da Eto'o ba cewar an dauki wani mataki ko sanar da shi abin da ya shafi shari'a.

Ranar Juma'a aka zargi dan wasan da cewar yana fuskantar mataki na shari'a da ya shafi cogen wasa da cewar 'yan sandan Kamaru na tare da takardun da ake zarginsa da yin amfani da matsayinsa don amfanin kai da cin hanci da wasu zarge-zarge da dama.

Koda yake BBC ta samu rahoton, sai dai ba ta iya tantance sahihanci sa daga mahukuntan Kamaru ba.

Wannan ba shi ne karon farko da Eto'o ke fuskanta kalubale irin haka ba.

A makon jiya, wani rukunin mahukuntan wasanni a Kamaru ya aike da budaddiyar wasika ga Fifa kan cewar hukumar kwallon kafa ta duniya ta yi gum, duk da tuhume-tumumen da ake yi wa Eto'o da wasu mukarrabansa a hukumar kwallon kafar kasar.

Wadanda suka sa hannu kan wasikar sun hada da babban mamba a kwamitin Fecafoot, Guibai Gatama da mataimakin shugaban kwararrun 'yan kwallon kafar Kamaru, wadanda ke gabatar da babbar gasar tamaula ta kasar.

An yi zargin cewar tsohon dan wasan na Barcelona da Inter Milan da Chelsea ''na tursasa kansa ta hanyar da ba ta dace ba a kujerar shugaban kwallon ƙafar kasar (Fecafoot).''

Wasikar ta kara da cewar lamarin ya zama mai muhimmanci fiye da wanda ya shafi shugaban hukumar kwallon kafar Sifaniya, Luis Rubiales da 'yar wasa Jenni Hermoso, inda ta kai Fifa ta dakatar da Rubiales kwana 90 da tsara hanyar da aka dauka don ladabtar da shi.

Lokacin da yake mayar da martani kan wasikar kamfanin lauyoyi na Vey & Associes ya ce Eto'o ya yi tsare-tsare da yawa don sauya alkiblar hukumar kwallon kafar Kamaru da gudanar da mulkin da masu ruwa da tsaki suka mara wa baya.

Sun kuma kira wasikar da cewar mai hadari da ɓata suna, ya kara da cewar Eto'o ya bugi ƙirjin tsari da zai kawo karshen wasu daidaiku, waɗanda koda yaushe a shirye suke su yi duk abin da zai sa kada su rasa cin hanci da rashawa da suke karba.

A watan Yuni, wani rukunin kungiyoyi 'yan dagaji da ake kira Amateur clubs a Kamaru suka yi kira da Eto'o ya yi murabus da cewar ya kawo rashin bin tsari, inda suka kada kuri'a da mutum 11-1 suka buƙaci da ya kara gaba.

BBC ta nemi Fecafoot ta yi bayani kan batun da kuma zargen zargen da aka yi mata, amma ba ta mayar da martani ba.

A watan Agusta hukumar kwallon kafar Afirka, Caf ta fara wani bincike kan zargin da ake yi wa Eto'o da cewar ta karbi wasiku daga bangaren masu ruwa da tsaki a kwallon kafar Kamaru, za kuma ta duba dukkan korafin kan doka da da'ar Caf.

Jawabin na Caf ya kara da cewar zargin yana da girma, amma Eto bai da laifi har sai wata kotu ta tabbar da zargin da ake yi masa.

BBC ba ta samu jawabi daga Fecafoot ba kan binciken da Caf ke yi.

Lokacin da Eto'o ke kan ganiya an nada shi fitatcen dan kwallon Afirka karo hudu, wanda ya lashe Champions League uku da buga wa Kamaru wasa 115 da lashe kofin nahiyar Afirka biyu tare da ƙungiyar Indomitable Lions.