Sojojin Nijeriya sun yi nasarar kashe ‘yan bindiga da dama tare da kubutar da wasu a jihohin Kaduna da Neja

Rundunar sojin sama ta Najeriya ta yi nasarar kashe ‘yan bindiga da dama wadanda ke kai hare -hare da kuma satar mutane a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna da yankin karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna .

Ta ce ta kaddamar da farmakin ne domin kakkabe ‘yan bindigar da suka addabi yankin,

Kakakin rundunar sojin sama ta Najeriya Air Comodore Edward Gabkwet ya shaidawa BBC cewa :

“An kashe ‘yan fashin dajin ne a tsaunin Doka da ke karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna”

“ Mun samu nasarar kashe ‘yan fashin daji ne bayan bayyanan sirri da mu ka samu kan kasancewar jagoran ‘yan bindigar da aka fi sani da Bodari tare da magoya bayansa a tsaunin na Doka”

Rundunar sojin sama ta Najeriya ta ce Bodari na cikin wadanda ‘yan fashin dajin da suka yi garkuwa da yara ‘yan makaranta a hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Ta ce tun farko sun samu bayyanai a kan cewa ba wuri daya Bodari ya ke zaune ba sai dai ta ce ba za ta iya tabattar da cewa ko an kashe shi ba:

“ Ba za mu iya tabattar ko an kashe Bodari da dan uwanshi Nasiru ba, amma mun san cewa mun yi nasara , an kashe wasu 'yan fashi daji a wajen”, in ji shi.

A wani labarin kuma hukumomi a jihar Nija da ke arewacin Najeriya sun ce wasu jami’an tsaro na sa kai daga jihar Bayelsa da jami’an tsaron kasar sun yi nasarar ceto sama da mutane 20 tare da hallaka 'yan bindiga da dama a jihar Neja.

Shugaban karamar hukumar Muye hon Najume Kuci ya ce sun shafe tsawon shekara biyar su na fama da matsalar 'yan bindiga da ke garkuwa da mutane a yankinsu wanda sakamakon kamari da matsalar ta yi ya sa su ka tunkari gwamnatin jihar.

"Shekaru kusan 6 hanyar Kaduna zuwa sarkin Pawa ba a iya bi, saboda hare haren 'yan bindiga, a makonin da suka gabata mun hadu da gwamna, ya ba mu mayakan sa kai wadanda suka fito daga jihar Bayelsa" in ji shi.

Yanzu da kawosu sun ceto mutane tara kuma daga bisani sun ceto wasu karin mutane kuma har yanzu suna kan aikin ceto mutane da aka yi agrkuwa da su.