Fashewar tanka a Jigawa: 'Ina ce wa Najib ka dawo yana ce min baba ganima zan je ɗebowa'

Najib Alhaji Sani

Asalin hoton, Family

Bayanan hoto, Najib mai shekara 13 na cikin gidansu lokacin da tankar man ta faɗi a garin Majia
    • Marubuci, Nabeela Mukhtar Uba
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Broadcast Journalist
  • Lokacin karatu: Minti 6

"Najib zo mu tafi."

Wannan ce tattaunawa ta ƙarshe tsakanin Sani Kansila Majia da ɗansa Najib mai shekara 13, wanda iftila'in fashewar tankar mai a Jigawa da ke arewacin Najeriya ya yi ajalinsa a ranar Talata.

Fashewar tankar man da ta faru a garin Majia da ke ƙaramar hukumar Taura ta jihar Jigawa, ta halaka mutum 153 zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, yayin da wasu 100 ke jinya a asibiti.

Yayin da ake ci gaba da alhini da zaman makokin mutanen da suka rasa rayukansu, BBC ta zanta da wasu iyalai da tsautsayin ya rutsa da ƴanuwansu ciki har da mahaifin Najib.

Cikin kaɗuwa, mahaifin Najib ya shaida wa BBC cewa bayan da ibtila'in ya faru, shi da mai ɗakinsa suna kwance sai suka jiyo hayaniyar mutane a ƙofar gida.

Hakan ne ya sa ya tashi ya buɗe ƙofa domin gane wa idonsa abin da ke faruwa, inda ya bayyana cewa ya ga mutane suna ta gudu suna nufar wani wuri da aka ce wata tankar mai ta faɗi, kuma man da take ɗauke da shi ya malale magudanan ruwa har cikin gonaki.

"A je a ɗebi ganima, mota ce ta faɗi mai ya zuɓe." abin da Alhaji Sani Kansila ya ji mutanen da ke wucewa suke faɗi kenan.

A cewarsa, a lokacin ne kuma Najib shi ma ya fito daga gida riƙe da bokiti inda yake neman zuwa wajen da lamarin ya faru da niyyar kwaso abin da suka dinga "ganimar mai".

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Alhaji Sani Kansila ya ce a lokacin da ya ga Najib ya fito da bokiti, ya yi ƙoƙarin hana shi zuwa wajen sai dai yaron ya yi ta ce masa "baba ina zuwa" shi da wani abokinsa.

Duk da haka sai da ya ƙara bin ɗan nasa yana neman ya zo su koma gida. Amma da yake ajali ya yi kira, sai Najib ya sake kada baki ya ce: "A'a baba, ka je, gaskiya ina nan sai na taho".

Alhaji Sani ya ce jin hakan sai kawai ya koma gida, kuma komawarsa gida ke nan ya ji wata ƙara "dam". "Ina duba yamma sai na hango kawai wuta ce ta tashi."

Haka mahaifin Najib ya bazama waje domin zuwa inda ya baro ɗansa cikin fatan "Allah ya sa ba ya daga cikin ibtila'in."

Ya ce ko da ya isa wajen da ke da tazarar kilomita ɗaya daga gidansu, bai ga Najib ba. Ya sake komawa gida yana tambayar mahaifiyar yaron ko ya koma gida, amma ta ce ba ta ji ɗuriyarsa ba.

"Aƙalla na yi sintiri daga gida zuwa wurin fashewar sau huɗu amma ban ga alamun Najib ba," kamar yadda mahaifinsa ya bayyana.

Hankalin Sani Kansila dai bai kwanta ba game da rashin ganin Najib. Ya ga ana kai mutane wani asibiti da ke kusa da gidansu, inda nan ma ya leƙa amma bai ga ɗansa ba.

"Tun daga lokacin ne na saddaƙar cewa Najib yana ɗaya daga cikin waɗanda ibtila'in ya ritsa da su."

Sai dai ya ce abokin Najib da suka tafi tare ya tsira, inda ya ce abokin ya faɗa masa yadda aka yi suka rabu bayan sun tafi da niyyar zuwa inda tankar ta faɗi.

"Yaron ya faɗa mani cewa bayan sun tafi sai suka gamu da mahaifinsa a hanya kuma shi ne ya kira ɗan nasa suka koma gida."

A cewar mahaifin Najib, bayan da wutar ta lafa, cikin daren sun je tare da wani mai suna Surajo suka yi ta haska gawawwakin da fitila amma bai iya gano Najib ba.

Bayan sallar asuba ma, sun sake komawa wajen tare da wani yaro, a nan ma dai bai iya gano Najib ba sai dai ya gano fuskar mutum biyu - wani abokinsa mai suna Ƙasimu ɗansanda, da ɗan sirikinsa.

"Su kawai na shaida a wurin."

'Yaro mai biyayya'

Sani Kansila Majia ya bayyana cewa mutuwar Najib babban rashi ne a gare shi da sauran ƴanuwansa kasancewar "ɗa ne mai biyayya".

"Yaro ne da yake taimaka mana, mai haƙuri, ba ya faɗa, ba ruwansa da kowa." in ji mahaifin Najib.

Ya ce duk da cewa sun rasa Najib amma har yanzu "ba na iya barci, barci ya ƙaurace mani".

"Kullum abin da nake gani kamar gashi ya taho wajena. Har yanzu hankalina bai yarda da cewa ya rasu ba."

Saboda a har yanzu yana ganin kamar zai ga Najib ya koma gida, "ko an kawo shi daga wani garin ko ya shiga jeji ne bayan da lamarin ya faru."

"Abin yana min gizo ne har yanzu." in ji shi.

Ya ce ibtila'in ya ritsa da Najib, yaron da ya bayyana a matsayin mai burin ganin ya zama babban ma'aikaci don ya kula da iyayensa kasancewar mutuwa ta zo masa a lokacin da suke shirye-shiryen shiga babbar sakandare domin ci gaba da karatu.

'Ban taɓa ganin munin gobara irin wannan ba'

Fashewar tanka a Jigawa
Bayanan hoto, Gangar tankar man ke nan bayan da ta faɗi

Shi ma Sadisu Yahaya Majia, ɗaya ne daga cikin waɗanda ya samu tsira daga hadarin inda kuma yake jinya a asibiti.

A tattaunawarsa da BBC, Sadisu ya ce da aka samu malalewar man, ya je wajen kamar sauran mutane da dama domin ya kori ƙananaun ƙannensa da suka yi dandazo a wajen suna kwasar man da suka kira 'ganima'.

"Ba ɗiban mai bane ya kai ni, na je ne na koro ƙannena daga wajen, da yake muna nesa-nesa ma, sai abin ya ritsa da mu lokaci guda." in ji shi.

A cewarsa, wutar ta samu ƙafafunsa ne. Sai dai ya ce wutar ta tashi ne a lokaci guda kuma kasancewar man ya malale a wurare, wutar da ta tashi ta riƙa laso wuraren.

"Babu wanda ya je da ashana wajen, wurin birji ne, akwai tsakuwa wasu kuma suna zuwa da kwano suna ɗiba, sai suka haɗu shi ne wutar ta tashi." kamar yadda Sadisu wanda ganau ne ya bayyana.

A jawabinsa, bayan da wutar ta tashi, wurin cunkushe yake da mutane "yayin kokawar tsira, duka an haɗe wuri ɗaya, ba damar guduwa."

"Duk wanda ya samu guduwa, yana gefe-gefe ne." in ji sa.

Sadisu ya ce "mu da muka gano ta daga nesa, lamarin ya yi muni, ɗan burbuɗinta ya riske mu."

"Ba wanda zai iya kwatanta ma yanayin tashinta, kowa ma abin sabo ne a wajensa, don ko a labarai ba za ka taɓa jin irin wannan gobara ba, ta tashi sosai." a cewar Sadisu.

Sadisu ya ƙara da cewa a danginsu mutum biyar ne lamarin ya ritsa da su.

"Mun rasa mutane biyu, biyu kuma suna asibiti, sai ni. Ni iya ƙafafu ne daga gwiwa zuwa ƙasa."

'Na rasa ƙannena biyu a haɗarin'

Ɗaya daga cikin gawawwakin waɗanda hadarin ya ritsa da su ke nan
Bayanan hoto, Ɗaya daga cikin gawawwakin waɗanda hadarin ya ritsa da su kenan

"Ba mu taɓa wayar gari mu tarar sama da 100 sun mutu, sama da 100 suna asibiti ba." Abin da Umar Salisu ya ce ke nan, wanda ya rasa ƙannensa biyu ƴan shekara 18 da 16 a wannan iftila'in fashewar tankar mai.

Akwai kuma guda mia shekara 22 da yake jinya a asibiti, kamar yadda Umar Salisu ya faɗa wa BBC.

Ya ce abin da ya sani shi n, "ba a inda tankar ta faɗi gobarar ta tashi ba sai daga baya, wutar ta ƙarasa wajen tankar." in ji shi.

Ya bayyana cewa sun gano sun rasa ƙannen nasa ne bayan da aka ji su shiru, an neme su ba a gani ba, an duba asibiti ba a gan su ba.

Umar Salisu ya ce akwai waɗanda tsoro da fargaba ya sa suka gudu, "wasu ma sun karye ba su san sun karye ba."

A cewarsa, ƙannin nasa da yake jinya ba ya iya yin magana a halin yanzu saboda yanayin da yake ciki.

Ya ce burin ƙannen nasa da suka mutu shi ne na zama ma'aikacin lafiya, ɗayan kuma yana son ya karanci fannin nazarin gine-gine.