'Mun fara karɓar tallafi don taimaka wa waɗanda gobarar tankar mai ta shafa a Jigawa'

Gwamnan jihar Jigawa a Najeriya ya shaida wa BBC cewa sun fara karɓar tallafi daga gwamnati da kuma ɗaiɗaikun jama'a yayin da adadin wadanda suka mutu sanadiyar hadarin tankar man fetur ya kai 170.
Malam Umar Namadi ya ce ƙarin wadanda suka rasun masu jinya ne a asibiti, waɗanda tuni ‘yan'uwansu suka ɗauki gawawwakin tare da yi musu sutura.
A ranar Alhamis ne gwamnatin Najeriya ta aike da wata tawaga, domin yi wa gwamnatin jihar Jigawa jaje da kuma ta’aziyya sakamakon tsautsayin da ya faru ranar Laraba.
Malam Namadi ya ce akwai ƙarin mutane 76 da suke kwance a asibitocin jihar da na birnin Nguru na jihar Yobe mai makobtaka.
‘’Mun zagaya asibitocin tare da tawagar shugaban ƙasa, kuma mutanen na ci gaba da karbar magani," a cewar gwamnan cikin wata hira ta musamman da BBC.
"Wurin da muke da marasa lafiya da yawa shi ne asibitin Nguru, kuma likitocin na tsaye a kan mutanen. Zan iya cewa akalla mutum biyu cikin 76 ne suke cikin mawuyacin hali, su ma muna fatan Allah ya ba su lafiya.
Ana ba su kulawa ne a manyan asibitoci biyar da suka haɗa da asibitin Malam Aminu Kano, da na Jahun, da Nguru, da Haɗejia, da kuma na Gumel.
Babbar jami'ar hukumar kiyaye haɗurra a Jigawa, Aishatu Sa'adu, ta ce hatsarin ya faru ranar Talata da daddare a garin Majiya na ƙaramar hukumar Taura.
Ta shaida wa BBC cewa ibtila'in ya faru ne a garin Majiya na ƙaramar hukumar Taura bayan da direban tankar ya kauce wa wata babbar mota ɗauke da tumatur.
'Tallafin da ya zo hannunmu zuwa yanzu'
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
BBC ta fahimci cewa dalilin da ya sa wutar ta kashe mutane da yawa shi ne ta tashi ne a daidai lokacin da dandazon mutane ke ɗibar fetur ɗin da ke zuba a motar da ta faɗi.
Zuwa yanzu hukumomi ba su bayyana abin da ya tashi wutar ba, wadda ta shafe kusan awa biyu tana ci kafin jami'an kashe gobara su kashe ta.
Gwamna Umar Namadi ya ce gwamnatin tarayya ta kafa kwamiti ƙarƙashin babban kwamandan kiyaye hadurra na kasa domin gudanar da bincike kan musabbabin iftila’in.
"Da ma mu ma a matsayinmu na jiha za mu gudanar da namu binciken," in ji shi.
‘’Gwamnatin tarayya ta yi mana alkawarin taimako ga wadanda wannan gobara ta shafa da iyalansu. Ta yi alƙawarin taimakawa da duk abin da ya dace ga mutanen nan.
"Sannan mun fara samun tallafi daga abokan arziki. Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya ba mu tallafin naira miliyan 100. Sai kuma sardaunan Dutse wanda ya ba mu naira miliyan 30. Waɗannan dai su ne tallafin da zan iya cewa sun shigo hannunmu."
A cewarsa, gwamnatinsa za ta kara da nata don ganin an taimaka wa mutanen nan "saboda babu abin da za a yi da zai biya su halin da suke ciki".
Ya kuma ce suna duba yadda gwamnatin jihar da hadin gwiwar hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar, wato SEMA, za su taimaka wa iyalan mutanen da lamarin ya shafa da abinci, da dukkan taimakon da suke bukata.
Motar dakon mai da ta kife ta taso ne daga jihar Kano a kan hanyarta t zuwa jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya.











