Yadda ma'aikacin banki ya riƙa naɗar bidiyon tsiraicin abokan aikinsa mata a Najeriya

Lokacin karatu: Minti 2

Rundunar ƴansanda a jihar Legas da ke Najeriya ta ce za ta gurfanar da tsophon ma'aikacin bankin Access wanda ake zargi da ɗaukar hotunan tsiraicin abokan aikinsa mata.

Wannan na zuwa ne bayan wata sanarwa da bankin ya fitar a ranar Litinin inda ya bayyana cewa ya miƙa batun zargin ɗaya daga cikin ma'aikatansu a ɓangaren hulɗa da abokan cinikayya, na ɗaukar hotunan tsiraici ga hukumomi.

Sanarwar da suka wallafa a shafin sada zumunta ta ce bankin zai bai wa hukumomi haɗin kai, kuma bankin zai ci gaba da kare mutuncin ma'aikatansa.

Bayani da ya fita a makon da ya gabata ya nuna cewa wani ma'aikacin bankin Access ya naɗi bidiyoyin abokan aikinsa mata a cikin ban-ɗaki ba tare da saninsu ba.

Rahotanni sun ce hukumomi sun kama wanda ake zargi sai dai an sake shi yayin da waɗanda ya naɗi bidiyonsu ke cikin damuwa.

Sai dai mai magana da yawun ƴansandan Najeriya a jihar Legas, Benjamin Hundeyin ya tabbatar wa BBC cewa an bayar da belin wanda ake zargin ne kafin kammala yin bincike.

"A yanzu kuwa wanda ake zargin ya sake kawo kansa wurinmu, yana tare da mu, za mu kai shi kotu domin gurfanar da shi," in ji Hundeyin.

Rahoton da aka bayar ya nuna cewa wasu ma'aikatan sashen hulɗa da abokan cinikayya na yin aiki har cikin dare, inda sukan kwana a bankin kuma sukan yi wanka a nan.

Sai dai an zargi ma'aikacin da cewa yakan shiga ban-ɗaki a sirrance ya ɓuya cikin, inda hakan ke ba shi damar naɗar bidiyon ma'aikata idan suna wanka. Sai dai an kama shi yana hakan ne a cikin ban-ɗakin mata.

"An kama shi ne lokacin da wata ma'aikaciya ke wanka sai ta ga alamar ana naɗar bidiyonta da wayar hannu," kamar yadda bayanai suka nuna.

Bayan ta yi ihu ne sai mutane suka shiga ban-ɗakin suka kama shi.

Bayan an duba wayarsa ta hannu da gidansa ne aka samu hotunan bidiyo har guda 400.

Wani bayani ya nuna cewa wanda ake zargin na sayar da bidiyon tsiraicin ne a shafukan sada zumunta, ya ce yana da masu saye.

Wasu daga cikin abokan aikinsa sun ce yana da shafin telegram inda a nan ne yake sayar da bidiyon na tsiraici.