Wutar daji ta tilasta kwashe mutanen wani gari a Kanada

Wildfire

Ana ci gaba da ayyukan kwashe mazauna birnin Yellowknife, kimanin 20,000 waɗanda aka faɗa musu su bar gidajensu ya zuwa ƙarfe 7 na yamma agogon Najeriya a yau.

Dubban mutane sun yi cincirindo a filin jirgin sama na yankin da kuma titin fita daga garin a daidai lokacin da ɗaruruwan wasu suka kafa layi don shiga sahun waɗanda za a kwashe su cikin gaggawa a jiragen sojoji.

Yankin Northwest Territories ya yi shelar kafa dokar ta-ɓaci da yammacin ranar Talata a lokacin da hukumomi ke fama da gobarar da ta tashi a wurare kusan 240.

Gobarar daji dai cikin sauri tana ƙara tunkarar ƙaramin garin Yellowknife da ke lardin Northwest Territories na ƙasar Kanada.

Hukumomi na ƙarfafa gwiwar mutane su fice daga garin ta hanyar shiga motoci fiye da mutum ɗaya don rage cunkoso a kan titi.

Jiragen sama na ta kwashe mutane tsawon wunin rana musamman ga waɗanda ba su da halin samun motar da za ta ɗauke su, sannan an samu rahotannin dogayen layuka a gidajen mai na birnin.

Ya zuwa jiya, wutar daji tana wani wuri da bai fi nisan kilomita 15 na daga gaɓar birnin, kuma ana ƙiyasta cewa gobarar na iya kai wa wajen birnin a gobe Asabar.

Wildfire

Asalin hoton, Reuters

Kanada na fuskantar gobarar daji mafi muni a tarihi, gobara ta tashi a wurare fiye da 1,000 na faɗin ƙasar daga gundumar British Columbia a yammaci zuwa Quebec a gabashi.

Ayyukan agaji sun kai matsayin abin da ake kira matakin shirin ƙasa na 5 - shi ne mataki mafi girma na tunkarar bala'i - abin da ke nufin duk ma'aikatan kashe gobara a ƙasa, an ɗora musu alhakin su shiga aikin kashe wutar.

Kanada ta saba fuskantar ɓarkewar gobarar daji a irin wannan lokaci na shekara amma yanayin ɗumi da bushewar daji a wannan zafi fiye da yadda aka saba gani, ya haddasa tashin gobara da aka gaza shawo kansu a sassa da dama.

Masana kimiyya sun ce sauyin yanayi ne ya ta'azzara hatsarin zafi, sannan busasshiyar iska mai yiwuwa ta ruruta wutar da ake samu.

Ƙarin hotuna na aikin kwashe mazauna garin Yellowknife:

Canada wildfire

Asalin hoton, REUTERS

Bayanan hoto, Wata fasinja na jira tare da karenta don ta samu jirgin sama a Edmonton bayan ta tsere daga Yellowknife
Canada Wildfire

Asalin hoton, REUTERS

Bayanan hoto, Mutane na jira a ɗakin motsa jiki na wata makaranta kafin su hau jirgin saman da zai kwashe su a garin Yellowknife
Canada Wildfire

Asalin hoton, CANADIAN ARMED FORCES/EPA

Bayanan hoto, Mutanen garin Fort Smith, na lardin Northwest Territories ne ke tafiya a cikin jirgin saman sojoji tun farkon wannan mako
Canada Wildfire

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Hayaƙi na tashi daga wutar daji da take ci a zagayen garin Kelowna, a gundumar British Columbia