Gwamna Abba Kabir ya kafa hujja 43 a ƙarar zaɓen Kano da ya ɗaukaka

Gov Abba Kabir

Asalin hoton, Abba Kabir/Facebook

Gwamnan Kano, da kotun zaɓen jihar ta soke nasararsa, Abba Kabir Yusuf ya miƙa shari'arsa gaban kotun ɗaukaka ƙara, inda yake ƙalubalantar hukuncin na ranar 20 ga watan Satumba.

Wata takardar kotu mai kwanan watan 2 ga Oktoban 2023, ta nuna, Gwamna Abba Kabir ya zayyana Hukumar zaɓe ta INEC da jam'iyyar APC da kuma jam'iyyarsa ta NNPP, a matsayin waɗanda yake da ƙorafi a kansu.

Mai ƙorafin a cewar takardar, bai gamsu da hukuncin alƙalan kotun ƙararrakin zaɓen gwamnan Kano, ƙarƙashin jagorancin Mai shari'a Oluyemi Akintan-Osadebay ba.

Kotun dai ta soke ƙuri'u sama da 165,000 daga cikin 1,019,602 da aka kaɗa wa Abba Kabir Yusuf a zaɓen 18 ga watan Maris, bisa hujjar cewa ba halattattun ƙuri'u ba ne, saboda ba su da hatimi da sa hannu da kuma kwanan wata.

Don haka, kotun ta ayyana Nasir Yusuf Gawuna a matsayin halastaccen gwamna, ta kuma umarci hukumar zaɓe ta janye shaidar cin zaɓen da ta bai wa Abba Kabir Yusuf tun da farko, sannan ta bai wa Gawuna shaidar nasara.

Sai dai Abba Kabir a yanzu ya ƙalubalanci matakin, inda ya yi iƙirarin cewa hukuncin ƙaramar kotun cike yake da kura-kurai, har ma ya kafa hujjoji guda 43.

Cikin buƙatun da gwamnan na jam'iyyar NNPP ya nema a gaban kotun ɗaukaka ƙara, har da jingine hukuncin kotun sauraron zaɓen gwamnan Kano, sannan ta kori ƙarar da jam'iyyar APC ta shigar tun da farko.

Ɓangaren jam'iyyar APC dai ya faɗa wa BBC tun farko, bayan yanke hukuncin na ranar 20 ga watan Satumba, cewa ba sa fargaba a kan zuwa kotun ɗaukaka ƙara.

Ga wasu cikin hujjojin da Abba Kabir ya gabatar

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Gwamna Abba Kabir Yusuf a cikin takardar shari'ar da ya ɗaukaka, ya yi iƙirarin cewa kotun sauraron ƙarar zaɓen gwamnan Kano ta yi kuskure, bisa shawarar da ta yanke na barin mai ƙorafi ya sake gabatar da shaidu da dama a ranar 22 ga watan Yuli, bayan ya gama gabatar da bahasi a ranar 15 ga watan.

Ya ce a rahotonta na kafin fara shari'a, kotun tun da farko ta bai wa mai ƙara kwana 14 ne ya gabatar da bahasi, abin da ya kammala a ranar 15 ga watan Yuli.

Haka zalika, gwamnan na Kano na jam'iyyar NNPP ya yi iƙirarin cewa kotun ta tauye masa 'yancin samun shari'ar adalci, inda ta yanke hukuncin da ya saɓa wa doka, ta hanyar gaza gabatar da hukunci gaban kowa a kotu, ranar 20 ga watan Satumba.

Sannan ya yi iƙirarin cewa kotun ta yi ba daidai, lokacin da ta yanke karkataccen hukunci, bayan ta cimma matsayar cewa ɗan takarar jam'iyyar APC Nasiru Yusuf Gawuna ya cika duk sharuɗɗan da suka wajaba kamar yadda tsarin mulki da dokar zaɓe suka shimfiɗa.

Abba Kabir ya kuma yi zargin cewa ƙaramar kotu ta yi kuskure, ta hanyar bai wa mai ƙara hukuncin da bai nema ba, bayan ta ɗebe ƙuri'a 282, 496 daga cikin ƙuri'un ɓangare na biyu da aka yi ƙara.

Abba Kabir ya kuma ce kotun ta yi ba daidai ba, da ta yanke hukuncin cewa INEC ta bai wa Nasiru Yusuf Gawuna shaidar cin zaɓe, saboda in ji mai ɗaukaka ƙarar, Gawuna ba ya cikin waɗanda suka yi ƙorafi game da zaɓen.

Ya kuma yi iƙirarin cewa hukuncin kutun zaɓen Kano kuskure ne da ya soke halarcin ƙuri'a 165,616, sannan ya ɗebe su daga cikin ƙuri'un wanda aka yi ƙara.

Takardar kotun ta ce ƙaramar kotu ta yi kuskure da ta yanke hukuncin amincewa da kuma dogara da takardun da wani mai shaida mai lamba PW32 ya gabatar.