Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Charles Soludo ya lashe zaɓen gwamnan jihar Anambra
Hukumar zaɓen mai zaman kanta INEC ta sanar da Charles Soludo na Jam'iyyar All Progressives Grand Alliance wato APGA a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Anambra wanda aka yi a jiya Asabar, 8 ga watan Nuwamba.
Baturen zaɓen jihar, Farfesa Edoma Omoregie ne ya sanar da sakamakon a cibiyar tattara sakamakon zaɓen da ke babban birnin jihar, Awka a safiyar yau Lahadi.
Ya ce Soludo ya samu ƙuri'a 422,664, sai kuma Nichola Ukachukwu na Jam'iyyar APC mai biye masa da ƙuri'a 99,445.
George Moghalu na Jam'iyyar Labour ne ya zo na uku da ƙuri'a 10,576, sai Jude Ezenwafor na PDP mai ƙuri'a 1401.
Charles Soludo wanda tsohon shugaban babban bankin Najeriya ne, ya lashe zaɓen ne domin yin sake mulkin jihar a karo na biyu.
Hukumar ta wallafa sakamakon zaɓen ne a shafin intanet na musamman mai suna IReV, kamar yadda Dokar Zaɓe ta 2022 ta tanada.
’Yantakara 16 ne suka fafata
‘Yantakara 16 ne gaba ɗaya ke neman kujerar gwamnan Anambra ciki har da gwamna mai ci, Chukwuma Soludo, wanda ke neman tazarce.
Dubban jami'an tsaro ne aka jibge a jihar domin zaɓen, yayin da manyan 'yan takara suka rattaɓa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya, domin tabbatar da zaɓen cikin lumana da mutunta juna.
Hukumar INEC ta amince da 'yan takara 16 da suka haɗa da mata 2 da maza 14 da za su fafata, ciki har da gwamnan jihar, Chukwuma Soludo, wanda ke neman mulkin jihar karo na biyu.
Wasu daga cikin 'yan takarar sun tsaya takara a zaɓen da ya gabata, kuma suna fatan a wannan karon za su yi nasara.
Sunayen 'yan takara da jam'iyyunsu sun haɗa:
- Onyeeze Chidi Charles – Jam'iyyar A
- Nweke Ezechukwu Japhet – Jam'iyyar AA
- Ifemeludike Chioma Grace – Jam'iyyar AAC
- Nwosu Chima John – Jam'iyyar ADC
- Nicholas Ukachukwu – Jam'iyar APC
- Soludo Charles Chukwuma – Jam'iyyar APGA
- Otti Cyprain Echezona – Jam'iyyar APM
- Nweke Chrispopher Chukwudubem – Jam'iyar APP
- Okeke Chika Jerry – Jam'iyyar BP
- Moghalu George Nnadubem - Jam'iyyar LP
- Onyejegbu Geoffrey – Jam'iyyar NNPP
- Ndidi Christy Olieh – Jam'iyyar NRM
- Ezenwafor Jude – Jam'iyyar PDP
- Chukwurah Vincent – Jam'iyyar SDP
- Chukwuma Paul Chukwuka – Jam'iyyar YPP
- Ugwoji Uchenna Martin – Jam'iyyar ZLP
Tarihin zaɓen jihar Anambra tun daga shekarar 1999
Jihar Anambra na da matsayi na musamman a harkar zaɓe a Najeriya saboda ita ce jiha ta farko da ta fara gudanar da zaɓukan da ake yi ba tare da sauran zabukan kasa baki daya ba tun bayan dawowar mulkin dimokuradiyya a 1999.
Abun ya fara ne lokacin da Kotun ƙoli ta ayyana Peter Obi a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a shekarar 2003, shekaru uku bayan Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta riga ta bayyana Chris Ngige na jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓen kuma aka rantsar da shi.
Obi ya kai ƙara kotu inda kotu ta yanke hukunci cewa lokacin mulkinsa na shekaru hudu zai fara ne daga ranar da aka rantsar da shi a matsayin gwamna.
Tun daga wannan lokaci, jihohi da dama da suka samu irin wannan lamarin suka fara samun jadawalin zaɓe daban da lokacin zabukan gama gari da Najeriya ke gudanarwa.