Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ƙalubale biyar da ke gaban sabbin hafsoshin tsaron Najeriya
A ranar Laraba ne Majalisar Dattawan Najeriya ta tantance da kuma amincewa da sababbin hafsoshin tsaron ƙasar da Shugban Ƙasa Bola Tinubu ya naɗa a mako da ya gabata.
Fadar shugaban Najeriya ta bayar da sanarwar sauke tsofaffi da kuma naɗa sababbin shugabannin rundunononin sojin ƙasar a ranar Juma'a da ta gabata, inda Shugaba Tinubu ya ce ya yi hakan ne "domin ƙarfafa tsaron ƙasa da kuma kyautata aikin" rundunar sojin.
Kundin tsari mulkin Najeriya ya tanadi cewa dole ne sai majalisar tarayya ta amince da naɗin hafsoshin kafin su fara aiki, kamar yadda wani hukuncin kotu ya tabbatar daga shekarar 2013.
Mutanen da majalisar ta tantance su ne:
- Janar Olufemi Oluyede - Hafsan hafsoshi (mafi girman muƙami)
- Manjo Janar W. Sha'aibu - Hafsan sojojin ƙasa
- Air Vice Marshall S.K. Aneke - Hafsan sojin sama
- Rear Admiral I. Abbas - Hafsan sojin ruwa
- Manjo Janar E.A.P Undiendeye - Shugaba sashen tattara bayanan sirri na soji
Bayan gabatar da kan su da kuma amsa 'yan tambayoyi, shugaban majalisa ya nemi su rusuna su koma wurin zamansu, inda daga baya 'yanmajalisar suka shiga ganawar sirri tare da hafsoshin tsaron ba tare da 'yanjarida ba.
"Na san kuna da tambayoyi masu tsauri, za mu rufe ƙofa da su domin tattanawa. Saboda haka ba sai sun amsa tambayoyi masu yawa ba a yanzu. Wannan ranar tasu ce baki ɗaya," kamar yadda Shugban Majalisa Godswill Akpabio ya faɗa wa 'yanmajalisar.
Naɗin nasu na zuwa ne daidai lokacin da rundunar sojin ƙasar ta ce tana tsare da wasu jami'anta 16 bisa zargin rashin ɗa'a da karya ƙa'idojin aiki.
Wasu rahotonni sun alaƙanta tsare jami'an da yunƙurin juyin mulki, zargin da rundunar ta musanta da kakkausar murya tana mai cewa labaran ƙarya ne.
Ƙalubalen da ke gaban hafsoshin tsaro
Naɗin sababbin hafsoshin tsaron na zuwa ne a daidai lokacin da Najeriya ke fuskantar sababbin barazanar tsaro daga ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadi, da kuma 'yanbindiga masu garkuwa da mutane.
Kabiru Adamu ya ce akwai abubuwa biyar da yake ganin babban hafsan tsaron zai saka a gaba wajen tabbatar da nasara a yaƙi da ƙalubalen tsaro.
- Samar da kayan aiki ga sojojin da ke filin daga ke buƙata: "Na farko shi ne samar da kayan aiki ga sojojin da ke filin daga ke buƙata. Daga cikinsu akwai manyan jami'ai da ke yawo a motocin da ba masu sulke ba a filin daga. Idan aka harbi jami'i zai iya mutuwa nan take.
- Samar da walwala ga dakaru: "Abu na biyu shi ne walwalar dakaru. A dinga sauya dakarun akai-akai kamar yadda ya kamata, da maganar abincinsu da sauran abubuwan da ke ƙarƙashin walwala.
- Tabbatar da ɗa'a da bin ƙa'idar aiki: "Abu na uku shi neɗa'a da bin ƙa'idar aiki. An wayi gari yanzu akwai sojojin da idan aka tura su yankuna kamar arewa maso gabas ko arewa maso yamma ba su son zuwa saboa suna ganin ba abin da ya sa suka shiga aikin soja ba kenan. Idan ana yin irin wannan ba za a samu cigaba ba.
- Kare dimokraɗiyya da nisantar harkokin siyasa: "Kare dimokuraɗiyya da nisantar harkokin siyasa. Tabbatar da cewa rundunar sojin Najeriya ta miƙa kai ga dimokuraɗiyya amma ba tare da ta shiga harkokin siyasa ba yana da muhimmanci sosai. Idan aka duba yankin Sahel, akwai ƙasashe kusan huɗu da sojoji ke mulki. To akwai buƙatar ya shawo kan wannan matsalar.
- Haɗa kan ɓangarori biyar na rundunar soja: "Haɗa kan ɓangarori biyar na rundunar soja. Akwai ma'aikatar tsaro, da hedikwatar tsaron ƙasa - inda Janar Oluyede zai zauna - da rundunonin ƙasa da sama da kuma ruwa. Dole ne Janar Oluyede ya haɗa kan dukkan waɗannan kafi a samu nasara."
'Abin da ya kamata mu yi'
Da yake jawabi lokacin tantance shi, sabon Babban Hafsan Tsaro Laftanar Janar Olufemi Oluyede, shi ne tsohon hafsan sojin ƙasa ne kuma ya bayyana ƙalubalaen da ya fuskanta a muƙamin.
"Abu ne da ke buƙatar ƙwarewa sosai, da hana kai barci, da cikakkiyar sadaukarwa wajen tsare ƙasa," in ji shi.
"Muna sane da cewa kayayyakin aiki ba su da yawa, amma dole ne Najeriya ta samar da abubuwa a cikin gida domin yaƙi da sababbin matsalolin tsaro na ta'addanci da laifukan zamba ta intanet."
Ya kuma bayyana irin abin da yake ganin shugabancinsa zai saka a gaba, musamman game da harkokin yaɗa labarai.
"Idan muka gaza fitar da bayanan da suka dace, matsalolinmu za su ci gaba da ƙaruwa," a cewar babban hafsan tsaron.
Dr Kabiru Adamu mai bincike ne da kuma tattara bayanai game da matsalolin tsaro a kamfanin Beacon Security and Intelligence, kuma ya yarda cewa shi ne abu na farko da Janar Oluyede ya kamata ya tunkara.
"Lokacin da yake hafsan sojan ƙasa bai cika shiga kafofin yaɗa labarai yana bayani ba. Ina ganin ya kamata ya ci gaba da yin hakan, kawai dai ya tabbatar yana da sashen yaɗa labarai da za su dinga bai wa 'yanjarida bayanan da suke nema, amma ba shi ne zai dinga yi ba," a cewarsa.
Wannan yunƙuri zai zama akasin abin da magabacinsa Janar Chris Musa ya dinga yi, inda yake yawan yin hira da kafofin yaɗa labarai na cikin gida da waje.