Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Satar mutane don karɓar kuɗin fansa ta zamo kasuwanci a Najeriya'
Masana tsaro a Najeriya, sun fara tsokaci kan wani rahoton cibiyar SB Morgan Intelligenc,e da ya ce 'yan bindiga masu satar mutane sun karbi kudin fansa sama da naira biliyan biyu da miliyan 57 a shekara daya kawai a kasar.
Rahoton kamfani da ke tattara bayanan tsaro a nahiyar Afirka ya nuna yadda harakar satar mutane ta koma kasuwanci a Najeriya, yayin da masana tsaro a kasar suka ce matsala ce da ke kara ta'azzara musamman a shiyyar arewa maso yamma inda nan ne matsalar ta fi kamari duk da ikirarin da hukumomi ke cewa suna yi na magance matsalar.
Rahoton ya yi bayani ne tun daga watan Yulin 2024 zuwa Yulin 2025, inda ya ce ciniki tsakanin 'yan uwan wadanda aka sace da masu satar mutanen ya samu wurin zama.
Rahoton ya ce a tsakanin wadannan watanni 'yan bindiga da ma masu garkuwar da mutane sun sace mutum 4,722 a hare-hare 997, sannan akalla mutum 762 sun rasa rayukansu a wadannan hare-hare.
Malam Munnir Fura Girke, dan jarida nem ai bincike a kan sha'anin tsaro a Najeriya, ya shaida wa BBC cewa, wannan rahoto abu ne mai tayar da hankali kasancewar duk kudaden fansar da za a ga an biya to wata kadara ce za a siyar ko a nema a wajen dangi kai wani lokaci ma har bara ana yi don a karbo mutanen da aka yi garkuwa da su.
Ya ce," Idan aka kalli wannan abun ya zama wani babban kasuwanci da ake samun kudi da shi,kuma mutum uku ne ke amfana da batun garkuwa da mutane wato da dillalan miyagun kwayoyi da dillalan makamai da kuma masu fataucin bil adama."
Dan jaridar ya ce," Ada dabbobi ake sacewa aje a siyar, to daga baya sai suka gane cewa maimakon a saci dabba 10, idan ka dauki mutum guda zaka samu kudin dabba dari ma."
Barista Audu Bulama Bukarti, mai bincike ne akan sha'anin tsaro a Nahiyar Afirka, shi ma ya bayyana wa BBC yadda ya ke Kallon wannan rahoto inda ya ce garkuwa da mutane da kuma karbar kudin fansa ya zamo wani kasuwanci wanda bama haramunne ba a Najeriya.
Ya ce," Sai an bincika sosai kan a samu kasuwancin da ya yi cinikin naira biliyan da miliyan dari biyar da saba'in a shekara guda, wato kudaden da ake maganar an karba a matsayin fansa."
"Mutane ake kwasa aje ajiye su a wulakantasu su yi wata da watanni wasu ma a kashe su, sannan 'yan uwansu su nemo kudin fansarsu su bayar, wannan bala'ine da kuma tabarbarewar tsaro a Najeriya."
Barista Bukarti, ya ce," Babban abin tashin hankalin shi ne yawan kudin da masu satar mutane ke karba shi ne yawan yadda matsalar zata kara ta'azzara."
"Dole ne gwamnati ta samo hanyoyin toshe inda ake zuwa a kashe kudin da ake karba na fansa tun da ba a dazukan da suke ne ake kashe kudaden ba."In ji Bukarti.
Barista Bulama Bukarti ya ce, dole ne a samo hanyoyin da za a daina kai wadannan kudade na fansa.
Rahoton ya yi gargadin cewa muddin mahukuntan Najeriya basu dauki matakan da suka dace ba kuma cikin gaggawa to ko shakka babu matsalar satar jama'a da kashe-kashe zata ci gaba da yawaita tare da jefa jama'a cikin dumbin talauci da tashin hankali.