Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Waiwaye: Taƙaddamar EFCC da Gwamna Matawalle da yajin aikin likitoci masu neman ƙwarewa
Waiwaye na wannan mako zai kawo muku abubuwan da suka wakana tsakanin 13 zuwa 20 ga watan Mayu da muke ciki, har da harin da aka kai kan jami'an jakadancin Amurka a Anambra da bajintar da Hilda Baci ta yi na shafe sa'a 100 da minti 40 tana girki a tsaye domin neman kafa tarihi a duniya.
Takun saƙa tsakanin EFCC da gwamna Matawalle na Zamfara
Bayan da hukumar EFCC a Najeriya ta fitar da sanarwa cewa tana binciken gwamnan jihar Zamfara Mohammed Bello Matawalle, kan zargin wawure kudin jihar fiye da Naira biliyan 70, gwamnan ya zargi shugaban hukumar Abdurrasheed Bawa da tafka almundahana iri-iri.
A cikin wata hira da BBC, gwamnan ya kalubalanci Bawa da ya sauka daga kan kujerarsa ya bayar da damar a bincike shi ya ga irin abubuwan da za a bankado.
Gwamna Matawalle ya ce “Bincike gaskiya ne, ba a hana a yi bincike ba, amma kuma ya kamata binciken ya zamo na kowa da kowa, don bai kamata a ce komai sai dai a ambaci gwamna ba, ai ba gwamna ne kadai ke da asusun ajiya ba.”
Ya ce, “Kamar yadda shugaban EFCC ya ce ya tanadi takardu na gwamnoni, to muna so ya nuna wa duniya takardu na wadanda yake aiki tare da su, sannan shi kansa ya kamata ya rubuta wa kansa takarda don a bincike shi saboda akwai zarge-zarge masu dumbin yawa a kansa.”
Sai dai ita ma hukumar ta EFCC ta kalubalanci gwamnan jihar Zamfarar, Bello Matawalle kan cewa idan yana da hujja a kan cewar shugabanta, Abdulrasheed Bawa na da hannu a ayyukan rashawa to ya kai kara wajen ‘yan sanda.
A lokacin da BBC ta tuntubi shugaban hukumar, Malam Abdulrasheed Bawa, ya ce ai babu wani ɗan'adama da yake 100 bisa 100 a duniya.
An dai shiga takun saka tsakanin gwamnan da EFCC ne bayan da hukumar ta ce ta aike da goron gayyata ga wasu gwamnoni da za su sauka a karshen watannan domin ta bincike su.
Daga cikin gwamnonin har da gwamnan na Zamfara Mohammed Bello Matawalle, inda ake zargin sa kan badaƙalar kuɗi sama da Naira biliyan 70.
Yajin aikin likitoci masu neman ƙwarewa
A ranar Larabar da ta gabata ne, Kungiyar likitoci masu neman ƙwarewa a Najeriya suka shiga yajin aikin gargaɗi na kwanaki biyar - zuwa ranar litinin 22 ga watan Mayu.
Likitocin dai sun ce suna neman gwamnatin Najeriya ta biya musu bukatunsu ciki har da inganta yanayin aiki da biyan kuɗaɗen alawus-alawus da ma albashinsu.
Yajin aikin dai ya durƙusar da ayyuka a asibitocin ƙasar. Marasa lafiya a asibitin koyarwa na Jami'ar Legas sun shaida wa BBC cewa ba su samu ganin likita ba saboda yajin aikin da ake yi.
Kungiyar na neman gwamnatin Najeriya ta warware matsalolinta kafin Shugaba Buhari ya bar ofis a ranar 29 ga watan nan.
Ganawar Kwankwaso da Tinubu a Paris
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar NNPP, Rabi'u Musa Kwankwaso ya yi wata ganawa da zaɓaɓɓen shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu a birnin Paris ranar Talatar da ta gabata.
Bayanai sun nuna cewa mutanen biyu sun shafe sa'o'i da dama suna tattaunawar.
Wata majiya da ba ta son a ambace ta, ta tabbatar wa BBC da ganawa a ƙasar Faransa.
Kwankwaso, wanda shi ne tsohon gwamnan jihar Kano ya zo na huɗu a cikin ƴan takarar shugaban ƙasa na 2023, inda ya samu ƙuri'u 1,496,687.
Duk da cewa babu cikakken bayani kan abin da tattaunawar ta ƙunsa, amma ana ganin cewa ba za ta rasa nasaba da shirye-shiryen kafa sabuwar gwamnati da za a rantsar a ranar 29 ga watan Mayu ba.
A halin da ake ciki, zaɓaɓɓen shugaban ƙasar, Bola Tinubu na ƙoƙari ne wajen ganin ya shirya yadda zai karɓi mulki ranar 29 ga watan Mayu.
A ranar Laraba 10 ga watan Mayu ne zaɓaɓɓen shugaban ƙasar ya bayyana cewa zai tafi wata ziyarar aiki a ƙasashen Turai.
Hare-hare kan Mangu da kwambar jami'an jakadancin Amurka
Wasu mahara, a makon da muke yi wa bankwana, sun far wa wasu ƙauyuka a ƙaramar hukumar Mangu da ke jihar Plateau tare da cinna wa gidaje wuta.
Lamarin ya tilasta wa hukumomi a jihar sanya dokar hana zirga-zirga a yankin Bwai na ƙaramar hukumar.
Wata sanarwa da ta samu sa hannun shugaban ƙaramar hukumar Mangu, Minista Daput, ta ce an amince da sanya dokar ne domin dawo da zaman lafiya, bayan harin da aka kai wanda ya yi sanadin rayukan kimanin mutum 20.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Plateau Alabo Alfred ya ce ba zai iya bayar da bayani ba kan lamarin saboda ana ci gaba da gudanar da bincike.
Sai dai ya ce shugaban ƙungiyar ci gaban al'ummar yankin, Joseph Gankat, ya ce adadin mutanen da suka mutu sun kai 85 kuma ana ci gaba da neman mutanen da suka yi ɓatan dabo.
Shugaban al'ummar Fulani a yankin, Adamu Usman shi ma ya faɗa wa BBC cewa mutum 30 cikin al'ummar yankinsa aka kashe.
A ranar Talata 16 ga watan Maris ɗin 2023 ne wasu ƴan bindiga a jihar Anambra suka afka wa ayarin Jami'an Ofishin Jakadancin Amurka.
Kwamishinan Yan Sandan Jihar ta Anambra, Echeng Echeng, ya bayyana cewar mutane bakwai da suka haɗa da ƴan sanda huɗu da ma'aikatan ofishin Jakadancin uku sun mutu lokacin da aka kai wa kwambar hari a hanyar Atani zuwa Osamala da ke ƙaramar hukumar Ogbaru.
Babu ɗaya daga cikin al'ummar Amurka ma'aikatan Ofishin Jakadancin da ya rasa ransa, amma biyu daga cikin jami'an ofishin sun ɓace amma an sanar da kuɓutar da su.
Mr Echeng ya ɗora alhakin harin kan ƴan awaren Ipob. Kodayake bai bayar da shaidar da za ta tabbatar da zargin ba.
Kwamishinan ƴan sandan ya ƙara da cewa sun yi nasarar kama wasu mutane biyu waɗanda a yanzu su ke taimakawa wurin bincike.
Bajintar Hilda Baci don neman kafa tarihi a duniya
Gwamnar girki a Najeriya, Hilda Effiong Bassey, da aka fi sani da Hilda Baci ta kafa tarihin girki a duniya, bayan shafe sa'o'i 100 da minti 40 tana girki a tsaye.
Hilda mai shekara 27, ta shafe wuni hudu tana girki domin kafa tarihin zarta Lata Tondon ta Indiya da ta shiga kundin tarihin bajinta na Guinness World Record.
Lata a 2019 ta shiga kundin Guinness bayan shafe sa'o'i 87 da minti 45 tana girki a tsakiyar Indiya.
Bajintar da Hilda ta nuna a yanzu ta zarta ta Lata, sai dai a hukumance ba a sanar da shigar da ita kundin Guinness ba.
Burin Hilda na kafa tarihi ya samu goyon-baya da yabo a shafukan sada zumunta.
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari na daga cikin fitattun mutanen da suka yaba wa Hilda Baci inda ya ce wannan abin alfahari ne ga 'yan Najeriya kuma kowa ya yaba da jajircewar da Hilda ta nuna.