Rayuwar ƙunci: Yadda matan Sudan ke fuskantar cin zarafi da fyaɗe a Libya

    • Marubuci, Amira Mhadhbi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Arabic
  • Lokacin karatu: Minti 6

"Muna rayuwa ne cikin ƙunci," kamar yadda Layla ta bayyana ta wayar tarho a hankali domin kada wani ya ji tana magana. Ta tsere ne daga Sudan tare da mijinta da yara shida a farkon shekarar da ta gabata domin tsira daga yaƙin ƙasar, inda yanzu take rayuwa a Libya.

Kamar sauran matan Sudan da BBC ta zanta da su a game da yadda suke rayuwa cikin ƙunci a Libya, ita ma an canja sunanta.

Gargaɗi: Labarin nan yana ƙunshe da wasu bayanai masu tayar da hankali.

Cikin sanyin murna ta bayyana yadda yaƙin wanda aka fara a shekarar 2023 ya kai ga gidansu da ke Omdurman.

Iyalan sun ratsa ta Masar ne kafin suka biya masu safarar mutane kuɗi $350 (£338) domin su kai su Libya, inda suke tunanin za su samu rayuwa mai kyau.

Bayan sun tsallake, Layla ta ce sai masu safarar mutanen suka tsare su, suka zane su, sannan suka buƙaci ƙarin kuɗi.

Bayan kwana uku aka sake su, inda Layla ta ce suka tafi yammacin ƙasar, suka kama ɗaki domin fara sabuwar rayuwa.

Amma watarana sai mijinta ya fita neman aiki, amma bai dawo ba. Sannan aka yi ƴarta mai shekara 19 fyaɗe.

"Sai ya faɗa wa ƴata cewa zai yi wa ƙanwarta fyaɗe idan ta faɗa abin da ya mata," in ji Layla.

Layla ta ce yanzu sun rasa yadda za su yi: ba su da kuɗin da za su biya masu safarar mutanen domin su tafi, sannan ba za su iya komawa Sudan ba.

"Da ƙyar muke iya cin abinci," in ji ta, sannan ta ƙara da cewa yaranta ba sa zuwa makaranta.

"Yarona na tsoron fita daga gida saboda wasu yaran suna cin zarafinsa da zaginsa saboda shi baƙi ne."

Miliyoyin mutane ne suka tsare daga Sudan tun bayan da yaƙin ya ɓarke tsakanin sojojin ƙasar da dakarun RSF a 2023. Ɓangarorin biyu ne suka haɗa hannu suka yi juyin mulki a shekarar 2021, amma ɓaraka tsakaninsu kan ƙarfin iko ya jefa ƙasar cikin yaƙin basasa.

Sama da mutane miliyan 12 ne suka bar gidajensu, sannan sassan ƙasar da dama na fuskantar yunwa, inda aƙalla mutum miliyan 24.6 - kusan rabin mutanen ƙasar - suka cikin tsananin yunwa.

Hukumar kula da ƴan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce aƙalla ƴan Sudan 210,000 ne suka gudun hijira yanzu haka a Libya.

BBC ta zanta da iyalai biyar ƴan Sudan, waɗanda suka fara zuwa Masar kafin suka tsallaka Libya, kuma duk sun bayyana cewa sun fuskanci wariyar launin fata da cin zarafi kafin suka garzaya Libya, suna tunanin cewa za sufi samun kwanciyar hankali.

Salma ta bayyana wa BBC cewa suna zaune ne a birnin Cairo na Masar tare da mijinta da yaranta uku lokacin da yaƙin ya ɓarke, amma lokacin da ƴan gudun hijira suka fara yawa a ƙasar, sai baƙi suka fara fuskantar ƙalubale.

Sai suka yanke shawarar tafiya Libya, ashe rayuwa ce za su shiga ta ƙunci.

Suna isa Libya aka tsare su a wata ma'adana. Wasu lokutan ma, Salma ta ce ana raba ta da mijinta, a ajiye ta a wani waje cike da mata da yara, inda ta ce ita da manyan yaranta suke shan duka.

"Bulalar da suke mana sai da ta jikinmu ya nuna alama. Suna zane ƴata, sannan su ƙona hannun yarona ina kallo.

"Nakan yi fata mu mutu tare kawai mu huta saboda na cire tsammani."

Salma ta ce ɗanta da ƴarta duk sun shiga cikin damuwa, tana cikin magana sai ta rage murya.

"Za su iya kai ni wani ɗaki 'na fyaɗe' da akwai maza da dama a ciki," in ji ta, sannan ta ƙara da cewa, "wani mutum daga cikin su ya min ciki har na haihu,"

Da sannu da tara kuɗi da taimakon wasu ƴanuwanta da suke Masar, sannan ta biya, masu safarar suka sake ta da iyalanta.

Ta ce sai likita ya faɗa mata cewa bai kamata ta zubar da cikin ba saboda ya riga ya girma, lokacin da mijinta ya gane tana da ciki kuma sai ya tafi ya bar ta da yaranta suka kwana a duk inda suka samu, sannan suna bara a tituna.

Sai suka samu mafaka a wani gida da ke arewa maso yammacin Libya na wani ɗan lokaci, inda suke cin duk abun da ya samu, sannan suke shan ruwa daga wani kwatamin gidajen mutane.

Jamila, wata ƴar Sudan ce wadda ta kusa shekara 40, wadda ta bar Sudan zuwa Libya domin samun rayuwa mai kyau.

Ta ce an sha yi wa yaranta mata fyaɗe, "saboda na tura su aikin goge-goge lokacin da na fara rashin lafiya; watarana sai suka dawo gida cikin jini - maza huɗu sun musu fyaɗe har sai ta ɗaya ta suma," in ji ta.

Jamila ta ce ita kanta an mata fyaɗe, sannan ta ce wani wanda ta girme shi ya tsare su na makonni bayan ya ce zai ɗauke su aikin goge-goge a gidansa.

"Yana kirana da baƙar banza, sannan ya min fyaɗe yana kuma cewa, 'wannan ne amfanin mata."

"Har ƙananan yara suna kyararmu, suna mana kallon dabbobi saboda mu baƙaƙe ne ƴan Afirka, shin suma ba ƴan Afirka ba ne,?"

Da aka yi wa yaranta fyaɗe, sai ta kai su asibiti, sannan ta kai ƙara wajen ƴansanda, amma da ƴansandan suka gane cewa ƴan gudun hijira ne, sai suka dakatar da bincike, sannan suka mata gargaɗin cewa za iya kulle ta a kurkuku idan aka shigar da ƙarar a hukumance.

Libya ba ta cikin ƙasashen da suka shiga yarjejeniyar taron ƴan gudun hijira na 1951 ko kuma taron da aka yi na 1967 na ƴan gudun hijira - inda suke yi wa ƴan gudun hijira kallon masu neman mafaka "baƙin haure."

Hanaa, wadda take tsintar robobin da aka zubar tana sayarwa domin ciyar da iyalinta, ta ce an sace ta ne a yammacin Libya, aka kai su wani daji, aka nuna musu bindigogi aka musu fyaɗe da ƙarfi da yaji.

Labarin cin zarafin ƴan gudun hijira waɗanda suka fito daga ƙasashen Afirka ba sabon abu ba ne a Libya. Ƙasar tana sadar da mutane ne zuwa turai, duk da cewa daga waɗanda BBC ta zanta da su, babu wadda ta bayyana wa BBC cewa tana da niyyar tafiya turai.

A shekarar 2022, ƙungiyar Amnest International ta zargi jami'an tsaron SSA da kame da tsare mutane ba gaira ba dalili, tare da azabtar da mutane da sauran tauye haƙƙin ƴan'adam.

Rahoton ya ƙara da cewa ma'aikatar harkokin cikin gida a babban birnin ƙasar na Tripoli sun bayyana wa Amnesty cewa ba su ƙarfin iko a kan SSA ɗin, saboda suna ƙarkashin firaminista Abdul Hamid Dbeibeh ne, wanda shi kuma ofishinsa ya ƙi amsa buƙatar BBC na yin bayani.

Cibiyar Crimes Watch ta shaida wa BBC cewa cin zarafin baƙi na faruwa a wuraren tsare mutane, ciki har da kurkukun Abu Salim da ke Tripoli.

A shekarar 2023, rahoton ƙungiyar likitoci ta Médecins Sans Frontières (MSF) ta ce ana samu ƙaruwar cin zarafi da fyaɗe a kurkukun Abu Salim.

Ma'aikatar harkokin cikin gida da sashen yaƙi da kwararowar baƙin haure ba su ce komai ba game da buƙatar bahasi kan zargin.

Salma ta ce yanzu ba za ta iya komawa gida ba, saboda "za su ce na kawo musu abin kunya. Ba na tunanin za su amince su karɓi ko da gawata ce," in ji ta.