Yadda Boko Haram ta ɗora wa al'ummomi haraji a jihar Borno

Lokacin karatu: Minti 2

Al’ummar garuruwan Gwange babba da Gwange ƙarami da ke yankin ƙaramar hukumar Kukawa a jihar Borno, sun koka kan sace ƴan uwansu da suka ce wasu ƴan Ƙungiyar Boko Haram ne suka yi.

Jama'ar garuruwan sun ce ƴan Boko Haram ɗin sun shiga ƙauyukan ne a cikin kwanaki biyu, inda suka sace aƙalla mutum goma da dabbobi da kayan abinci, kuma suka ɓullo da wani sabon salo na ɗora wa al’ummomin garuruwan harajin dole.

Lamarin ya jefa mazauna yankunan cikin wani mawuyacin hali, kamar yadda wani mazaunin yankin da ya buƙaci a sakaya sunansa ya shaida wa BBC cewa al’ummomin yankin na zaune ne a cikin tashin hankali da kuma fargabar dawowar maharan.

‘’Maharan dai sun afka mana ne da tsakar dare inda suka yi awon gaba da mutane guda tara, wanda akasarinsu matasa ne, sa’annan suka kwashi kayayakin abinci kuma suka ɗora wa ƙauyukan guda biyu harajin dole. Kowane ƙauye an ɗora masa harajin naira miliyan goma.’’ In ji shi

Ya ƙara da cewa maharan sun sake kai hari a wani yankin da ke arewacin ƙaramar hukumar inda suka auka wa wasu manoma, suka yi garkuwa da mutum biyu kuma suka ɗauke dabbobi da kayan abinci.

Ya ce: ''Yanzu dai a yankin arewaci babu wani makiyayi da ke cikin dajin, kuma babu wani ƙauye da mutane ke zaune a wurin. Yanzu dai ana cikin halin zaman ɗar-ɗar ne a wannan yankin.’’

Mazaunin ya kuma ce ba su ga wata alamar matakin da jami’an tsaro ke ɗauka ba duk da cewa sun sanar da su kan afkuwar lamarin.

Ya ce: ‘’Akwai jami’an tsaro a wasu garuruwa da ke yankin, amma yawanci ƴan Boko Haram ɗin da dare suke zuwa su kawo hari, sai su koma. An yi magana da jami’an tsaro amma har yanzu dai ba su ce komai ba.”

BBC ta tuntunɓi kwamishinan yaɗa labarai da tsaron cikin gida na jihar Borno Farfesa Usman Tar domin ji ko hukumomi na sane da afkuwar lamarin da kuma matakan da suke ɗauka amma ya shaida mana cewa bai sami wani bayani kan batun ba.

Jihar Borno dai ta shafe shekaru da dama tana fama da matsalar ƙungiyar Boko Haram, duk da cewa a baya bayan nan hukumomin tsaro sun yi iƙirarin cewa lamarin ya yi matuƙar sauƙi.