Matakan da za ku dauka domin kare kanku daga gobara

Bayanan bidiyo, Matakan da za ku dauka domin kare kanku daga gobara
Matakan da za ku dauka domin kare kanku daga gobara

A yayin da aka shiga lokacin hunturu wato sanyi ana yawan samun gobara a gidaje da ofisoshi da kasuwanni har ma a wasu lokuta da asibitoci.

Wannan kuwa na da nasaba da sauyin yanayi na kadawar iska wadda kan rura wuta ko da kuwa kadan ce.

To ko yaya mutane za su kaucewa tashin gobara musamman a lokacin hunturu?

A cikin wannan bidiyon, Aisha Shariff Baffa ta tambayi Injiniya Sani Sa’idu, babban jami’i a hukumar kashe gobara ta Najeriya, kuma shugaban hukumar a Abuja, inda ya yi mata karin bayani a kan abubuwan da ke haddasa gobara.