Elon Musk ya sauka daga matsayin wanda ya fi kowa kuɗi a duniya

Mujallar Forbes mai bibiyar masu arzikin duniya ta ce a yanzu Elon Musk ba shi ne attajirin da ya fi kowa kuɗi a duniya ba.

Hakan ya faru ne sakamakon mummunar faɗuwar da darajar hannayen jarinsa suka yi a kamfaninsa na Tesla mai ƙera motoci cikin wannan shekara.

A cewar Forbes da Bloomberg, a yanzu Bernard Arnault, mai kamfanin sayar da kayan ƙasaita na LVMH ne ya sha gaban Mista Musk a arziki.

Mista Musk ne shugaba kuma mai kashi mafi yawa na hannayen jarin kamfanin Tesla.

A watan Oktoba ne kuma ya kammala cinikin sayen shafin Tuwita kan $44bn.

A cewar Forbes, darajar arzikin Mista Musk a yanzu ta kai kimanin $178bn (£152bn). Yayin da Bernard Arnault aka ƙiyasta nasa arzikin kan $188bn.

Mista Musk ya kammala ƙulla yarjejeniyar sayen Tuwita ne bayan shafe watanni ana kwan gaba kwan baya ta fuskar shari'a, wasu kuma sun bayyana cewa mayar da hankalinsa kan cinikin shafin na ɗaya daga cikin dalilan da suka janyo hannun jarin Tesla ya yi ƙasa.

Bayan da ya zuba hannun jari a kamfanin Tuwita a farkon shekarar nan ne, Mista Musk ya yi tayin sayen shi kan $44bn a watan April, sai dai mutane da dama na ganin kuɗin ya yi yawa matuƙa.

A watan Yuli ne kuma ya fice daga yarjejeniyar inda ya bayyana damuwa game da yawan shafukan bogi da ke amfani da dandalin.

Daga baya dai shugabannin Tuwita ɗin suka shigar da ƙara domin ganin Mista Musk ya tsaya ga tayin da ya yi.

Dan Ives, jami'i daga kamfanin hada-hadar hannayen jari na Wedbush Securities ya ce al'amuran da ke zagaye da batun sayen Tuwita sun yi tasiri sosai kan hannun jarin kamfanin Tesla.

"Musk ya yi faɗuwar tasa" in ji shi. "Musk shi ne Tesla kuma Tesla ne Musk." Mista Musk ya sayar da hannayen jarin Tesla na biliyoyin daloli domin samun damar sayensa, lamarin da ya taimaka wajen durƙusar da hannun jarin.

Masu hannayen jari sun nuna damuwa kan yadda za a samu raguwar masu buƙatar motoci masu amfani da lantarki yayin da tattalin arziki ke yin ƙasa.

Kamfanin Tesla dai ya fuskanci koma-baya da dama da kuma binciken da gwamnati ta yi kan matsalolinsa da kuma tsarinsa na mota mai sarrafa kanta.