Yadda Boko Haram ta kai wa sojojin Najeriya harin 'ramuwar gayya'

Lokacin karatu: Minti 3

A ranar 4 ga watan Janairu ne mayaƙan Boko Haram na ɓangaren ISWAP, haye a kan babura masu yawa, riƙe da manyan makamai suka kai hari tare da buɗe wuta kan sojojin Najeriya a ƙauyen Sabon Gari a ƙaramar hukumar Damboa ta jihar Borno.

Cikin wata sanarwar da shalkwatar tsaron ƙasar ta fitar, ranar Laraba ta ce harin na ramuwar gayya ne, kan kisan da dakarun ƙasar suka yi wa wani kwamanda da wasu mayaƙan ƙungiyar.

Cikin sanarwar da daraktan yaɗa labaran shalkwatar, Manjo-Janar Edward Buba ya fitar, ya ce sojojin da ke komawa sansanin daga sintirin da suke yi ne suka shammaci mayaƙan a lokacin da suke shirin ƙaddamar da harin inda suka daƙile harin.

Nan take kuma sojojin suka samu ɗauki daga rundunar haɗin gwiwar farar hula, da ta ƙunshi ƴan banga da rundunonin tsaro, inda suka isa wurin a kan lokaci don murkushe ƴan ta'addar.

Haka kuma, rundunar kai ɗauki ta ci karo da abin fashewa da mayaƙan suka tayar lamarin da ya raunata babban kwamandan ƴan sa-kai, kamar yadda Manjo Janar Buba ya bayyana.

Ya ci gaba da cewa bayan gumurzu da mayaƙan na ISWAP ta ƙasa ne kuma, sai sojojin sama na rundunar 'Operation Haɗin Kai' suka bi 'yanbindigar da suka gudu ta sama suka riƙa sakar musu wuta.

''Kuma bayanan da muka samu na cewa sakamakon luguden wuta da aka yi musu ta sama an kashe mayaƙan da dama tare da wato makamai'', in ji shi.

'Mun kashe ƴan bindiga 34'

Sanarwar da shalkwatar tsaron ta fita ta kuma yi ƙarin haske kan mutanen da aka kashe a lokacin arangamar.

"Mun kash ƴanbindiga 34 tare da ƙwato bindiga kirar AK 47 23. Sannan sojoji suka ƙwato alburusai fiye da 200," a cewarsa.

''Sai dai abin baƙin cikin shi ne an kashe sojojin shida yayin gumurzun'', kamar yadda ya bayyana.

Tun farko rahotannin wasu jaridun Najeriya sun bayyana cewa sojoji bakwai aka kashe a lokacin gumurzun.

Wasu da suka zanta da BBC sun ce an yi artabu sosai tsakanin sojoji da ƴan bindigar waɗanda suka kai harin ba-zata.

Sun bayyana cewa mayaƙan sun ƙone motoci da kayan yaƙi na sojoji a sansanin nasu.

Wannan ne karo na biyu a cikin wata biyu da mayaƙan Boko Haram suka kashe sojoji a Najeriya.

A watan Nuwamban 2024, an kashe gomman sojoji a wasu hare-hare da mayaƙan suka kai kan sojoji a ƙauyen Kareto da ke ƙaramar hukumar Mobbar a Borno.

Haka ma a watan Disamban da ya gabata mayaƙan Boko Haram sun kai wa sojojin ƙasar Chadi hari inda suka kashe sojoji fiye da 40.

Lamarin da ya sa shugaban ƙasar Chadi, Mahamat Idris Deby ya yi barazanar ficewa daga haɗakar soji da ke yaƙi da ƙungiyar Boko Haram a Tafkin Chadi, bayan da ya zargi haɗakar sojin da rashin kyakkyawan tsarin gudanar da ayyukanta tare mambobinta wajen yaƙar Boko Haram.

Kodayake daga baya gwamnatin Najeriya ta aika tawaga zuwa ƙasar domin tattaunawa da shugaban kan yiwuwar janye kamalaman nasa.