Me ya sa Fafaroma Francis ya zaɓi a binne shi a wajen fadar Vatican?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Caio Quero
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Brasil, Editor
- Aiko rahoto daga, Rome
- Marubuci, Juan Francisco Alonso
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Mundo
- Aiko rahoto daga, Rome
- Lokacin karatu: Minti 4
Fafaroma Francis ya karya al'adar da ta wuce shekaru 100 ta hanyar zaɓar kada a binne shi cikin birnin Vatican.
Maimakon haka, za a binne shi a Basilica na St Mary Major, wanda aka fi sani da 'Santa Maria Maggiore' a Italiya, wani coci da ya saba ziyarta domin yin addu'a, musamman kafin da bayan tafiye-tafiyensa zuwa ƙasashen waje.
Zaɓin da Fafaroman ya yi na inda za a binne shi yana nuna yadda tun da farko ya damu da rayuwar mutane masu fama da ƙalubale a cikin al'umma.
Basilica tana kusa da babbar tashar jirgin ƙasa ta birnin Rome, a wani yanki na garin mai cike da masu ƙaramin karfi da ƙabilu daban-daban.
A wannan unguwar, akwai kantunan ƴan China, da wuraren gyaran gashi na 'yan Afirka, da gidajen cin abinci na Indiyawa, da shagunan ƴan Bangladash duk sun haɗe da tsofaffin gidajen Rumawa da kafuna.
Alamim Mohammad, wanda ke aiki a wani shagon gyaran wayar hannu, ya ce yana yawan ganin fafaroman yana ziyartar cocin.
"Na saba jin muryarsa," in ji Alamim, wanda ya yi ƙaura daga Bangladash zuwa Rome shekaru da suka wuce.
"Mutum ne mai kamala. Kullum yana son zaman lafiya. A ganina, mutum ne mai kirki kuma mai sauƙin kai."

Nancy, wata matar da ba ta da matsuguni daga Najeriya ta ce ta tuna ganin Pope Francis sau uku yayin da take bara kusa da cocin.
"Wata rana, na yi matuƙar farin ciki da ganinsa," in ji ta cikin murmushi.
Nancy ta ce ta ga wata babbar ma'ana a lokacin rasuwar Fafaroman, wato a Ranar Litinin bayan Ista.
"Wannan lokaci ne na Ista. Ina ganin mutuwar Pope a lokacin Ista alama ce da zai gana da Yesu Almasihu," in ji ta.

'Santa Maria Maggiore' na ɗaya daga cikin fitattun coci-cocin da suka fi kyau a birnin Rome.
Rufin cocin yana sheƙi da zinari da aka kawo daga ƙasashen Amurka, kuma kayan ado na mosaic da ke cikin cocin na Byzantine suna kai nunawa baƙi zamanin kiristoci na farko zuwa zamanin Baroque.
An kafa cocin fiye da shekaru 1,600 da suka wuce. Kamar yadda hikayoyi suka tabbatar, inda ake cewa ya samo asali ne daga wani abin al'ajabi — dusar ƙanƙara da ta sauka a watan Agusta, wanda aka ɗauka a matsayin alama daga Maryamu mahaifiyar Yesu.

Asalin hoton, Getty Images
A cikin cocin basilica, dubban masu ibada daga sassa daban-daban na duniya sun taru domin yin addu'ar tunawa da Fafaroma Francis.
"Wannan ne karona na farko da zuwa nan. duk na ji tsigar jikina na tashi," in ji Mary Grace daga ƙasar Philippines.
A cikin wasiyyarsa, marigayi Pope ya nemi a binne shi cikin sauƙi a wani ɓangare na cocin.
Wani baƙo daga ƙasar Girka ya ce shawarar Pope Francis na a binne shi a wannan wuri ta dace da hali da irin koyarwarsa.
"Wurin yana da kyan gani matuƙa. Ina son rufin cocin da zinariya da komai kuma yanayin cikin cocin yana saka kwanciyar hankali," in ji shi.
"Ni ba Katolika ba ne, amma na ga mutanen da ke ciki suna cikin alhini. Za ka san cewa suna makoki da gaske," ya ƙara da faɗa.

Marigayi Fafaroma Francis ya bayyana cewa burinsa na binne shi a wajen Vatican ya samo asali ne daga ƙaunar da yake yi wa Maryamu, mahaifiyar Yesu Almasihu.
"A koyaushe ina da matuƙar ƙauna da girmamawa ga St Mary Major, tun kafin na zama Fafaroma," in ji Francis a cikin littafinsa na 2024 mai suna El Sucesor
Fasto Ivan Ricupero, shugaban al'amuran ibada na cocin basilica, ya shaida wa jaridar The Times cewa Fafaroma Francis ya ziyarci cocin sau 125 a lokacin mulkinsa, sau da dama kuma yana kawo furanni.
Francis zai zama Pope na farko da aka binne a wajen Vatican tun bayan Fafaroma Leo XIII, wanda ya rasu a shekarar 1903.











