Ina ake kai kadarorin da hukumomin yaƙi da rashawa na Najeriya ke ƙwacewa?

Asalin hoton, X/EFCC
A Najeriya gwamanatin ƙasar ta sha fito da matakai da dama na ƙwace kadarori daga hannun waɗanda ake zargi da yin almundahana da dukiyar ƙasar.
Na baya-bayan nan da ya fi ɗaukar hankali shi ne makeken rukunin gidaje da aka ƙwace daga tsohon shugaban Babban bankin ƙasar, Godwin Emefiele.
Baya ga kadarori, hukumomin yaƙi da rashawa a Najeriyar kamar EFCC da ICPC lokaci zuwa lokaci suna sanar da ƙwato kuɗaɗe daga hannun waɗanda aka kama da laifin almundahana.
To ammaya ake yi da waɗannan kadarori da kuma kuɗaɗe da hukumomin ke ƙwatowa?
Bayan sanar da matakin ƙwace rukunin gidaje mallakin tsohon shugaban bankin na CBN, ƙungiyoyi da kuma mutane da dama sun yi ta bayar da shawarwari kan yadda ya kamata a yi amfani da su.
BBC ta tuntuɓi shugaban hukumar ICPC a Najeriya, Musa Adamu Aliyu kan yadda ake sarrafa dukiyar haramun da aka ƙwato daga mutane.

Asalin hoton, X/@icpcnigeria
Shugaban na Hukumar yaƙi da almundahana da dukiyar gwamnati a Najeriya (ICPC), ya ce akwai tsarin da ake bi wajen sarrafa dukiyar da aka ƙwace daga hannun waɗanda aka kama da laifi.
Ƙa'idojin na ƙunshe ne a dokar ƙwatowa da sarrafa dukiyar masu laifi ta Najeriya ta shekarar 2022, kamar yadda ya bayyana wa BBC.
"Bayan an ƙwace kaya bisa yadda doka ta tanada ana sayar da su, sai a sanya kuɗaɗen a asusun gwamnati, sannan kuma wasu kadadrorin shugaban ƙasa na da damar ya faɗi yadda za a yi da su.
"Akwai wani asusu da duka hukumomin yaƙi da rashawa ke amfani da shi a Babban bankin Najeriya domin ajiye kuɗaɗen da suka ƙwato kafin kotu ta yanke hukunci, idan kuma kotu ta yanke hukunci akwai wani asusun da ake sanya kuɗin, wanda hakan ke nufin sun tafi wurin gwamnatin tarayya," in ji shugaban na ICPC.
Waɗanne abubuwa za a iya yi da kadarori/kuɗaɗen da aka ƙwace?
Sashe na 72 na dokar ƙwacewa da sarrafa dukiyar masu laifi ya ce Shugaban ƙasa, bisa sahhalewar Majalisar Dokokin Tarayya na da ƙarfin bayar da umarnin a yi amfani da kuɗaden da aka ƙwace domin gudanar da ayyuka kamar haka:
- Inganta ɓangaren shari'a da daƙile aikata laifuka
- Ayyukan tabbatar da doka
- Ayyukan yi wa masu matsalar shan miyagun ƙwayoyi magani
- Sake tsugunar da mutanen da aka yi safarar su
- Inganta ɓangaren ilimi da lafiya da ci gaban matasa da samar da gidaje ko lantarki ko noma ko kuma samar da tsaftataccen ruwa
- Biyan diyya ko sauya halin waɗanda suka tuba daga ta'addanci
- Ayyukan jin-ƙai da walwalar al'umma
- Sauran ayyukan ci gaba da suka samu amincewar Majalisar Zartarwa da kuma Majalisar Dokokin Tarayya
Ko ICPC da EFCC na da ikon amfani da kuɗaɗen da suka ƙwace?
Shugaban na hukumar ICPC ya kuma ce "hukumomin yaƙi da rashawa ba su da damar amfani da kuɗaɗen da suke ƙwatowa daga hannun al'umma saboda doka ba ta ba mu damar yin hakan ba, shugaban ƙasa ne kawai yake da damar amfani da kuɗaɗen."
Ta yaya gwamnatin Najeriya ke ƙwace kadarori?
Shugaban ICPC ya ce "ana ƙwace dukiya ce ta hanyar zuwa kotu, inda kotu ce za ta tabbatar dukiyar ta haram ce ko a'a".
Hukumomi ba su da ikon ayyana dukiya a matsayin wadda aka ƙwace har sai kotu ta tabbatar cewa dukiyar an same ta ne ba ta hanyar da ta dace ba.
Musa Adamu Aliyu ya ce yanzu haka akwai wasu kuɗaɗe da hukumar ICPC ke riƙe da su tana neman kotu ta sahhale mata ƙwacewa kasancewar tana zargin cewa kuɗaɗe ne na haram.
"Mun ƙwato kudi sama da biliyan 20 waɗanda yanzu haka ake jiran kotu ta tantance matsayinsu kafin a miƙa su ga gwamnati.
"Haka nan yanzu haka akwai wasu kaɗaɗen a gaban Babbar kotun tarayya da ke Kaduna kusan biliyan 1.3 wadanda muke jiran a yanke hukunci kafin mu miƙa su ga gwamnati."

Asalin hoton, X/Multiple
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A Najeriya sau dama an sha samun gwamnoni da ministoci da sauran manyan masu riƙe da muƙaman gwamnati da laifin wawure kuɗaden gwamnati.
Misali shi ne baya ga rukunin gidajen da ke Abuja da aka ƙwace daga hannun Godwin Emefiele, akwai kuma wasu kadarorin da kuɗaɗe a wasu sassan ƙasar da ake ci gaba da taƙaddama a kansu, musamman a jihar Legas, kamar:
- Gini mai hawa 11 - Ikoyi, Legas
- AM Plaza, mai hawa 11, Lekki Peninsula 1, Legas
- Imore Industrial Park, Ƙaramar hukumar Amuwo Odofin, Legas
- Mitrewood and Tatler Warehouse, Ibeju-Lekki, Legas
- Gine-gine buda biyu da ke Lakes Estate, Lekki, Lega
Kazalika, a shekarar 2024 da ta gabata gwamnatin Najeriyar kuma bisa umurnin kotu ta ƙwace kadarorin marigayi tsohon hafsan hafsoshin tsaron ƙasar, Air Chief Marshal Alex Badeh, da ke unguwannin masu hali na Wuse 2 da Maitama.
Ga wasu daga cikin gidajen da aka tabbatar da mallakar sa ne a suka haɗa da :
- Gida da mai lamba 14 Adzope Crescent, daura da Kumasi Crescent,
- Da mai lamba 19 Kumasi Crescent, Wuse 2
- Da gida mai lamba 6 Umme Street, Wuse 2.
Sai kuma tarin gidaje da filaye da motocin alfarma da gwala-gwalai da gwamnatin da ta gabata ta Muhammadu Buhari ta ƙwace daga hannun tsohuwar ministar man fetur ta Najeriya a lokacin gwamnatin shugaban ƙasar Goodluck Ebele Jonathan, Diezani Alison-Madueke, waɗanda suka haɗa da na Banana Island, ɗaya daga cikin unguwanni masu tsada a Legas da ƙumshi rukunin gidaje 24.











