Yadda aka yi jana'izar mutanen da Boko Haram suka kashe a Jihar Yobe

..

Asalin hoton, Ibrahim Jirgi

Lokacin karatu: Minti 3

A yau Talata ne aka gudanar da jana’izar mutanen da ake zargin mayaƙan kungiyar Boko Haram sun kashe a ƙauyen Mafa na karamar hukumar Tarmuwa da ke jihar Yobe.

Ko da ya ke kawo yanzu dai hukumomin jihar Yoben ba su bayyana adadin wadanda suka mutu sakamakon harin ba, amma bayanan da ke ci gaba da fitowa daga yankin na cewa adadin wadanda aka kashen ya kai akalla mutum saba’in.

Bayanan sun ce mayakan wadanda ke kan babura sun fi dari dauke da makamai suka kai harin.

Tun da farko rundanar 'yansanda ta jihar Yobe ta tabbatar da al’amarin kuma ta bayyana cewa a yau ne za a yi jana’izar wadanda suka rasa rayukansu a harin wadanda kawo yanzu gwamnati ba ta fitar adadin wadanda aka kashe a hukumance ba.

Wani dan jarida a yankin, Husseini Jirgi ya shaida wa BBC cewa an wuce gawarwakin wadanda aka kashe asibiti:

''An kawo gawarwakin wadanda jami'an tsaro suka taho da su daga jeji, suna cikin wani babban asibitin inda ake ta shirya su tare da tantance adadin wadanda suka rasa rayukansu kuma an tabbatar da cewa za a yi jana'izarsu yau da safe'', in ji shi

Ya ce an samu bayanai da yawa da suka tabbatar da cewa mayakan Boko Haram ne suka aiwatar da harin.

''Sun riga sun bayar da gargadi tun ranar 30 ga watan Augusta a kan cewa dukkanin mazauna garin su fice, idan ba su yi hakan ba to za su kai mu su hari,'' kamar yadda ya shaida wa BBC.

Harin na zuwa ne bayan da aka ruwaito cewa wasu 'yan bindiga da ake zargin Boko Haram ne sun kai hari a wata makaranta da ke kusa da garin Geidam tare da kashe dalibai 3 da kuma raunta wani mutum daya.

..

Asalin hoton, Hussaini Jirgi

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A baya-bayan nan hare-haren mayaka da ake alakantawa da kungiyar Boko Haram na kara kamari a yankin na arewa maso gabashin Najeriya.

Yankin ya kwashe sama da shekara 10 yana fama da matsalar ta rikicin Boko Haram, wani abu da ya gurguntar da ayyukan tattalin arziki da haifar da rasa rayukan dubban mutane.

A baya an samu sassauci game da hare-haren, har ma gwamnatin tarayyar Najeriyar ta ayyana cewa ta ci galabar kungiyar, sai dai hare-haren na baya-bayan nan na neman mayar da hannun agogo baya.

Harin na ranar Lahadi a Mafa na zuwa ne yayin da miliyoyin al’ummar kasar ke cikin kaduwa sanadiyyar kona wasu manyan motocin sulke na sojojin kasar da ‘yan fashin daji suka yi a jihar Zamfara da ke arewa maso yamma.

Arewa maso yammacin Najeriya na fama da matsalar ‘yan fashin daji, inda shi ma abin ya ki ci ya ki cinyewa.

Gwamnatin kasar na cewa tana bakin kokarinta wajen magance matsalar, to amma har yanzu ‘yan bindigar na ci gaba da barnata rayuka da dukiyoyin al’umma.

A ranar Lahadi shugaban kasar Bola Tinubu ya umarci ministan tsaro da manyan hafsoshin sojin kasar su koma Sokoto - daya daga cikin jihohin da ‘yan fashin daji suka durfafa a kwanan nan - domin kara azama wajen kawar da gagaruman ‘yan fashin daji da ke addabar al’umma.

Abin da ba a sani ba shi ne ko wannan umarni na shugaba Tinubu zai yi tasiri, kasancewar irin sa da tsohon shugaban kasar Muhammadu Buhari ya bayar bai samar da wani sauyi ba game da hare-haren na ‘yan bindiga.