Ko ya kamata Najeriya ta hada kai da Faransa kan matsalar tsaro?

Asalin hoton, Getty Images
A Najeriya, ana ci gaba da tafka muhawara kan tayin da Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi domin taimakon ƙasar wajen taya ta lalubowa tare da magance matsalolin tsaro da ke addabar yankunan ƙasar.
Emmanuel Macron ya bayyana haka ne a cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya ce bayan taimakon da ƙasarsa za ta bayar, ya kuma buƙaci ƙasashen da ke ƙawayence da Faransa da su ƙara inganta hulɗarsu da Najeriya.
A cewarsa, "Na yi magana da Shugaban Najeriya Bola Tinubu, na shaida masa goyon bayan Faransa game da matsalolin tsaro musamman a arewacin Najeriya," kamar yadda ya rubuta.
Ya ƙara da cewa, "kamar yadda ya [Tinubu] buƙata, za mu ƙarfafa hulɗarmu da hukumomi da kuma taimaka wa al'ummomin da lamarin ya shafa," in ji shi, sannan ya ƙara da cewa "bai kamata mu zama ƴankallo ba."
Wannan kalaman na Macron na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa a ƙasar a game da zargin Shugaban Amurka Donald Trump cewa gwamnatin Najeriya da ƙyale ƴanbindiga suna yi wa mabiya addinin Kirista kisan gilla, iƙirarin da gwamnatin Tinubu ta musanta.
Najeriya dai na fama da matsalolin tsaro da dama, lamarin da ya daɗe yana ci wa mutanen ƙasar tuwo a ƙwarya, inda ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama, sannan ya raba dubbai da muhallinsu duk da ƙoƙarin da gwamnati da jami'an tsaro suka ce suna yi.
Sai dai an buɗe sabon babi ne a rikita-rikitar tun bayan da Trump ya yi barazanar tura sojoji zuwa ƙasar domin fatattakar waɗanda ya bayyana da ƴan ta'adda masu yi wa Kiristoci kisan kiyashi, inda ya ce ko dai gwamnatin Najeriya ta ɗauki mataki, ko shi ya ɗauka.
Sai dai a daidai lokacin da ake tunanin yadda za ta kaya kan barazanar ta Trump ne sai kallo ya koma sama bayan Faransa ta miƙa tayin za ta iya haɗa hannu da Najeriya domin magance matsalar tsaro da ƙasar ke fuskanta.
Muna maraba - Amsada Sulaiman Ɗahiru

Asalin hoton, Nigeria State House
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Domin jin ta bakin masana, BBC ta zanta da Ambasada Sulaiman Ɗahiru wanda ya ce shi dai yana tunanin babu wata matsala don Faransa ta yi yunƙurin taimakon Najeriya domin magance matsalar.
Ya ce, "Duk waɗanda suke so su taimaka wa Najeriya su zo su taimaka domin mu samu mu huta da wannan masifar da muke ciki. Maganar Faransa ba ta shiri da wasu ƙasashe a Afirka, wannan tsakaninsu ne," in ji tsohon jami'in na diflomasiyya.
Ya ce babu ruwan Najeriya da takun-saƙa da ke tsakani Faransa da wasu ƙasashen na Afirka, domin a cewarsa ba ta yi wa Najeriya wani laifi da za a gani a zahiri ba da zai sa a guji karɓar taimakonta.
"Mu dai Faransa ba ta mana komai ba, don haka babu dalilin da zai sa mu ƙi karɓar taimakonta. Sannan kuma tun bayan da Shugaba Najeriya Bola Tinubu ya hau karagar mulki, sai dangantaka tsakanin Faransa da Najeriya ta inganta, waƙakila wannan ne ma ya sa Faransa ke so ta taimaka wa Najeriya. Don haka idan za su taimaka, su zo za mu karɓa hannu biyu-biyu," in ji shi.
A game da fargabar da ake yi na samun matsala idan Amurka ta shigo, sannan Faransa ta shigo kuwa, sai ya ce ko a baya Najeriya na da dangantaka da Amurka da Faransa, ''A lokacin muna mu'amala mai kyau da Amurka da Faransa a tare, idan su biyun sun ce za su taimaka, ni dai ban ga abin laifi ba."
Sai dai tsohon ambasadan ya yi gargaɗin cewa akwai buƙatar a yi taka-tsantsan da Amurka, inda ya ce ''Amurkar Donald Trump ba irin Amurka da aka sani a baya ba ce."
Da na gaba ake gane zurfin ruwa - Jibrin Ibrahim
A nasa ɓangaren, Jibrin Ibrahim na cibiyar CDD, cewa ya yi an daɗe ana ruwa ƙasa na shanyewa, inda ya ƙara da cewa in dai agajin Faransa ne, to me jiya ma ta yi, bare yau.
A cewarsa, ''Idan ka duba shekara 20 da suka gabata, ta sha cewa za ta taimaka wa ƙasashen da suke cikin matsala, amma ta gaza. Har ƙungiya suka kafa da ta ƙunshi ƙasashe biyar wato Chad da Jamhuriyar Nijar da Burkina Faso da Mauritania da Mali," in ji shi.
Ya ce duk da alƙawarin da ta yi cewa za ta taimaka musu wajen yaƙi da ta'addanci, ''wajen shekara 20 ke na amma babu abin da ta tsinana musu, shi ne ƙasashen suka gane Faransa ba ta da niyyar taimakonsu," in ji shi, sannan ya yi zargin cewa akwai dai wasu abubuwan daban da suk enema.
Ya ce ya kamata Tinubu ya duba komai da natsuwa, ''ya yi dogon tunani ya duba maƙwabtaka ya ga abin da ya faru da su."










