BBC ta bankaɗo mayakan da ake zargi da kisan kiyashi a Sudan

    • Marubuci, Peter Mwai, Kumar Malhotra & Matt Murphy
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Verify
  • Lokacin karatu: Minti 7

Binciken da BBC ta gudanar da ke tabbatar da bidiyo da dama da ke nuna mayaƙa suna murna da alhafarin kisan kiyashi, daga baya kuma suka dinga kyarar waɗanda suka tsira da rayukansu, ya gano na mayaƙan RSF ne na Sudan.

BBC ta tabbatar da cewa aƙalla mutum 80 ne suka mutu a harin na watan Oktoba da aka kai a al-Seriha a jihar Gezira, inda Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce adadin na iya kai mutum 124.

Wani shaida ya faɗa wa sashen bincike na BBC cewa ya ga wasu fararen hula da mayaƙa suka harbe a yayin da suke ƙoƙarin tserewa.

Ga dukkan alamu sauya sheƙar da wani babban kwamandan ƙungiyar RSF a jihar Gezira zuwa ga dakarun gwamnati ne ya haifar da kisan kiyashin.

A wata sanarwa da ta aika wa BBC, rundunar RSF ta musanta cewa mayaƙanta na da hannu a kashe-kashe tana mai cewa "aikin mayaƙan shi ne kare fararen hula da tabbatar da tsaro da zaman lafiya amma ba kashe su ba."

Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan'adam sun yi allawadai da yaƙin na gwagwarmayar shugabanci na tsawon wata 20 tsakanin dakarun gwamnati da na RSF inda dukkaninsu ake zargi sun aikata laifukan yaƙi.

Gargaɗi: Wannan labarin yana ɗauke da bayanai na kashe-kashe da hotunan gawarwaki, wanda zai iya tayar da hankalin wasu masu karatu.

Yadda sauya sheƙa ya haifar da harin ramuwa

A ranar 20 ga Oktoba, rundunar sojin Sudan ta sanar cewa Abu Aqla Keikal, wani babban kwamadan RSF a jihar Gezira ya dawo cikin rundunar tare da wasu dakarunsa da dama.

Matakin Keikal na dawowa cikin rundunar sojin Sudan, inda yake aiki kafin soma yaƙin, an bayyana shi a matsayin wata nasara ta farfaganda, inda aka buƙaci sauran mayaƙan RSF su miƙa wuya a matsayin wata dama ta yin afuwa.

Bayan sauya sheƙar Keikal, mayaƙa suka ƙaddamar da hare-hare kusan 68 na ramuwa a garuruwa da ƙauyukan jihar Gezira tsakanin 20 ga Oktoba zuwa 4 ga Nuwamba, kamar yadda alƙaluman ƙungiyar ACLED da ke sanya ido kan yaƙi suka bayyana.

Sashen bincike na BBC ya gudanar da bincike kan ɗaya daga cikin hare-hare, ta hanyar amfani da shaidu da hotunan tauraron ɗan'adam da bidiyo da kuma hotuna domin tabbatar da asalin abin da ya faru.

Yadda aka yi kisan kiyashi a al-Seriha

Mohammad Ismail ya fita sallar asuba a wani masallaci a ranar 25 ga Oktoba, lokacin da ya ji mayaƙa na tunkarar al-Sariha, garin da ke da yawan al'umma 15,000 da tazarar nisan kilomita 90 da Khartoum babban birnin ƙasar.

Ya shaida wa BBC cewa nan take ya ruga gida domin kare iyalansa, bayan rikicin ya ɓarke.

Ƴanbindiga sun afka wa masallacin, a cewarsa, suna buɗe wuta "ga duk abin da ya motsa."

An harbi mutane da dama lokacin da suka yi ƙoƙarin tserewa, in ji shi. Wasunsu an harbe su a kusa a wani filin da ya kewaye birnin. Ƴan'uwansa da dama na cikin waɗanda aka kashe.

Su wa suka aikata kisan?

Sashen bincike na BBC ya samu bidiyo da dama da mayaƙa da kansu suka ɗauka, suna alfahari da abin da suka aikata, suna yin kira ga Keikal, tsohon kwamandan RSF ya gani da idonsa abin da suka aikata ga mutanen yankinsa.

A wani bidiyon, an ga wasu mayaƙan na RSF na murnar kai harin a harin da kuma kisan mutane.

Mun tabbatar da cewa an ɗauki wannan bidiyon ne a al-Sariha ta hanyar kwatanta gine-gine da sauran abubuwa a cikin bidiyon a hotunan tauraron ɗan'adam na garin.

A ɗaya daga cikin bidiyon, wani sojan ya nuna agogonsa a kyamara, da ke nuna ranar 25 ga Oktoba - yana kuma nanata a bayyane da ƙarfi - ranar da aka yi kisan a al-Sariha.

Mr Ismail shi ma ya shaida wa BBC cewa lokacin da suka shigo garin, ya gane wasu daga cikin mayaƙan da suka kai harin a matsayin mazauna garin ne da suka shiga RSF.

Ya kuma ga wasu kwamandoji biyu da aka san shugabannin RSF ne a yankin.

Sashen bincike na BBC ya ɗora wasu hotunan ƴantawayen na RSF a wata manhaja domin ƙoƙarin gane su, amma hakan bai yi ba.

Mayaƙan sun nuna wa mutanen garin cewa sun aiwatar da kisan ne a matsayin martani ga sauya sheƙar Keikal.

A wani bidiyon, ɗaya daga cikin mayaƙan ya ce da larabci: "Keikal... kalla waɗannan mutanenka ne.

Mun yi ƙoƙarin kwatanta bidiyon da kuma bishiyoyi da nau'in gine-ginen yankin ta hanyar amfani da tauraron ɗan'adam na garin al-Seriha.

A wani bidiyon kuma wanda ba a gano wurin da aka ɗauke shi ba, da aka fara gani a intanet a ranar 26 ga Oktoba - an ga wasu sanye da kayan soja da tambarin RSF suna magana kan sauya sheƙar Keikal wanda suka kira "maciyi amana" a jihar Gezira.

Sun ambaci al-Sariha, tare da cewa garin zai fuskanci abin da ya yi daidai da shi.

Lokacin da sashen bincike na BBC ya tuntuɓi RSF domin martani, sun musanta cewa waɗanda aka gani a bidiyon a matsayin dakarunsu. "Za ka iya samun kakin RSF kuma ka saka... da kuma aikata laifi kan fararen hula domin ɓata sunan dakarun RSF," kamar yadda kakakin ƙungiyar ta bayyana.

BBC ta ga wasu bidiyo uku da mayakan suka ɗauka da kansu kuma an ga tambarin RSF a kakin da suke sanye da su.

Wani rahoton HRW kan hare-haren al-Sehira da kuma wasu garuruwan jihar Gezira tun sauka sheƙar Keikal a ranar ga watan Oktoba ya bayyana dakarun RSF ne suka kai harin.

A ranar 29 ga Oktoba, majalisar Ɗinkin Duniya ta fitar da sanarwa inda ta yi allawadai a al-Seriha da wasu garuruwan Gezira inda ta bayyana RSF a matsayin wadanda suka kai hare-haren.

Fararen hula nawa aka kashe?

BBC ta samu wasu hotunan bidiyo huɗu na daban bayan kai harin a al-Seriha.

Suna tayar da hankali inda suka nuna gawarwakin mutane a kwance a harabar wani masallaci an lulluɓe su da likkafani.

An fara ganin waɗannan bidiyoyin a ranar 26 ga Oktoba. Kuma binciken BBC ya tabbatar da harabar masallacin aka jera gawarwakin.

Sashen bincike na BBC ya yi nazari kan hotunan bidiyon, inda aka kidaya gawa 82 da aka jera a gado ko a ƙasa.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce mutum 124 suka mutu a harin na al-Seriha.

Wata ƙungiyar farar hula a Gezira ta ce adadin waɗanda suka mutu za su iya zarta mutum 140.

Wani abin da kuma binciken BBC ya gano shi ne makaken kabari a maƙabartar garin.

Mr Ismail ya ce an gina makaken ƙabari a maƙabartar. Kuma binciken BBC ta hanyar tauraron ɗan'adam a maƙabartar ya nuna cewa babu makeken ƙabarin ba hotunan da aka ɗauka a watan Mayu.

An yi garkuwa da waɗanda suka tsira don karɓar kuɗi

Bayan sun gama harbe-harben kuma sojojin sun ƙwace iko, sai aka yi wa waɗanda suka tsira ƙawanya aka kama su.

Sashen bincike na BBC ya ga waɗannan bidiyoyin na yadda aka kama da kuma garkuwa da mutanen.

A ɗaya daga ciki, an ga aƙalla mutum 60 a zaune ko a tsaye a wani bangon gini ƴanbindiga na tsare da su.

Wasu daga cikin waɗanda aka kama tsofaffi ne, wasunsu sanye da tufafi fari da jini.

A cikin bidiyon, an ji wasu ƴanbindigar na kiran mutanen karnunka da kukan dabbobi.

Sashen bincike na BBC ya tabbatar da cewa an ɗauki hotunan bidiyon ne a arewa maso yammacin garin kamar yadda hotunan tauraron ɗan'adam suka tabbatar.

Akwai wasu gugun mutanen da aka jera hannunsu a baya.

A yayin da suke tafiya gaban mayaƙan, ɗaya daga cikin mayaƙan da aka gani a bidiyon farko yana kyarar su.

"Mun samu galaba kan al-Seriha ko," kamar yadda ɗaya daga cikin ɗanbindigar ya tambayi ɗaya daga cikin waɗanda suka kama.

Elmubir Mahmoud, sakatare janar na majalisar Gezira ya shaida wa BBC cewa mayakan sun tafi da mutum 150 bayan sun bar garin. Ya ce aƙalla 11 daga cikinsu - haɗi da yarinya ƴar shekara uku aka kashe. BBC ba tabbatar da wannan ba.

Amma abin da mazauni garin Mahammad Ismail ya shaida mana ya nuna cewa waɗanda suka tsira an tilasta masu biyan kuɗin fansa domin sakin ƴan'uwansu.

Ya ce mayaƙan sun buƙaci a biya tsakanin dala 100 zuwa dala 1,000.

Ƙasashen duniya da dama sun yi allawadai da ayyukan RSF da dakarun sojin Sudan a Gezira.

A wata sanarwa jekadiyar Amurka a Majalisar Ɗinkin Duniya Linda Thomas-Greenfield ta ɓukaci ƙasashe su daina samar da makamai ga ɓangarorin da ke yaki a Sudan. Ta ce samar da makaman ke ƙara kazancewar yaƙin.

"Mutanen Sudan jure bala'i," in ji ta. "Sun cancanci kariya da mutunci da adalci. Sun cancanci yin rayuwa."