El Clasico: Real Madrid da Barcelona a La Liga

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid za ta karbi bakuncin Barcelona a wasan mako na 32 a La Liga a Santiago Bernabeu ranar Lahadi.
Kungiyar da Carlo Ancelotti ke jan ragama tana ta daya a teburin La Liga da maki 78 da tazarar maki takwas tsakani da Barcelona ta biyu.
Girona ce ta uku mai maki 65 da kuma Atletico Madrid mai maki 61 a mataki na hudu a teburin babbar gasar tamaula ta Spaniya.
Wannan shi ne wasa na uku da za su kara a bana, inda Real Madrid ta je ta ci Barcelona a La Liga 2-1 ranar 28 ga watan Oktoban 2023.
Haka kuma Real Madrid ta doke Barcelona 4-1 a Spanish Super Cup ranar 14 ga watan Janairun 2014.
Wasannin da aka buga tsakanin Real Madrid da Barcelona 2023/2024:
Spanish Super Cup Lahadi 14 ga watan Janairun 2024
- Real Madrid 4 - 1 Barcelona
Spanish La Liga Asabar 28 ga watan Oktoban 2023
- Barcelona 1 - 2 Real Madrid
Barcelona ta ci karo da koma baya a Champions League a bana, bayan da Paris St Germain ta fitar da ita a zagayen daf da na kusa da na karshe.
PSG ta kai daf da karshe, bayan da aka doke ta 3-2 a Faransa, ita kuma ta ci 4-1 a Spaniya a wasa na biyu, kenan ta ci kwallo 6-5 gida da waje.
Barcelona ce ke rike da La Liga da ta dauka a bara, wadda rabon da ta lashe Champions League tun 2014/15 mai biyar jimilla.
Ita kuwa Real Madrid ta kai zagayen daf da karshe a gasar zakarun Turai, bayan da ta fitar da Manchester City a bugun fenariti, sakamakon da suka tashi 1-1 har da karin lokaci a Etihad.
Tun farko sun tashi 3-3 a Spaniya, kenan Real Madrid ta rama abinda City ta yi mata a bara da ta cire ta a Champions League.

Asalin hoton, Getty Images
'Yan wasan Real Madrid da za su kara da Barcelona:
Masu tsaron raga: Lunin, Kepa da kuma Mario de Luis.
Masu tsaron baya: Carvajal, Militão, Nacho, Lucas Vázquez, Fran García, Rüdiger and Mendy.
Masu buga tsakiya: Bellingham, Kroos, Modrić, Camavinga, Valverde, Tchouameni, Ceballos da kuma Arda Güler.
Masu cin kwallaye: Vini Jr., Rodrygo, Joselu da kuma Brahim.
Wadanda ke kan gaba a cin kwallaye a La Liga:
- Artem Dovbyk Girona 17
- Ante Budimir Osasuna 16
- Jude Bellingham Real Madrid 16
- Borja Mayoral Getafe 15
- Alvaro Morata Atletico Madrid 14
- Alexander Sorloth Villarreal 14
- Robert Lewandowski Barcelona 13
- Antoine Griezmann Atletico Madrid 13
- Gorka Guruzeta Athletic Bilbao 12
- Vinicius Junior Real Madrid 12
- Hugo Duro Valencia 12
Wasannin mako na 32 a La Liga ranar Lahadi 21 ga watan Afirilu:

Asalin hoton, Getty Images
- Getafe da Real Sociedad
- Almeria da Villarreal
- Deportivo Alaves da Atletico Madrid
- Real Madrid da Barcelona










