Rashford na son ci gaba da zama a Barcelona, Zikzee na shirin barin Man United

Lokacin karatu: Minti 2

Dan wasan gaban Manchester United Marcus Rashford, mai shekara 27, yana son ci gaba da zama a Barcelona bayan zaman aron da ya ke yi a ƙungiyar ya ƙare a ƙarshen kakar wasan bana, inda kulob ɗin na Sifaniya ke da zaɓin ƙulla yarjejeniya ta dindindin da ɗan wasan na Ingila a bazara mai zuwa. (ESPN)

Ɗan wasan gaban Holland Joshua Zirkzee zai nemi barin Manchester United a kasuwar musayar ƴan wasa a Janairu, inda a halin yanzu West Ham ke kan gaba wajen neman ɗaukar ɗan wasan mai shekara 24. (Mirror)

Zirkzee zai fi son ci gaba da zama a gasar Premier yayin da yake neman samun gurbi a tawagar ƴan wasan Netherlands da za ta buga gasar cin kofin duniya. (Star)

Manchester United na shirin sayen sabbin ƴanwasan tsakiya guda biyu a shekara mai zuwa, inda ɗan wasan Chelsea ɗan ƙasar Brazil Andrey Santos mai shekara 21 ke na gaba a jerin wasu ƴanwasa shida da ƙungiyar ke zawarci, da suka haɗa da ɗan wasan Brighton da Kamaru Carlos Baleba mai shekara 21. (Talksport)

Ɗan wasan Newcastle United ɗan ƙasar Jamus Nick Woltemade mai shekara 23 bai cire rai kan fatan da ya ke da shi na taka leda a Bayern Munich a nan gaba ba. (Bild)

Ɗan wasan baya na Crystal Palace da Ingila Marc Guehi, mai shekara 25, yana ɗaya daga cikin waɗanda Bayern Munich ke sha'awar ɗauka, ƙungiyar ta na kuma zawaricin ɗan wasan Borussia Dortmund da Jamus Nico Schlotterbeck mai shekara 25, amma sai idan har ɗan wasan Faransa Dayot Upamecano, mai shekara 26, bai tsawaita kwantiraginsa ba ko kuma an sayar da Kim Min-jae na Koriya ta Kudu, mai shekara 28. (Sky Sports Germany)

Everton ta shirya wurin yunƙurin sake siyan ɗan wasan Brazil Richarlison, yayin da Tottenham ke tunanin sanya ɗan wasan mai shekara 28 a kasuwa a watan Janairu. (TeamTalk)

AC Milan da Aston Villa da kuma West Ham na cikin ƙungiyoyin da ke zawarcin ɗan wasan tsakiyar Manchester City da Croatia mai shekara 31, Mateo Kovacic. (Caught Offside)

Golan Jamus Marc-Andre ter Stegen na iya barin Barcelona a watan Janairu kuma tuni ƙungiyoyi da dama suka shiga neman ɗan wasan mai shekara 33. (Sky Sports Germany)

Chelsea na neman sabon mai tsaron gida ruwa a jallo kuma za ta iya duba yiwuwar ƙulla yarjejeniyar aro da Ter Stegen, kafin ta yi yunƙurin ɗaukar ɗan wasan AC Milan da Faransa Mike Maignan, mai shekara 30, a bazara mai zuwa kan kyauta. (TeamTalk)

Tsohon kociyan Liverpool da Real Madrid, Rafael Benitez na shirin komawa aikin horas da ƴan wasan bayan da aka fara raɗe-raɗin cewa dan ƙasar Sifaniyan zai zama sabon kocin ƙungiyar Panathinaikos ta ƙasar Girka. (Mail)