Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
"Zan iya bayar da raina kan buhun fulawa": Yadda ƴan Gaza ke cikin tsananin yunwa
- Marubuci, Swaminathan Natarajan and Gaza Lifeline programme
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- Lokacin karatu: Minti 7
"Dukkanin yarana na kuka saboda ba su ci abinci ba tsawon kwana huɗu," wani mutum a Gaza ya faɗa.
"Na je wurin rabon tallafin, ina fatan kawo buhun fulawa gida. Amma da muka kai, ban san me zan yi ba," ya faɗa wa Sashen Larabci na BBC.
"Na ceci waɗanda suka ji rauni, na ɗauki wadanda suka rasu, ko kuma na nemi fulawa? Na rantse da Allah, na zaɓi na mutu idan hakan na nufin zan kai buhun fulawa ɗaya ga yarana don su samu abinci."
Rashin abubuwan gina jiki, yunwa da kuma kashe-kashe a kusa da wuraren rabon tallafi na ƙara zama abubuwan damuwa a Gaza, yayin da mutane suka dogara da tallafin da ake rabawa ta hannun Gidauniyar Tallafi ta Gaza, wadda Amurka da Isra'ila ke goyon baya.
"Sama da Falasɗinawa 1000 sojojin Isra'ila suka kashe yayin da suke neman abinci tun bayan da Gidauniyar GHF ta fara aiki a 27 ga watan Mayu", a cewar Thameen Al-Kheetan, Mai magana da yawun ofishin yancin ɗan adam na Majalisar Dinkin Duniya.
"Zuwa 21 ga watan Yuli, mun samu mutum 1,054 da suka rasu a Gaza yayin da suke ƙoƙarin samun abinci; an kashe 766 cikinsu a wuraren rabon tallafi na GHF, da kuma 288 kusa da tawagogin tallafi na Majalisar Dinkin Duniya, ya kara faɗa wa BBC World Service.
Ƙarin mace-mace
GHF sun fara aikinsu a Gaza a ƙarshen watan Mayu, sun fara da raba tallafi mara yawa a wurare daban-daban a kudanci da cikin Gaza. Hakan ya biyo hana shigar da tallafi tsawon makonni 11 da Isra'ila ta yi, ba a shigar da abinci ba tsawon wannan lokacin.
Dr Mohammed Abu Salmiya ne daraktan asibitin Shifa a birnin Gaza, kuma ya ce yara 21 sun mutu sakamakon yunwa da rashin abinci cikin awanni 72 da suka wuce.
Kusan yara 900,000 a Gaza ne suka rasu sakamakon yunwa, kuma 70,000 a cikinsu na cikin halin rashin abubuwan gina jiki, ya fada wa BBC.
Suna fuskantar hauhawar yawan mace-mace, likitan ya yi gargadi, kuma masu fama da ciwon ƙoda da na siga ne suka fi shiga hatsari.
Wani mai magana da yawun ma'aikatar lafiya ta Hamas ya ce mutum 33, cikinsu yara 12, ne suka rasu cikin awanni 48 da suka wuce.
Adadin mace-macen da aka samu sakamakon rashin abinci sun kai 101, kuma 80 a cikinsu yara ne, tun daga farkon yakin a 2023, ma'aikatar ta ƙara.
Ana fuskantar yunwa
Daukacin mutanen Gaza na fuskantar yunwa, a cewar Shirin Samar da Abinci na Duniya (WFP).
"Rashin abinci mai gina jiki na ƙaruwa yayin da mata da yara 90,000 ke tsananin buƙtar kulawa. A ƙalla mutum ɗaya cikin uku ba ya iya samun abinci tsawon kwanaki," WFP ya bayyana a cikin wata sanarwa, ya ƙara da cewa:
"Tallafin abinci ne hanya guda da yawancin mutane za su iya samun abinci - farashin kilogiram na fulawa ya haura daya 100 a kasuwannin yankin."
A watan Maris, Israʼila ta rufe dukkanin hanyoyin shiga Gaza, lamarin da ya hana shigar da kayan masarufi da suka haɗa da abinci, fetur da kuma magunguna daga kai wa yankin - kuma ta dawo da kai hare-hare, bayan yanke yarjejeniyar tsagaita wutar da ta yi da Hamas.
Wannan matakin ya kuma hana shigar da muhimman abubuwa kamar magunguna, rigakafi da kuma kayayyakin aikin lafiya da asibitocin Gaza ke matukar buƙata.
Maʼaikatar harkokin wajen Israʼila a ranar Lahadi ta ce motoci 4,400 ɗauke da tallafi sun shiga Gaza tun daga tsakiyar Mayu. Ana kuma jiran wasu motocin 700 su isa ga Majalisar Dinkin Duniya, ta ƙara.
Israʼila ta kuma dage cewa babu ƙarancin kayan tallafi a yankin, kuma ta zargi Hamas da sace kayan tallafin don bai wa mayaƙanta ko kuma ta sayar.
'Mun zama mabarata'
"Yau, kilo daya na fulawa ya kai shekels 300 [$90] a kasuwa... kuma ba mu da hali," Ala Mohammed Bekhit ya fada wa Sashen Larabci na BBC. "Ba ma iya samun abubuwan amfanin yau da kullum."
Ta kuma yi magana kan hare-hare na kullum da mutanen da ke kusa da cibiyoyin ba da tallafi ke fuskanta.
"Wani saurayi na zaune kusa da ni, kawai sai aka harbe shi a kai," ta ce. "Ba mu ma san daga inda harsashin ya fito ba. Muna neman tsira kawai, amma mun gan mu cikin jini. Yau duk wanda ya samu fulawa sai da ya yi arba da harsasai."
Watan da ya wuce, Rundunar sojin Isra'ila ta fada wa BBC cewa tana binciken rahotannin "cutar" da fararen hula yayin da suke tunkarar cibiyoyin raba tallafi a Gaza mallakin GHF.
Jawabin ya kuma kara da cewa "ana binciken rahotannin cutar da mutane" kuma duk wani zargin laifuka da sojojin Isra'ila suka yi, kuma za a dauki matakin da ya dace.
Isra'ila ta zargi hukumomin Hamas na Gaza da kara yawan mutanen da suka mutu, amma ta yarda cewa "ta yi harbin gargadi" don kakkabe "wata barazana ta gaske".
Hari na baya-bayan nan
Wannan makon, tankokin Isra'ila sun shiga Deir al-Balah a tsakiyar Gaza karo na farko, lamarin da ya janyo mutane da dama suka kara rasa muhallansu.
This week, Israeli tanks have advanced into Deir al-Balah in central Gaza for the first time, triggering a fresh wave of displacement among civilians.
A ranar Lahadi, rundunar sojin Isra'ila ta bayar da umarnin barin unguwanni shida a kudancin Deir al-Balah, lamarin da ya janyo dubban iyalai suka bar gidajensu.
Fararen hula sun fada wa BBC cewa ba su da wurin zuwa.
Deir al-Balah na cikin wurare kalilan na Gaza da Isra'ila ba ta kai hari ta kasa ba cikin watanni 21 da ta shafe tana yaki da Hamas.
Majiyoyi a Isra'ila sun ce dalilin da ya sa sojojin ba su shiga Deir al-Balah ba shi ne suna zargin Hamas na rike da wadanda ake garkuwa da su a nan. A kalla mutum 20 cikin 50 da suka rage a Gaza na raye.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce wannan umarni da aka bayar a Deir al-Balah ta shafi dubban Falasdinawa, kuma ta yi mummunar illa ga ayyukan jin kai.
Yankin na kunshe da gwamman tantunan masu neman mafaka, wuraren ajiyar kayan tallafi, asibitoci da kuma kayan samar da ruwan sha.
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce an kai hari kan wuraren aikinta yayin harin Isra'ila a Deir al-Balah, kuma an kai hari sau uku kan gidajen ma'aikatanta, lamarin da ya bar mazauna - ciki har da yara cikin tashin hankali.
Hukumar ta ce sojojin Isra'ila sun shiga ginin, kuma sun daure tare da titsiye ma'aikatansu a wurin, kuma sun kama mutum hudu, inda aka saki uku daga baya.
Rundunar sojin Isra'ila ba ta ce komai ba dangane da wadannan abubuwa.
'Tashin hankalin da mutane suka samar'
Majalisar Dinkin Duniya ta ce ma'aikatanta za su zauna a Gaza don kare manyan abubuwan aiki, ciki har da wata ma'aikatar cire gishiri daga ruwa, duk da hare-haren na Isra'ila.
"Tashin hankalin da ke faruwa a Gaza mutane ne suka samar da shi," cewar Julitte Touma, Daraktar Yada Labarai a Hukumar kula da yan gudun hijira a Falasdinu.
Touma ta fada wa BBC cewa dakatar Isra'ila Unrwa daga aiki a Gaza da Isra'ila ta yi ya hana su kai motocin agaji 6,000 kai tallafi yankin.
"Cikin awanni 24 da suka wuce, ma'aikatanmu sun fada mana cewa wasu daga cikin abokan aikinsu sun fadi saboda yunwa yayin da suke aiki."
"Yunwar da matakin siyasa na hukunta mutanen Gaza ya haifar," ta kara da cewa.
A Nuwamban 2024, wani kwamitin alkalan Kotun Manyan Laifuka ta Duniya ya yanke cewa akwai "shaida mai karfi" cewa Firaministan Isra'ila da tsohon ministan tsaro Yoav Gallant na da "laifin amfani da yunwa a matsayin makamin yaki".
Amma Isra'ila ta musanta amfani da yunwa a matsayin makamin yaki, kuma Netanyahu ya kira zargin a matsayin "karyar da hankali ba zai dauka ba".
Ma'aiktar lafiya ta Gaza ta ce adadin mutanen da suka mutu a Gaza bayan hare-haren da Isra'ila ta kaddamar a Oktoban 2023 ya wuce 59,000.
Hakan ya biyo bayan harin da Hamas ta kai inda mutum 1,200 suka mutu, aka kumka yi garkuwa da 251.
An ayyana Hamas a matsayin kungiyar ta'addanci a kasashen Amurka, Birtaniya da kuma Isra'ila.